ukarofi

12715 Posts
Ɗan Majalisar da ke wakiltar Maradun ya koma APC daga PDP a Zamfara

Ɗan Majalisar da ke wakiltar Maradun ya koma APC daga PDP a Zamfara

Da SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wani ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Maradun a majalisar dokokin Jihar Zamfara, Hon. Maharazu Salisu Faru, ya sauya sheka daga Jam'iyyar sa ta Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC) a Jihar Zamfara. Da yake sanar da shawarar sa a hedikwatar APC da ke Gusau a yau Talata, Hon. Faru ya bayyana cewa rashin gaskiya, adalci, da daidaito a cikin gwamnatin da PDP ke jagoranta a jihar, su ne wasu daga cikin dalilan da suka sa ya fice daga jam'iyyar sa ta PDP. Ya yi zargin cewa gwamnatin da PDP ke jagoranta…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya rantsar da sabbin alƙalai uku na babbar kotun Katsina

Gwamna Raɗɗa ya rantsar da sabbin alƙalai uku na babbar kotun Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sabbin alƙalai da aka rantsar su ne Abubakar Mohammed Dikko da Maryam Umar Abdullahi ɗaya ga tsohon babban alƙalin kotun ɗaukaka ƙara na ƙasa mai shari'a Umar Abdullahi,sai shamsuddeen Abdulrahaman Yanmama. A jawabinsa ga sabbin alƙalai, Gwamna Raɗɗa ya jaddada girman amanar da aka ɗora a wuyansu, yana mai nanata muhimmancin kiyaye manyan ƙa’idodin shari’a na gaskiya, adalci, da amana a aikinsu ga jama’ar Jihar Katsina. Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafa wa bangaren shari’a tare da kare cikakken ‘yancin sa. Ya bayyana cewa, zaɓin sabbin alƙalai…
Read More
Mace mai ilimi tana jagorantar al’umma da nutsuwa – Nana Asma’u Bintu Danfodiyo

Mace mai ilimi tana jagorantar al’umma da nutsuwa – Nana Asma’u Bintu Danfodiyo

"Addinin Musulunci ya ɗaukaka mace, jahilci ne yake taƙaita ta" Daga AISHA ASAS Shafin Gimbiya bai tsaya a iya fira da mata kan sana'oinsu ba, ko samun bayanai kan ƙalubalen rayuwa ko nasarorin da suke samu ba, haka ma bai tsaya a iya darrusan wayar da kai ba, maimakon haka, ya yi nutso har zuwa ga tarihi, inda zai dinga kawo wa masu karatu labaran matan da suka kafa tarihi, ba don nishaɗi ko sani ba, sai don ya zama izna, ya koyar, sannan ya samarwa mata hanyar kamawa, wadda za ta zama makaranta a lokacin da suke fuskantar rayuwarsu.…
Read More
Jerin wuraren shaƙatawa 20 mafi tsada a Legas

Jerin wuraren shaƙatawa 20 mafi tsada a Legas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da ƙarshen shekara ke gabatowa, rahotanni sun nuna cewa, yawancin manyan wuraren shaƙatawa da wuraren taro na alfarma a birnin Legas sun fara cika tun kafin lokacin hutun na Disamba, wanda ake yi wa laƙabi da ‘Detty December 2025’, ya iso. Wannan na zuwa ne bayan Detty December 2024 ta kafa sabon tarihin shaƙatawa da nishaɗi a Nijeriya, inda ta zama ginshiƙi ga harkokin yawon buɗe ido da tattalin arzikin nishaɗi. Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewa Nijeriya ta samu kusan kashi 4% na tattalin arzikin GDP ɗinta daga ayyukan Detty…
Read More
Gwamnatin Katsina tare da UNDP sun shirya taron ƙarawa juna sani kan tsaro

Gwamnatin Katsina tare da UNDP sun shirya taron ƙarawa juna sani kan tsaro

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar Ɗinkin duniya (UNDP) tare da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina sun shirya taron bita da ƙarawa juna sani a kan dabarun samun zaman lafiya mai ɗorewa a cikin al'umma. Taron bitar ya ƙunshi masu ruwa da tsaki a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a ƙananan hukomomi dake fama da matsalar tsaro a jihar Katsina. Su dai waɗannan al'ummomi sun fito ne daga ƙananan hukomomin Faskari, Jibia, Batsari, Safana, Ɗanmusa, Ƙanƙara, Matazu da kuma Kurfi. Yayin taron wanda ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta ɗauki nauyi, an gabatar da ƙasidu masu nuna muhimmancin…
Read More
Ta samu tagwagen bazata bayan ta shafe shekaru 10 babu haihuwa

