25
Oct
Daga MAHDI MUSA MUHAMMMAD Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su fi mayar da hankali wajen amfani da kayayyakin da ake samarwa a cikin ƙasa, a matsayin wata hanya ta ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasa da gina dogaro da kai. Dangote ya bayyana haka ne yayin wata ziyara ga ‘yan jarida a matatar mai ta Dangote da ke yankin Lekki Free Trade Zone a Legas, ƙarƙashin jagorancin tsohon mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Reno Omokri, wanda kuma yake jagorantar ƙungiyar #GrowNairaBuyNaija — wacce ke yaƙi don bunƙasa sayen kayayyakin cikin gida. Dangote…
