ukarofi

12715 Posts
Majalisar Dokokin Katsina ta tabbatar da Yusuf Jibia da Aisha Aminu a matsayin kwamishinoni

Majalisar Dokokin Katsina ta tabbatar da Yusuf Jibia da Aisha Aminu a matsayin kwamishinoni

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta tabbatar da naɗin Hon Yusuf Suleiman Jibiya da Hajiya Aisha Aminu a matsayin Kwamishinoni a majalisar zartarwa ta Jihar Katsina, bayan da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa, ya gabatar da sunayensu domin tantancewa da amincewa. An tabbatar da naɗin ne bayan zaman tantancewa da aka gudanar a zauren majalisa, inda ’yan majalisar suka yaba da gogewar su, ƙwarewa, da jajircewarsu wajen gudanar da ayyukan gwamnati. Hon. Yusuf Suleiman Jibia gogaggen ma’aikacin gwamnati ne kuma kwararren jami’i wanda ya riƙe muhimman muƙamai da dama a gwamnatin jihar Katsina, ciki har da Kwamishinan…
Read More
An ƙaddamar da ƙungiyar Musa Adamu Funtua Network for Gwagware Countinuity 2027

An ƙaddamar da ƙungiyar Musa Adamu Funtua Network for Gwagware Countinuity 2027

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamred Mannir Suleiman shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua shine sabon shugaban ƙungiyar tare da mutane 11. Da yake jawabi bayan da ya amshi ragamar shugabancin ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman ya nuna jin daɗin na yadda ya ga mutane masu mutunci masu ƙima kuma ya ƙara da cewa" fuskokin da ya gani dama "irinsu muke son muyi aikin wannan ƙungiya tare dasu", a cewar sa. Manufar wannan ƙungiya, ƙungiya ce wadda za ta bada nata gudunmawa wajen taya Gwamna DIkko Raɗɗa yaƙin neman zaɓe a karo na biyu duba da Irin cikin ɗan lokaci kaɗan ya…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Katsina ya ƙaddamar da gyaran asibitin Ƙofar Durɓi

Shugaban ƙaramar hukumar Katsina ya ƙaddamar da gyaran asibitin Ƙofar Durɓi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A ƙoƙarin da ya ke yi domin inganta harkar lafiya, shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya ƙaddamar da aikin gyaran Asibitin Ƙofar Durbi Kwanar Yan Lemo da ke cikin mazaɓar Wakilin Gabas 1 cikin garin Katsina. Da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamarwar, Hon. Miqdad ya bayyana cewa aikin zai gudana ne cikin matakai biyu domin tabbatar da cikakken gyara mai ɗorewa da inganci. Ya ce a Kashi na farko, aikin zai haɗa da gina katangar zagaye, cikakken gyaran gine-ginen da suka lalace, tare da samar da muhimman kayan aikin asibiti…
Read More
Juyin mulki: Ana zargin tsohon gwamna da ɗaukar nauyin sojoji

Juyin mulki: Ana zargin tsohon gwamna da ɗaukar nauyin sojoji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Leƙen Asirin Soji ta Nijeriya (DIA) tana gudanar da bincike kan wani tsohon gwamna bisa zargin sa da ɗaukar nauyin sojoji da nufin yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki.Majiyoyin Blueprint Manhaja sun bayyana cewa akwai zargi mai ƙarfi cewa tsohon gwamnan, wanda ɗan asalin yankin Kudu ne kuma tsohon babban jami’in gwamnati a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas ne, ya ɗauki nauyin yunƙurin juyin mulkin, wanda da aka shirya aiwatarwa a ranar 25 ga watan Oktoban nan da muke ciki. A ƙarshen mako ne kafofin watsa labarai na Sahara Reporters…
Read More
Zargin sauya sheka: APC a Zamfara ta musanta kafa kwamitin maraba da Gwamna Dauda

Zargin sauya sheka: APC a Zamfara ta musanta kafa kwamitin maraba da Gwamna Dauda

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen Jihar Zamfara ta bayyana labaran dake yawo cewar ta kafa kwamitin karɓar Gwamnan Jihar Dr. Dauda Lawal a matsayin soki burutsu da Kuma ƙirƙira Karya tsagwaron ta. Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na jihar, Yusuf Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa Blueprint Manhaja yau Lahadi a Gusau babban birnin Jihar. A cewar sanarwar, rahotannin sun nuna rashin kishin ƙasa da ƙage ta hanyar munanan manufofin marubuta da kafafen yaɗa labarai. Ya ce, jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ba ta taɓa tunkarar jam’iyyar PDP…
Read More
Ashraf Mahrous: Jarumin ɗan Masar da ya ja jirgi mai nauyin tan 700 da haƙoransa

