ukarofi

12715 Posts
ADC ta dakatar da mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa

ADC ta dakatar da mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta dakatar da mataimakin shugabanta na ƙasa (Kudu maso Kudu), Dr. Usani Usani, bisa zarginsa da aikata laifukan cin amanar jam’iyya da kuma rashin biyayya ga wasu hukumomi a jam’iyyar. Dakatarwar da ta fara aiki nan take, ya biyo bayan shawarwarin da Kwamitin Ayyuka na Jiha (SWC) na jam’iyyar ADC a Jihar Kuros Riba ya yi a taron da ta gudanar a ranar Laraba, 15 ga Oktoba, 2025. A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, Sakataren Yaɗa Labarai na Jihar, James Otudor, ya ce kwamitin…
Read More
Hattara da sojojin waya, masu fushi da fushin wani

Hattara da sojojin waya, masu fushi da fushin wani

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Na san mai yiwuwa taken rubutun nan zai bai wa wani dariya. ƙila ma wani ya tambayi ko su waye kuma sojojin waya? To, in dai ka san su waye ake nufi da Sojojin Baka, ba za ka kasa gane Sojojin Waya ba. Kamar yadda aka san Sojojin Baka da shiga tashoshin rediyo suna sayen fili don kare muradun wasu ko cin mutuncin wasu abokan hamayyar ubangidansu na siyasa, don ƙara angiza wutar adawa ko son a sani. Haka su ma sojojin waya suke yin nasu yaƙin ta zaurukan sada zumunta, suna rubuce-rubuce na ɓatanci ko…
Read More
SWIT ta tattauna da masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen haraji, lafiya da daidaiton Jinsi a Kano

SWIT ta tattauna da masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen haraji, lafiya da daidaiton Jinsi a Kano

Daga RABIU SANUSI Kungiyar mata ta 'Society of Women in Taxation' (SWIT), wacce ke ƙarƙashin Chartered Institute of Taɗation of Nigeria (CITN), ta shirya taron kwana ɗaya a Kano domin tattauna batutuwan sauye-sauyen haraji, daidaiton jinsi, da kuma wayar da kan jama’a kan lafiyar kwakwalwa. Taron wanda aka gudanar a dakin taro na Grand Central Hotel dake Kano ya haɗa masana, klƙwararru da membobin fannin haraji don tattauna tasirin sauye-sauyen haraji na kasa da yadda suke shafar daidaiton jinsi da ci gaban ƙasa gaba ɗaya. A jawabin maraba da ta gabatar, Shugabar ta SWIT ta making Kasa Dr. Caroline Ndubuisi…
Read More
A shirye nake na sake haɗe kan ‘yan ƙungiyar Zabi Sonka ta ƙasa – Garba Ubale

A shirye nake na sake haɗe kan ‘yan ƙungiyar Zabi Sonka ta ƙasa – Garba Ubale

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Tsohon Shugaban ƙungiyar Matasa ta ƙasa reshen jihar Gombe kuma tsohon shugaban ƙungiyar Zabi Sonka da taimakon juna a jihar Gombe, Kwamared Garba Ubale, ya sha alwashin haɗe kan 'ya'yan ƙungiyar idan aka zaɓe shi. 'Ya'yan ƙungiyar daga yankin Arewa maso Gabas ne suka bayyana hakan a lokacin da suke zantawa da wakilinmu a shirye-shiryen ƙungiyar na zaɓenta na ƙasa. Mambobinta ƙungiyar daga sassa daban-daban na ƙasar suka nuna cikakken goyon baya ga Kwamared Garba Muhammad Ubale domin ya jagoranci ƙungiyar a matakin ƙasa. Kwamared Garba, wanda ya shahara wajen shiryar da matasa da…
Read More
‘Yan Nijeriya fiye da miliyan takwas ne suka yi rajistar zaɓe ta Intanet zuwa yanzu – INEC

‘Yan Nijeriya fiye da miliyan takwas ne suka yi rajistar zaɓe ta Intanet zuwa yanzu – INEC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta ce ‘yan Nijeriya fiye da miliyan takwas ne suka kammala rajistar zaɓe matakin farko a intanet yayin rajistar masu kaɗa ƙuri’a da ake gudanarwa a faɗin ƙasar. Cikin rahoton da hukumar ta fitar a Abuja, Inec ta ce baya ga mutum miliyan 8,003,196 da suka yi rajistar a matakin farko, miliyan 1,700,000i ne suka kammala cikakkiyar rajistarsu. Bisa ga ƙididdigar mako na tara, Jihar Imo ce ta fi kowa yawan masu rajista da 826,850, wanda ya yi daidai da kashi 10.32 cikin 100. Sai Legas da 604,619…
Read More
WHO za ta yi wa yara miliyan 1.8 allurar rigakafin Polio a Zamfara

