25
Oct
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wani masanin manufofin gwamnati kuma mai fafutukar ingantaccen shugabanci, Tijjani Sarki, ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya naɗa Farfesa Abdallah Uba Adamu a matsayin Shugaban Jami’ar Northwest, Kano na dindindin. Ta cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa a aka rubuta ranar 25 ga Oktoba, 2025, Sarki ya bayyana Farfesa Adamu a matsayin “mabuɗi, haziƙin malami, shugaba mai hangen nesa wanda ya tabbatar da bajintarsa a harkar ilimi a Najeriya.” Ya bayyana cewa Farfesa Adamu, ɗan asalin Kano da aka haifa a shekarar 1956, ya samu digirinsa daga Jami’ar Ahmadu Bello,…
