ukarofi

12715 Posts
Sojojin Nijeriya sun mutu wajen ƙoƙarin daƙile harin Boko Haram a Borno

Sojojin Nijeriya sun mutu wajen ƙoƙarin daƙile harin Boko Haram a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce wasu dakarunta sun rasa rayukansu wajen ƙoƙarin daƙile wani mummunan harin da mayaƙan Boko Haram suka shirya kai wa a yankin Kashimri, cikin ƙaramar hukumar Bama, jihar Borno. Harin, wanda aka yi ƙoƙarin kai wa a ranar 17 ga Oktoba 2025, rundunar ta ce sojojinta ƙarƙashin Operation Haɗin Kai su samu nasarar daƙile shi bayan da suka gano kuma suka lalata sansanonin ’yan bindigan da ke yankin. A cikin sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na ɗ, kakakin rundunar, Laftanar Kanal Appolonia Anele, ta bayyana cewa sojojin sun…
Read More
Zubar da ciki: An sake yamutsa hazo tsakanin Akpabio da Natasha a zaman Majalisar Dattawa

Zubar da ciki: An sake yamutsa hazo tsakanin Akpabio da Natasha a zaman Majalisar Dattawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Talatar da ta gabata ne aka samu rashin jituwa a Majalisar Dattawa yayin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, da Sanata Adams Oshiomhole suka fafata tare da taƙaddama akan ƙudirin gyaran dokar aikata laifuka da ke neman tsananta hukunci ga masu taimakawa wajen zubar da ciki a cikin Kundin Dokar Laifuka (gyara) 2025. Tun da farko a zaman majalisar dattijai bakiɗaya, ta zartar da wani muhimmin ƙudiri na doka ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata da ƙaramar yarinya, ba tare da zaɓin tara…
Read More
Dan uwa ya cire wa ƙanwarsa idanu don neman kuɗi a Bauchi

Dan uwa ya cire wa ƙanwarsa idanu don neman kuɗi a Bauchi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Bauchi ta kama mutum shida da ake zargi da hannu cikin mummunan laifin cire wa wata yarinya mai shekaru bakwai idanu don yin asiri da nufin neman kuɗi. ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Auwalu Muhammad, shi ne aka bayyana cewa ya kai ƙanwarsa, Rukayya Muhammad, cikin daji da ke Bayan Dutse a yankin Wailo, ƙaramar hukumar Ganjuwa, inda ya kai mata hari ya cire mata idanu biyu. Rahoton rundunar ya ce, an ceto yarinyar, aka garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi,…
Read More
Na haifi ɗana na farko Ina da shekara 14 – Shina Peters

Na haifi ɗana na farko Ina da shekara 14 – Shina Peters

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fitaccen mawaƙin Juju na Najeriya, Oluwashina Akanbi Peters, wanda aka fi sani da Sir Shina Peters, ya bayyana yadda rayuwarsa ta fara da wuri sosai, inda ya ce ya zama uba tun yana da shekara 14 kacal. A wata hirar sa da aka yi da shi a shirin The Honest Bunch Podcast, Shina Peters ya ce ya fara harkar waƙa tun yana da shekara 10, kuma ya cimma manyan nasarori kafin ya kai balaga sosai. “Na fara sana’ar waƙa ina da shekara 10. Na haifi ɗa na farko ina da 14. Na sayi motata ta farko…
Read More
Harajin VAT: Gwamnatocin Nijeriya sun raba tiriliyan N2 a Satumba

Harajin VAT: Gwamnatocin Nijeriya sun raba tiriliyan N2 a Satumba

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Tarayya (FAAC) ya bayyana cewa, an raba jimillar kuɗin da ya kai Naira Tiriliyan 2.103 ga matakai uku na gwamnati – Tarayya, Jihohi, da ƙananan Hukumomi — a matsayin rabon kuɗin watan Satumba 2025. Taron raba kuɗin na FAAC ya gudana ne a Abuja a watan Oktoba, inda aka tabbatar da rabon da aka samo daga manyan hanyoyin samun kuɗin shiga — tiriliyan N1.239 daga kuɗin da aka tara ta hanyoyin doka, biliyan N812.593 daga harajin ɓAT, da biliyan N51.684 daga harajin EMTL. A cewar sanarwar da aka fitar bayan taron, an samu…
Read More
Diyata ba za ta tsirgo da kanta daga bene ba, inji mahaifin ‘yar jaridar Arise TV

