ukarofi

12715 Posts
Makiran Arewa: Gwagwarmaya ko damalmala?

Makiran Arewa: Gwagwarmaya ko damalmala?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA  Har yanzu alkalamina na kan wasu ‘yan bazata da ke biyowa ta bayan gida don yin maƙarƙshiya ga zaman lafiya a tsohon Lardin Arewacin Nijeriya. Hakika duk Lardi na da iyaye har ma da kakanni da mutanen kirki ke alfahari da girmama su. A ɓangaren waɗannan ‘yan bazata na Arewa aibanta shugabannin da su ke da amfani da labaru na shaci-faɗi da murɗe wuyan tarihi don cimma miyagun muradunsu. Duk mai yawo a dandalin yanar gizo da ya shafi Arewa zai ci karo da waɗannan mutanen da akasarinsu matasa ne. Ba lallai dukkansu na cikin Nijeriya…
Read More
Muhallin darbejiya a gyaran jiki (2)

Muhallin darbejiya a gyaran jiki (2)

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja.  Idan kuna bibiye da mu za ku tuna a wancan mako mun faro shimfiɗa kan muhimmanci da amfanin darbejiya ga jiki. Kuma mun sanar da ku darasin bai ƙare ba, domin za mu kawo maku muhimmancin sa ga fata da yadda zai iya gyara ta. A cikin duniyar mata 'yan ƙwalisa, masu kula da kyau da lafiyar jiki, an daɗe ana yabon iccen darbejiya, wato neem tree, a matsayin ɗaya daga cikin kyautukan da Allah ya ba wa fatar jikin mace.…
Read More
Gwamnatin Katsina ta kashe Naira biliyan 113.51 wajen gina hanyoyi

Gwamnatin Katsina ta kashe Naira biliyan 113.51 wajen gina hanyoyi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙarƙashin shirin "Urban Renewal" gwamnatin Katsina ta kashe fiye da Naira biliyan 113.51 wajen gina hanyoyi a manyan biranen Katsina, Funtua da Daura. Hanyoyin sun ƙunshi gina EASTERN BYPASS da sha tale tale, tagwayen hanyoyi da gadoji, kwalbatoci da sanya fitillu masu amfani da hasken rana a titunan. Darakta mai kula da aikin hanya na ma'aikatar ayyuka da gidaje na jihar Injiniya Falalu Hussaini ya shaidawa manema labarai haka a ofishin sa a Katsina. Ya ce a Birnin Katsina kawai wanda itace babban birni, cikin wannan adadi, gwamnati ta kashe Naira biliyan 74.95 wajen gina…
Read More
Gwamnatin Najeriya za ta mayar da Katsina cibiyar kasuwanci – Shettima

Gwamnatin Najeriya za ta mayar da Katsina cibiyar kasuwanci – Shettima

Daga UMAR GARBA a Katsina Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da tallafin Naira 250,000 ga ƙananan 'yan kasuwa da matsaƙiitan masana’antu (MSME) da suka nuna bajinta a yayin babban taron ƙanana da matsaƙaitan masana’antu na ƙasa (Eɗpanded National MSME Clinic) da aka gudanar a Katsina. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya sanar da hakan yayin ƙaddamar da taron karo na tara, wanda aka shirya don tallafawa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i da kuma farfaɗo da tattalin arziƙin al’umma Shettima ya bayyana cewa an samar da shirin ne domin kawo hukumomin gwamnati kusa da masu sana’a da…
Read More
JIBWIBS a Katsina ta shirya taron horar da malamai domin tabbatar da zaman lafiya

JIBWIBS a Katsina ta shirya taron horar da malamai domin tabbatar da zaman lafiya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatis Sunnah (JIBWIS) ta Jihar Katsina ta gudanar da taron horas da malamai da limamai daga yankunan da ke fama da matsalar tsaro, musamman inda aka samu yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga. An gudanar da taron ne a masallacin Juma’a na cibiyar horas da limamai da masu Khuduba ta Al-Wasil da ke kan hanyar Batsari. Da yake jawabi yayin buɗe taron, sshugaban JIBWIS na Jihar Katsina, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan (Sautus-Sunnah), ya ce manufar horaswar ita ce faɗakar da malamai da limamai kan muhimmancin tabbatar da zaman lafiya, haƙuri…
Read More
Aikin jarida da rubutun adabi na tafiya kafaɗa da kafaɗa – Hajaru Baba Sakkwato

