ukarofi

12715 Posts
Shugaban matasa ya canja sheƙa daga APC zuwa ADC a Kebbi 

Shugaban matasa ya canja sheƙa daga APC zuwa ADC a Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Wani ɗan kasuwa mazaunin birnin Legas kuma shugaban matasa a mazaɓar Sauwa/Kaurar Sani a ƙaramar hukumar Argungu Alhaji Zaki Dalatu ya canja sheƙa daga Jam'iyyar APC zuwa ADC. Da ya ke zantawa da manema labarai a garin Argungu yayin wata ziyara da tawagar sa ta kai wa Honarabul Sani Yakubu (Yar Giwa) Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Argungu da Augie. Alhaji Zaki ya bayyana cewa ya baro kasuwancinsa da ya ke yi a Legas saboda kawai ya jaddada barin Jam'iyyar APC mai mulki zuwa Jam'iyyar ADC ta adawa tare da dukkan magoya bayansa.…
Read More
Kananan hukumomin Rano da Kumbotso sun taya Kwankwaso murnar cika shekara 69

Kananan hukumomin Rano da Kumbotso sun taya Kwankwaso murnar cika shekara 69

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Shugaban ƙaramar Hukumar Rano, Hon. Muhammad Wada, ya shiga sahun sauran shugabanni wajen miƙa saƙon taya murna ga tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Jagoran jam’iyyar NNPP, Injiniya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, bisa cikar sa shekaru 69 da haihuwa. Hon. Wada ya bayyana cewa wannan rana ta zagayowar haihuwar Jagoran nasu ta yi kama da ranar babbar sallah, saboda farin cikin da al’umma ke ciki da kuma irin gudunmawar da Kwankwaso ya bayar ga ci gaban Jihar Kano da Nijeriya bakiɗaya. Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wurin taron…
Read More
Aiki tuƙuru ne sirrin dukkan nasara – Ronaldo ga matasa bayan ya zama ɗan wasa na farko da ya mallaki Dala biliyan

Aiki tuƙuru ne sirrin dukkan nasara – Ronaldo ga matasa bayan ya zama ɗan wasa na farko da ya mallaki Dala biliyan

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo, ya aika da sako mai cike da ƙarfafa gwiwa ga matasa a faɗin duniya, kwanaki kaɗan bayan da ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa na farko da ya kai matsayin mallakar dala biliyan. ɗan wasan mai shekaru 40, wanda ke bugawa ƙungiyar Al Nassr FC ta Saudiyya da kuma ƙasarsa Portugal, yanzu yana da dukiya da aka kiyasta ta kai dala biliyan 1.4. Wannan na zuwa ne bayan ya zura wata ƙwallo mai nisa a nasarar da ƙungiyarsa ta samu kan Al Fateh SC da ci 5–1 a gasar Saudi Pro…
Read More
Hakimi da Salah na kan gaba a ’yan takarar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2025

Hakimi da Salah na kan gaba a ’yan takarar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na 2025

Achraf Hakimi da Mohamed Salah suna kan gaba a jerin ’yan takara 10 dake fatan lashe ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afirka na 2025. Hakimi mai tsaron bayan tawagar Morocco ya bayar da gudunmuwar da Paris St Germain ta lashe kofi uku a Faransa da Champions League a kakar da ta wuce, shi kuwa Salah ya ɗauki Premier League tare da Liverpool. ɗan wasan da ke taka leda a Everton, Iliman Ndiaye da na Tottenham, Pape Matar Sarr, waɗanda suka taka rawar da ƙasashensu suka samu damar samun tikitin shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026, suna…
Read More
Kano Pillars ta dakatar da mai horar da ’yan wasanta

Kano Pillars ta dakatar da mai horar da ’yan wasanta

Hukumar gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da masu horas da ƙungiyar bisa jagorancin Ogenyi Evans da mataimakinsa Ahmed Yaro Yaro. Hakan na zuwa ne bayan ƙungiyar ta sha kashi a hannun Barau FC a karawar da suka yi ranar Lahadi a gasar Premier ta Nijeriya. Sanarwar da hukumar gudanarwar ƙungiyar ta fitar ta ce an dakatar da kocin da mataimakinsa ne "sanadiyyar rashin ƙowari a gasar Premier ta Nijeriya ta 20025/26 da ke gudana." Ya zuwa yanzu Pillars ta yi nasara a wasanni biyu ne kacal cikin wasa takwas da ta buga a wannan…
Read More
An buƙaci Beckham ya goyi bayan sayar da Man United