Ashraf Mahrous: Jarumin ɗan Masar da ya ja jirgi mai nauyin tan 700 da haƙoransa

Wani ɗan dambe daga ƙasar Masar mai suna Ashraf Mahrous ya jawo hankalin duniya bayan da ya ja jirgi mai nauyin tan 700 (kusan kilo 635,000) da haƙoransa a gaɓar tekun Hurghada da ke yankin Bahar Maliya. Mahrous, wanda ake kira “Kabonga”, kuma aka fi saninsa da laƙabin “Jarumi Mai ƙarfi” a Masar, ya kuma ci gaba da jan wasu jiragen ruwa biyu tare da nauyin tan 1,150 (fiye da kilo miliyan ɗaya) gaba ɗaya. “Na zo yau domin kafa tarihi a duniya,” inji Mahrous bayan gwajin. “Na jawo su duka, da taimakon Allah, domin in tabbatar wa duniya cewa…
Read More
Magidanci ya sayar da ɗansa kan miliyan N1.5

Magidanci ya sayar da ɗansa kan miliyan N1.5

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan ƙaramar Hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kan Naira Miliyan 1.5. An gano cewa Onwe ya sayar wa wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu jaririn, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje. Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa matar Onwe, mai suna Philomena Iroko, ce ta fallasa shi bayan ta samu labari daga maƙwabta cewa mijinta ya sayar da jaririn da suka haifa. Da ta tabbatar da hakan, sai ta garzaya ta kai rahoto…
Read More
Daulolin da Fulani suka yi nasarar kafawa a tarihi

Daulolin da Fulani suka yi nasarar kafawa a tarihi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mutanen Fula sun taimaka sun kafa dimokiraɗiyya da yawa na tarihin Islama kuma sun jagoranci yawancin Jihadi kamar Masina a ƙarni na 19. Masarautar Maasina wacce ake kira ‘Diina’ a Fulfulde, tare da asalin Larabci, an kafa ta ne ta hanyar jihadin Fulbe wanda Sheeku Aamadu ya jagoranta a 1818. Asalin masarautar Maasina a cikin Inner Delta na Niger shima ana samunsa a tawaye, a wannan karon kan Masarautar Bambara/Bamana na Segou, ikon siyasa wanda ke sarrafa yankin daga waje. Wannan jihadi ya sami karɓuwa ne daga abubuwan da suka faru a arewacin Nijeriya inda wani…
Read More
Dangote bai taɓa shigo da man da bai cika ƙa’ida ba – IIP

Dangote bai taɓa shigo da man da bai cika ƙa’ida ba – IIP

Daga MAHDI MUSA MUHAMMADl Kungiyar Masu Binciken Harkokin Man Fetur Mai Zaman Kanta da ke ƙasar Ingila (IIP), ta ce ba ta samu wani hujja da ke nuna cewa Kamfanin Tace Mai na Dangote ya shigo da man fetur mara inganci cikin Nijeriya ba, tana mai bayyana irin waɗannan zarge-zargen a matsayin “marasa tushe, marasa ma’ana, kuma ba su da hujjar da za a iya tabbatarwa.” A cikin wani rahoto da jagoran binciken ƙungiyar, Raymond Neil, ya sa hannu a kai a ranar Juma’a, IIP ta bayyana cewa binciken da ta gudanar kan bayanan jigilar kaya, takardun kwastom da kuma…
Read More
Iyalan da suka amfana da tallafin gwamnati sun kai miliyan takwas – Ministan Jinƙai

Iyalan da suka amfana da tallafin gwamnati sun kai miliyan takwas – Ministan Jinƙai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta raba fiye da Naira Biliyan 300 ga iyalai sama da miliyan takwas a faɗin ƙasar nan ta hanyar shirin Conditional Cash Transfer (CCT) — wani shiri da ke nufin rage talauci da inganta rayuwar al’umma. ƙaramin Ministan Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Yusuf Tanko Sanunu, ne ya bayyana hakan a taron tattaunawa da aka gudanar a Abuja domin tunawa da Ranar Rage Illolin Bala’o’i ta Duniya, a ranar Litinin. Sanunu ya ce, wannan ci gaba wani ɓangare ne na Hope Agenda na Shugaba Bola Tinubu, wanda ya mayar da…
Read More