Aikin jarida da rubutun adabi na tafiya kafaɗa da kafaɗa – Hajaru Baba Sakkwato

"Gudunmawar marubuta wajen gyaran al'umma ba kaɗan ba ce" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Malama Hajaru Abdullahi Baba fitacciyar 'yar jarida ce da ke aiki a tashar rediyo ta ɓision FM a garin Sakkwato Birnin Shaihu. Marubuciya ce da ta samu nasarar wallafa littafin ta na farko mai suna 'Kishiyar mafalki' kimanin shekaru goma da suka gabata, amma halayyar wasu 'yan kasuwar littattafan Hausa marasa tausayi ya sa ta tsorata da harkar buga littafi, ta koma tunanin sakin rubuce-rubucen ta na gaba a yanar gizo wato 'online' kawai. A tattaunawar ta da Blueprint Manhaja, marubuciyar wacce kuma har wa yau 'yar…
Read More
Shettima ya ƙaddamar da babban taron ƙanana da matsakaitan sana’o’i karo na tara a Katsina

Shettima ya ƙaddamar da babban taron ƙanana da matsakaitan sana’o’i karo na tara a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima tare da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa sun ƙaddamar da babban taron tallafawa ƙanana da matsakaitan masana’antu na ƙasa karo na 9 (Expanded National MSME Clinic) a birnin Katsina. Taron ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci da ci gaban masana’antu, domin ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasa ta hanyar bunƙasa ƙananan ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mataimakin shugaban ƙasa tare da Gwamna Raɗɗa sun ziyarci rumfunan da aka baje kolin kayayyakin MSME, inda suka gana da ’yan kasuwa masu gabatar da sabbin kayayyaki da fasahohi…
Read More
Gwamnatin Kano ta bayyana lokacin da za ta kammala aikin gadojin sama na Tal’udu da Ɗan Agundi

Gwamnatin Kano ta bayyana lokacin da za ta kammala aikin gadojin sama na Tal’udu da Ɗan Agundi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta na kammala manyan ayyukan gine-gine da nufin inganta walwalar jama’a. Kwamishinan sashen kula da ayyuka, Nura Ma’aji, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Talata, bayan duba wasu ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa a faɗin jihar. A cewar sa, aikin gina gadar sama ta Ɗan Agundi da ta Tal’udu zai kammalu kafin ƙarshen watan Disamba. Ma’aji ya ce an riga an biya diyya da warware duk wasu batutuwan da suka shafi aikin domin tabbatar da kammalawarsa a kan lokaci. Ya…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya bayyana shirye-shiryen ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa matasa a Katsina

Gwamna Raɗɗa ya bayyana shirye-shiryen ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa matasa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, bisa irin jagorancin hangen nesa da yake bayarwa wajen inganta ƙirƙire ƙirƙire, sana’o’i da kuma bai wa matasa damar ci gaba. Shettima ya bayyana Jihar Katsina a matsayin "fitila ta ƙirƙira da juriya a Arewacin Nijeriya," yana mai cewa jihar na farfaɗo da tsohon gadon ta na ilimi, kasuwanci da fasaha. Yayin da yake jawabi a bikin kammala karatun Dikko Social Innovation Academy (DSIA) da kuma ƙaddamar da kyaututtukan Katsina MSME karo na farko a ɗakin taro na gidan gwamnati,…
Read More
Bai kamata mata su rungume hannu komai sai an yi masu ba – Bilkisu Beely 

Bai kamata mata su rungume hannu komai sai an yi masu ba – Bilkisu Beely 

"Idan kina yi wa kanki yan buƙatu har son ki sai ya ƙaru wurin mijinki" Daga UMAR GARBA, a Katsina  Bilkisu Yunusa matashiyar 'yar kasuwa ce da ta yi fice a fannin sana'o'i iri daban daban, bata tsaya a nan ba domin kuwa matashiyar ta na koyar da matasa maza da mata dabarun kasuwanci na zamani. Wakilin Blueprint Manhaja a Katsina Umar Garba, ya zanta da Bilkisu Beely game da batutuwan da suka shafi dabarun kasuwanci a kafafen sada zumunta, yadda take koyar da wasu matan ƙananan sana'o'i a ajujuwan 'online', ta kuma ba wa matasa maza da mata shawara…
Read More