An buƙaci Beckham ya goyi bayan sayar da Man United

Rahotanni sun bayyana cewa an tuntuɓi David Beckham, domin ya goyi bayan sayar da Manchester United. A raɗe-raɗin da ake yi wasu attajirai masu zuba hannun jari daga Haɗaɗɗiyar Daulal Larabawa ne ke shirye-shiryen sayen hannun jarin da iyalan Glazer suka mallaka. Kamar yadda Star da Mirror ta wallafa, attajiran na son Beckham ya zama jakada a lokacin da za a yi cinikin. Tsohon ɗan wasan United, wanda yake da hannun jari Inter Miami da Salford, zai iya samun damar mallakar hannun jari a ƙungiyar Old Trafford. Beckham wanda ya daɗe yana caccakar iyalan Glazer kan yadda suke gunadar da…
Read More
Ana samun sabbin hare-hare bayan sulhu da ’yan bindiga Arewa maso Yamma

Ana samun sabbin hare-hare bayan sulhu da ’yan bindiga Arewa maso Yamma

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD A yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, an samu sauyin lamura na tsaro yayin da shugabannin ‘yan bindiga suka saki mutane sama da 120 da suka daɗe a hannunsu a jihohin Zamfara da Katsina — duk da cewa an sake kai sabuwar harin garkuwa da mutane a Zamfara. Rahotanni daga PRNigeria sun nuna cewa sanannen shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, ya saki fiye da mutum 100 a Zamfara, yayin da wani shugaban ‘yan bindiga da ba a bayyana sunansa ba ya saki mutum 20 a Katsina. Wannan matakin ya biyo bayan ci gaba da tattaunawa da gina…
Read More
SERAP ta buƙaci Akpabio da Abbas su bayyana yadda aka yi da biliyan N18.6 na majalisa

SERAP ta buƙaci Akpabio da Abbas su bayyana yadda aka yi da biliyan N18.6 na majalisa

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Kungiyar Kare Haƙƙin Jama’a da Gaskiya ta SERAP ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, su bayyana yadda aka kashe Naira Biliyan 18.6 da aka ware domin gina ofishin Rukunun Ofisoshin Majalisar Aasa, kamar yadda rahoton mai binciken asusun gwamnati na 2022 ya nuna. SERAP ta nemi shugabannin majalisun su bayyana sunan kamfanin da ya karɓi kuɗin, tare da bayyana cikakken bayani kan masu hannun jari, shugabanni da adireshinsa. Kungiyar ta kuma buƙaci a yi bayani kan yadda aka karya dokar saye da kaya ta gwamnati (Procurement Act), saboda babu…
Read More
Barayi suka yi awon gaba da kayan sarautar Faransa mafi tsada daga gidan tarihi

Barayi suka yi awon gaba da kayan sarautar Faransa mafi tsada daga gidan tarihi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu ɓarayi sun kai mummunan farmaki a gidan tarihin Louvre da ke birnin Paris, wanda shi ne mafi girma a duniya, inda suka sace kayan adon da ba a auna su da kuɗi, a cewar gwamnatin Faransa. Rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin sun yi amfani da motar crane wajen kakkarya tagar benen, suka shiga sashen da ke ajiye da kayan sarautar Faransa, sannan suka tsere a kan babura. Ma’aikatar cikin gida ta ce, satar ta faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe a ranar Lahadi, daidai lokacin da gidan tarihin ya fara karɓar baƙi. Ministar…
Read More
An ƙaddamar da sabon tsarin lasisin tuƙi na zamani a Nijeriya

An ƙaddamar da sabon tsarin lasisin tuƙi na zamani a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta sanar da sabon tsarin lasisin tuƙi wanda ba zai an taɓa na'ura ba (contactless biometric system), wanda za a fara amfani da shi a faɗin ƙasar domin tabbatar da samun lasisi cikin sauri ba tare da jinkiri ko amfani da lasisin wucin-gadi ba. Kwamandan hukumar, Shehu Mohammed, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin yayin ƙaddamar da yaƙin wayar da kai na “Ember Months 2025”, inda ya ce wannan tsarin sabon salo ne na sauya fasalin ayyukan FRSC gaba ɗaya zuwa tsarin fasahar zamani. Ya bayyana cewa an…
Read More