Ta samu tagwagen bazata bayan ta shafe shekaru 10 babu haihuwa

Wani labari mai taɓa zuciya ya karaɗe kafafen sada zumunta bayan wata mata ta ruwaito yadda ta samu ’yan tagwaye bayan shekaru kimanin 10 tana fama da rashin haihuwa. Matar, wadda ta kasance cikin auren farko na tsawon shekaru goma ba tare da ta samu haihuwa ba, ta sha gwaje-gwaje da jinyoyi ciki har da zagaye biyar na IɓF da duk suka gaza. A ƙarshe, ta yanke shawarar daina gwaje-gwajen, ta kuma mayar da hankali kan rayuwarta ba tare da matsin lambar neman ciki ba. Sai dai yayin da ta ke ci gaba da gwagwarmaya, auren nata ya mutu ta…
Read More
Magidanci ya ɓarke da kuka bayan matarsa ta haifi ’yan shida

Magidanci ya ɓarke da kuka bayan matarsa ta haifi ’yan shida

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wani mutum yana kuka sosai a asibiti bayan matarsa ta haifi ‘ya’ya shida lokaci guda. Rahotanni sun ce matar ta haifi jarirai shida a lokaci ɗaya, abin da mijin bai taɓa zato ba. A maimakon farin ciki da yawanci ake yi a irin wannan lokaci, mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya fashe da kuka a gefen jariran, yana bayyana damuwarsa kan yadda za su kula da su a irin wannan mawuyacin halin tattalin arziki. A cikin bidiyon, an jiyo shi yana faɗa wa matarsa da mamaki,…
Read More
Zuwa ga iyaye: Ku kula da ’ya’yanku domin sakaci na janyo hauhawar satar yara

Zuwa ga iyaye: Ku kula da ’ya’yanku domin sakaci na janyo hauhawar satar yara

Assalamu alaikum iyaye. Wannan wasiƙa ce ta faɗakarwa, da niyyar tunatarwa cikin kulawa da aauna. Ba da laifi ko zargi nake ba, amma da zuciyar tausayi da damuwa kan abin da ke ta faruwa a tsakanin al’umma — matsalar satar yara wadda ke ƙaruwa a sannu a hankali saboda sakaci, rashin tsaro, da kuma sakarwa wajen kula da yara. A cikin ‘yan shekarun nan, an samu ƙaruwar rahotanni daga sassa daban-daban na ƙasar nan game da yadda ake sace yara a hanya, a makaranta, a kasuwa, ko ma a gida. Wasu yara kan ɓace cikin yanayi mai ban mamaki, yayin…
Read More
2027: Tsarin karɓa-karɓar mulki alama ce ta raunin APC a Zamfara – Hon. Jaji

2027: Tsarin karɓa-karɓar mulki alama ce ta raunin APC a Zamfara – Hon. Jaji

Na SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Ƙaura Namoda da Birnin Magaji a Jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji ya yi Allah wadai da yunƙurin kace nace da wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar ke yi na ayi tsarin karɓa karɓar mulki kan wanda zai zama ɗan takarar gwamna a 2027 a ƙarƙashin jam'iyyar ta APC a jihar. Hon. Jaji ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a gidansa da ke Gusau yau Lahadi. A cewarsa, batun tsarin karɓa karɓar mulki alama ce ta rauni a jam'iyyar ta APC a…
Read More
Kwamandan NSCDC ya miƙa ta’aziyya kan rasuwar kwamishinan tsaron cikin gida na Gombe

Kwamandan NSCDC ya miƙa ta’aziyya kan rasuwar kwamishinan tsaron cikin gida na Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen Jihar Gombe, Kwamanda Jibrin Idris, ya bayyana babban jimami bisa rasuwar kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar Gombe, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (Mai Ritaya), tare da ɗan sandan da ke tsaron sa, Sajan Adamu Husaini, da direbansu, waɗanda suka rasu sakamakon mummunan hadarin mota da ya rutsa da su a ranar Juma’a. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar, Kwamanda Idris ya bayyana cewa wannan lamari babban rashi ne ba kawai ga iyalan mamatan ba, har ma…
Read More