ukarofi

12715 Posts
Yadda tsadar gas ta tursasa talakan Nijeriya koma wa amfani da gawayi

Yadda tsadar gas ta tursasa talakan Nijeriya koma wa amfani da gawayi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsadar gas ta kai ƙololuwa a Nijeriya, inda farashin kilogiram ɗaya ya kai N1,600, lamarin da ya tilasta yawancin iyalai komawa amfani da gawayi, garin katako da itace domin dafa abinci. Rahotanni daga Blueprint sun nuna cewa yajin aikin da ƙungiyar Ma’aikatan Mai da Gas (PENGASSAN) ta shiga ya haifar da cikas ga harkar rabon iskar gas, wanda ya haddasa ƙarancin kayayyaki da tashin farashi a sassan ƙasar. Yajin aikin na tsawon kwanaki uku ya katse rabon kayayyaki daga manyan kamfanoni kamar matatar Dangote, da kuma gyare-gyare a Nigeria LNG Train 4. Sai dai masana tattalin…
Read More
Ku kare kanku, ba za mu biya fansa ga ’yan bindiga ba – Gwamna Bago

Ku kare kanku, ba za mu biya fansa ga ’yan bindiga ba – Gwamna Bago

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa shiga tattaunawa ta sulhu da ’yan bindiga ba, kuma ba za ta biya kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane ba — yana mai kira ga al’ummar jihar da su ɗauki mataki na kare kansu daga hare-haren da ke ƙaruwa a faɗin jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ziyarar jaje da ya kai garuruwan Rijau da Magama a yankin Kontagora, inda ’yan bindiga suka yi mummunan ta’adi a kwanakin baya. Da yake magana cikin fushi da takaici, Gwamna Bago ya ce…
Read More
Majalisar Wakilai ta umarci a gyara hanyar Bida–Agaie bayan gobarar tanka ta kashe mutum 30

Majalisar Wakilai ta umarci a gyara hanyar Bida–Agaie bayan gobarar tanka ta kashe mutum 30

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta umarci Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya tare da Hukumar Kula da Hanyoyi (FERMA) da su hanzarta gyara da faɗaɗa hanyar Bida–Agaie–Lapai–Lambata–Diko, bayan yawaitar gobarar tankokin mai da ke faruwa a yankin. Wannan mataki na Majalisar ya biyo bayan gobarar tankar mai da ta afku a yankin Essa, inda rahotanni suka ce sama da mutum 30 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 40 suka ji mummunar rauni. Majalisar ta kuma umarci Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) da sauran hukumomin da abin ya shafa da su ƙarfafa matakan tsaro da binciken…
Read More
Sojoji sun kashe manyan kwamandojin ISWAP biyar a Borno da Yobe

Sojoji sun kashe manyan kwamandojin ISWAP biyar a Borno da Yobe

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Dakarun Operation Haɗin Kai (OPHK) sun samu babbar nasara kan ’yan ta’adda, inda suka halaka aƙalla ’yan ta’adda 62 ciki har da shahararrun kwamandojin ISWAP guda biyar, bayan sun fatattake a hare-haren da aka kai musu a sansanonin soji daban-daban a jihohin Borno da Yobe — abin da aka bayyana a matsayin babban nasarar soja mafi girma a shekarar 2025. Hare-haren da suka faru ne a lokaci guda tsakanin ƙarfe 12 na dare zuwa 4 na safe a ranar Alhamis, inda mayaƙan ISWAP suka aaddamar da gagarumin hari kan sansanonin soji a Dikwa, Mafa, Gajibo da…
Read More
Jiga-jigan PDP na Arewa sun cimma matsaya kan Kabiru Turaki a matsayin shugaban jam’iyya

Jiga-jigan PDP na Arewa sun cimma matsaya kan Kabiru Turaki a matsayin shugaban jam’iyya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Ministan Harkokin Musamman da Dangantakar Gwamnatoci, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa bayan cimma matsayar haɗin kai tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar daga arewacin ƙasar. Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ne ya sanar da fitowar Turaki a matsayin sabon shugaban jam’iyyar a wani taro da aka gudanar a Abuja daren Laraba, 22 ga Oktoba, 2025. An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa mai zurfi da aka yi tsakanin shugabannin jam’iyyar daga arewa, domin ƙarfafa haɗin kai da daidaiton cikin gida kafin babban taron jam’iyyar da ke tafe a shekarar…
Read More
Za a yi gumurzu a zaɓen 2027 – Kwankwaso