WHO za ta yi wa yara miliyan 1.8 allurar rigakafin Polio a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tare da haɗin gwiwa da UNICEF, Solina, gidauniyar chigari da gidauniyar Sultan da kuma hukumar bayar da lafiya matakin farko za su yi wa yara sama da miliyan 1.8, allurar rigakafin Shan Inna, Polio a faɗin Jihar Zamfara. Dr. Murtala Ibrahim Salahuddeen, manajan lamarin, cibiyar gaggawa ta ayyukan Polio, a jihar Zamfara, ya bayyana haka a wani taron manema labarai don bikin tunawa da ranar Polio ta duniya a jihar a yau Asabar. A cewarsa, taken ranar Polio ta duniya ta wannan shekarar shine, kawo ƙarshen Polio yanzu, kowane yaro…
Read More
Ƙungiyar Wamban Shinkafi ta yi kira ga Tinubu ya hana Matawalle amfani da ofishinsa don siyasa

Ƙungiyar Wamban Shinkafi ta yi kira ga Tinubu ya hana Matawalle amfani da ofishinsa don siyasa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar All Progressive Congress APC, ɓangaren ƙungiyar Wamban Shinkafi Democratic Front a jihar Zamfara, ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugabannin jam'iyyar APC na ƙasa da su hana ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle amfani da ofishin sa wajen gudanar taron siyasa. Yushau Abdullahi MadaShugaban ƙungiyar Democratic Front Wamban Shinkafi ya yi wannan kira a Gusau yau ranar Asabar. A cewarsa, kiran ya zama dole idan aka yi la'akari da cewa, ofishin Ministan ba don siyasa aka kafashi ba, sai don kare ƙasa daga dukkanin ƙalubalen rashin tsaro a faɗin Nijeriya. Yushau ya…
Read More
Shinkafi ya ci amanar APC a Zamfara – Yusuf Idris

Shinkafi ya ci amanar APC a Zamfara – Yusuf Idris

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar All Progressive Congress APC, reshen jihar Zamfara, ta bayyana Dr. Sani Abdullahi Shinkafi a matsayin mutumi da ke cin amanar jam'iyyar a siyasance a Jihar Zamfara. Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar, Yusuf Idris ya yi wannan furuci a cikin wata sanarwa yayin da yake mayar da martani ga kalaman da Shinkafi ya yi wa shugabannin jam'iyyar kwanan nan. Jam'iyyar ta bayyana kalaman da Shinkafi ya yi wa shugabannin jam'iyyar kwanan nan, musamman ƙaramin ministan tsaro, Bello Muhammad Matawalle da Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin yunƙurin ɓata sunan su. Jam'iyyar ta koka da yadda Shinkafi…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya naɗa sabbin shugabannin hukumomin gwamnati a jihar

Gwamna Raɗɗa ya naɗa sabbin shugabannin hukumomin gwamnati a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sun haɗa da Shugabannin a KASROMA, KASEDA, Hukumar kula da ma’aikata da hukumar fansho. Sanarwar ɗauke da sa hannun babban jami'in hulɗa da jama'a na gwamnan Muhammad kaula,Gwamnan ya umurce su da su tabbatar da aiwatar da ajandar wannan gwamnati na“Gina Makomar Ku” Gwamnan ya amince da naɗin Injiniya Abba Junaidu MNSE a matsayin Shugaban hukumar gyaran hanyoyi ta Jihar Katsina (KASROMA). Injiniya Junaidu yana da digiri na biyu (Master’s) a fannin gudanar da muhalli, da kuma digiri na farko (B.Eng) a Injiniyan gini. Ya yi aiki na dogon lokaci a matsayin Chief Building Officer…
Read More
Farfesa Muhammad Khalid Othman ya zama shugaban jami’ar FUDMA

Farfesa Muhammad Khalid Othman ya zama shugaban jami’ar FUDMA

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar gudanarwar na jami'ar Gwamnatin tarayya da ke Dutsinma ta amince ta daɗin Farfesa Muhammad Khalid Othman a matsayin shugaban jami'ar. Shugaban hukumar gudanarwar na jami'ar HE.Ali Abubakar Jatau ya sanar da haka jim kaɗan da kammala taron hukumar gudanarwa na jami'ar karo na 36 da ya gudana a garin Dutse,a jihar Jigawa. A wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na jami'ar malam Nasiru Abdul ya fitar naɗin ya biyo bayan gabatar da rahoton haɗin gwiwa na zaben shugaban jami'ar. Jatau ya ce fitowar Farfesa Othman matsayin shugaban jami'ar sai da…
Read More