Diyata ba za ta tsirgo da kanta daga bene ba, inji mahaifin ‘yar jaridar Arise TV

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mahaifin Marigayi 'yar jarida Somtochukwu Maduagwu ya ƙi amincewa a hukumance akan mutuwarta, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike. Injiniya Ifeanyi Maduagwu, mahaifin marigayi Somtochukwu Maduagwu, ya yi kira ga jami’an tsaro da su yi bincike sosai kan lamarin mutuwar ‘yarsa, yana mai dagewa cewa zarge-zargen da ake yi ba za su lissafu ba. Wata ‘yar jarida mai suna Somtochukwu ta rasu ne a daren ranar 29 ga watan Satumba bayan da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai hari gidanta da ke Katampe a Abuja. Tun farko dai…
Read More
Gwamnatin Kano ta ɗage aikin tsaftar muhallin ƙarshen wata

Gwamnatin Kano ta ɗage aikin tsaftar muhallin ƙarshen wata

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ɗage aikin tsaftar muhalli na ƙarshen watan Oktoba 2025 da aka tsara gudanarwa a gobe Asabar. Wannan mataki ya biyo bayan shirye-shiryen babban bikin baje kolin gargajiya da gwamnatin jihar ta shirya, wanda ya zo daidai da ranar da ake gudanar da tsaftar muhalli. A cewar sanarwar da sashen wayar da kai na ma’aikatar muhalli ta jihar ya fitar a ranar Juma’a, 25 ga Oktoba 2025, ta ce an ɗage aikin ne domin bai wa jama’a damar halartar taron baje kolin cikin natsuwa da tsari. Sai dai ma’aikatar ta…
Read More
Rigakafin shan Inna ba ta da illa — Jatau Ga Iyaye

Rigakafin shan Inna ba ta da illa — Jatau Ga Iyaye

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Shugaban ƙaramar hukumar Balanga a Jihar Gombe, Ibrahim Salisu Jatau ya buƙaci iyaye da masu kula da yara da su fito da ’ya’yansu domin yin rigakafin cutar shan inna, yana mai tabbatar da cewa rigakafin ba ta da wata illa ga lafiyar yara. Jatau ya yi wannan kira ne yayin ƙaddamar da bikin ranar yaƙi da cutar shan inna ta duniya ta shekarar 2025, wanda ƙungiyar Rotary ta shirya domin inganta lafiyar yara a faɗin Jihar Gombe. A cewarsa, “Allurar rigakafin shan inna tana da matuƙar muhimmanci, kuma babu wata illa a cikinta. Abin…
Read More
An yi kira ga matan shugabannin ƙananan hukumomi su tashi tsaye wajan yaƙi da cutar polio a Katsina

An yi kira ga matan shugabannin ƙananan hukumomi su tashi tsaye wajan yaƙi da cutar polio a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Uwargidan Gwamnan Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Raɗɗa ta yi kiran a wajan taron ranar Cutar polio a Katsina. Taron wanda ya gudana a ɗakin taro na fadar gwamnatin jihar Katsina ya sami halartar ƙungiyoyi da dama da suka haɗa da ƙungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO da ƙungiya da ke kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF da wasu ƙungiyoyi na ƙasa masu zaman kansu. Akwai wakilan malaman addini da na sarakunan gargajiya da matan shugabannin ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin jihar. Uwargidan Gwamnan ta ce babu shakka akwai rawar…
Read More
Mai wushirya ya fasa auren ‘Yarguda

Mai wushirya ya fasa auren ‘Yarguda

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Fitaccen ɗan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya, yabayyana cewa ba zai auri Basira ’Yar Guda da kotu ta umarce shi bayan tuhumarsa da wasu laifukan watsa baɗala a kafafen sada zumunta. Cikin wani sabon bidiyo da Mai Wushirya ya fitar, a yau ranar Alhamis ya bayyana cewa duba da ƙorafe-ƙorafen da iyayensa suka yi da sauran abokansa, yana shaida wa mutane cewa idan ya tashi aure zai sanar da su. Ya ƙara da cewa da ma ba a son ransa ya amsa cewa zai auri ƴar Guda ba, tsoro ne…
Read More