Za a yi gumurzu a zaɓen 2027 – Kwankwaso

*A shirye muke mu yi haɗaka, inji shi Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar kujerar Shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi hasashen cewa zaɓen 2027 zai kasance mafi tsanani a tarihin dimokuraɗiyyar Nijeriya, kamar yadda ya bayyana cewa jam’iyyarsa a shirye take ta ƙulla ƙawance da sauran jam’iyyun siyasa ciki har da shugaban ƙasa Bola Tinubu da Peter Obi na jam’iyyar Labour. Da yake magana a wata hira da BBC Hausa da Blueprint Manhaja ta sa ido, Kwankwaso, wanda a kwanan…
Read More
Remi Tinubu ta ƙaddamar da cibiyar dijital a Zamfara

Remi Tinubu ta ƙaddamar da cibiyar dijital a Zamfara

Daga MUHAMMAD SANUSI a Gusau Uwargidan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da cibiyar hada-hadar karatu ta dijital watau E-learning Library Center na miliyoyin Naira a yau Alhamis a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Uwargidan shugaban ƙasar kuma shugabar shirin sabunta ƙasa ta bayyana cewa an kuma kafa cibiyoyin a jihohi 10 domin bunƙasa fasahar E-Learning na dijital a tsakanin ɗalibai. Sen. Remi Tinubu wadda ta samu wakilcin uwargidan gwamnan jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda Lawal a wajen taron, ta bayyana cewa a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da haɗin gwiwar hukumar bunƙasa fasahar…
Read More
An rantsar da sabbin kwamishinoni da manyan sakatarori a Katsina

An rantsar da sabbin kwamishinoni da manyan sakatarori a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya rantsar da sabbin Kwamishinoni uku da kira a gare su da a ko da yaushe su yi aiki da gaskiya da riƙon amana. Ya ja hankalinsu da su ɗauki muƙamansu a matsayin nauyin amanar jama’a, ba wata hanya ta azurta kan su ba. An gudanar da bikin rantsuwar ne a fadar gwamnati ta Katsina, inda manyan jami’an gwamnati, sarakuna da ‘yan uwa na waɗanda aka naɗa suka halarta. Sabbin kwamishinonin sun haɗa da Hon. Yusuf Suleiman Jibia, Hajiya Aisha Aminu, da Injiniya (Dr.) Sirajo Yazid Abukur. Gwamna Raɗɗa ya yabawa Hon.…
Read More
Jami’ar British American University ta karrama shugabanni kamfanin ASIA a Kano

Jami’ar British American University ta karrama shugabanni kamfanin ASIA a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban kuma wanda ya assasa kamfanin ASIA Group of Companies wato Alhaji Sani Isah Abubakar (ASIA) ya samu Digirin Girmamawa na (Doctor of Excellence – Honoris Causa) daga British American University, a matsayin yabo bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban kasuwanci, jagoranci, da ayyukan jin ƙai. An gabatar da wannan taron lambar yabo ne a wani biki da kamfanin ASIA Group ya shirya a garin Kano ranar Alhamis, wanda ya ja hankalin manyan baƙi, sarakunan gargajiya, shugabannin kasuwanni da fitattun mutane daga sassan ƙasar nan. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa…
Read More
Majalisar Dokokin Katsina ta amince da gina dam a Matazu

Majalisar Dokokin Katsina ta amince da gina dam a Matazu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta amince da gina Dam a garin Unguwar Mai Yaji a mazaɓar Karaduwa a ƙaramar hukumar Matazu. A zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar Rt.Hon.Nasir Yahaya Daura, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Matazu Hon. Ibrahim Dikko ya gabatar da ƙudurin akan a gina Dam a garin Unguwan Mai Yaji a mazaɓar Karaduwa a ƙaramar hukumar Matazu. Ya bayyana cewa samar da madatsar ruwa a wannan wuri zai taimaka wajen noman rani da wadata al'ummar Mai Yaji da sauran garuruwan yankin da ruwan sha. Haka zalika majalisar ta amince da gyaran…
Read More