24
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da karatu na biyu na ƙudirin da ke neman soke Dokar Zaɓe ta 2022 domin samar da sabuwar Dokar Zaɓe ta 2025. Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da amincewar yayin zaman majalisa a ranar Laraba bayan mafi yawan 'yan majalisa sun goyi bayan ƙudirin ta hanyar ƙuri’ar murya. Bayan haka, an miƙa ƙudirin zuwa Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Zaɓe domin ƙarin nazari da shirya sauraron jama’a. An umurci kwamitin da ya dawo da rahoto cikin makonni biyu. ƙudirin, wanda Shugaban Kwamitin Zaɓe na Majalisar…
