26
Oct
Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya karɓi sabon Kwamandan hukumar tsaro ta Civil Defence (NSCDC) da aka tura domin jagorantar rundunar a Jihar Kano. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi. Yayin ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan a fadar gwamnatin Kano, sabon kwamandan, Bala Bawa Bodinga, ya yi alƙawarin yin aiki tare da gwamnatin Kano domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar. Kwamanda Bodinga ya tabbatar da biyayyarsa da cikakken goyon…
