ukarofi

12715 Posts
Yajin aikin PENGASSAN ya durƙusar da samar da fetur a Satumba – NUPRC

Yajin aikin PENGASSAN ya durƙusar da samar da fetur a Satumba – NUPRC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta ƙasa (NUPRC) ta bayyana cewa, adadin samar da ɗanyen mai a Nijeriya ya faɗi zuwa matsakaicin ganga miliyan 1.581 a kowace rana a watan Satumbar 2025 a sakamakon yajin aikin da aka gudanar a fannin. A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Asabar ta hannun mai magana da yawunta, Eniola Akinkuotu, an bayyana cewa wannan koma baya ya samo asali ne daga yajin aikin kwana uku da ƙungiyar Ma’aikatan Mai da Iskar Gas (PENGASSAN) ta gudanar, wanda ya jawo rufe wasu muhimman cibiyoyin samar da mai da tashoshin…
Read More
Yadda farashin zinari ya kai matsayin da bai saba kaiwa ba

Yadda farashin zinari ya kai matsayin da bai saba kaiwa ba

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Farashin zinari ya yi tashin gwauron zabi zuwa sabon matsayi na tarihi — Dala 4,070 a kowace ounce a ranar Litinin, sakamakon ƙaruwa wajen buƙatar masu zuba jari da ke neman mafaka a cikin rashin tabbas na tattalin arzikin duniya. Masana kasuwa sun danganta wannan tashin farashin da tsoron raguwar tattalin arziki, rikice-rikicen kasuwanci tsakanin ƙasashe, da kuma tashe-tashen farashin hannayen jari da musayar kuɗi. Masu saka jari suna ƙara karkata zuwa zinari a matsayin madogara mai aminci don kare jarinsu daga girgizar kasuwa da rashin tabbas da ke yaɗuwa a duniya. Wannan hauhawa da ba…
Read More
IMF ta gargaɗi Nijeriya da sauran ƙasashe su rage dogaro da bashi

IMF ta gargaɗi Nijeriya da sauran ƙasashe su rage dogaro da bashi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya buƙaci Nijeriya da sauran ƙasashe masu tasowa da su rage yawan bashin da suke ɗauka, yana mai cewa tarin bashi mai yawa na “hana tattalin arziki numfashi.” Shugabar IMF, Kristalina Georgieɓa, ta bayyana haka ne a ranar Litinin yayin taron tattaunawa da ƙungiyoyin fararen hula (CSO) a taron shekara-shekara na Babban Bankin Duniya da IMF da ke gudana. A ranar 12 ga Oktoba, Hukumar Kula da Bashi ta ƙasa (DMO) ta sanar da cewa jimillar bashin Nijeriya ya kai tiriliyan N152.39 zuwa ranar 30 ga Yuni. Daga ciki,…
Read More
Matakan samun sana’a da yadda za ka yi nasara kashi na ɗaya

Matakan samun sana’a da yadda za ka yi nasara kashi na ɗaya

Tare da BILKISU YUSUF ALI, PhD 08054137080, [email protected] Gabatarwa Sana’a tana daga cikin muhimman hanyoyin da matasa da kowa zai iya dogaro da kai ta hanyar samun abin dogaron rayuwa. Amma samun nasara a sana’a na bukatar bin wasu matakai na musamman, kiyaye ka’idoji, da sanin hanyoyin rage asara. Wannan makala za ta yi bayani dalla-dalla kan matakan samun sana’a, yadda za ka yi nasara, hanyoyin rage asara, ka’idojin sana’a, da muhimmancin sana’a. Matakan samun sana’a: 1. Neman ilimi da horarwa Samun ilimi a fannin da kake son sana’a shi ne mataki na farko. Za ka iya samun horo a…
Read More
Raddina ga Malam Lawan Triump

Raddina ga Malam Lawan Triump

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Mudassir Bello Tudun Wada ya janyo hankali na zuwa ga wani Bidiyo da Mubarak Ibrahim Lawan ya saka a shafinsa mai mintuna 4 da dakikoki 2 inda Malam Lawan Triump ya bada bayanin raddi da Marigayi Sheikh Jafar ya min bayan na yi masa raddi akan taƙaddama a game da husufi na rana ko wata a shekarar 2006. Malam Lawan ya yi nasa raddin, yadda su ka saba yi, ba tare da kawo kwararan hujjoji ba sai babatu da kokarin cin fuska. Zan yi kokari na kawo labarin tun asalinsa da irin hujjojin da na baiwa…
Read More
An ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro Jihar Karaɗua a matakin ƙananan hukumomi na shiryar Funtua

An ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro Jihar Karaɗua a matakin ƙananan hukumomi na shiryar Funtua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban kwamatin neman Jihar Karaɗua daga cikin Jihar Katsina, Alhaji Kabir Aliyu Maska ​, ya ƙaddamar da Kodinetoci 11 na ƙananan hukumomin shiyar domin faɗaɗa ayyukan su na neman Jihar Karaduwa.  A jawabinsa lokacin da yake ƙaddamar da ko'odinetocin, shugaban babban kwamitin zartarwar Alhaji Kabir Aliyu Maska ya bayyana cewa, a yayin taronsu na zartaswar an yanke shawarar a bai wa kodinetoci alhakin tafiyar da al’amuran ƙananan hukumomin su, dan samun gudunmuwa ta kowa da kowa dan ganin "haƙar mu ta cimma ruwa na neman Jihar Karaduwa,"Inji Maska . Ya bayyana cewa duk da wasu…
Read More
Hukumar tsara birane ta fara tayar da waɗanda suka mamaye gefen hanyoyi a Katsina

Hukumar tsara birane ta fara tayar da waɗanda suka mamaye gefen hanyoyi a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar tsara birane daJihar Katsina (URPB) ta fara tayar da waɗanda suka mamaye gefen hanyoyi da jikin bangayen gine-ginen gwamnati da sauran inda doka ta hana kasa kayan saye da sayarwa. Wuraren da abun ya shafa sun haɗa da shatatalen High Court zuwa hanyar Daura da titin Sarki Abdulraman da kan kwanar High Court. Sauran wuraren sune kan titin mai Shari'a Mohd Bello da na Isah Kaita kusa da gadar sama da ke GRA da wuraren da ake sana'o'i a jikin bangayen wasu ma'aikatu gami da jikin gadar sama da ke GRA nan cikin birnin…
Read More
A gaggauta sakin ɗan jarida, Ɗan Uwa Rano ba tare da sharaɗi ba – CIPP

A gaggauta sakin ɗan jarida, Ɗan Uwa Rano ba tare da sharaɗi ba – CIPP

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Daraktan cibiyar kula da gaskiya da kare haƙƙin ’yan jarida wato Center for integrity and press protection Nigeria (CIPP), Olumide Adekunle, ya bayyana kamawa tare da tsare ɗan jarida Ibrahim Ishaq (Danuwa Rano), da ’yan sandan Kano suka yi a matsayin abin da ya saɓawa doka. Ana zargin ɗan jaridar da laifukan da suka haɗa da ɓata sunan daraktan karɓar baƙi na gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, da kuma gudanar da tashar YouTube ta Ɗan'uwa Rano TV ba tare da samun amincewar hukumar NBC ba. A cewar CIPP, hukumar NBC tana da hurumin kula da…
Read More
Al’ummar Dutsi sun karrama shugaban ƙaramar hukumar

Al’ummar Dutsi sun karrama shugaban ƙaramar hukumar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Al’ummar garin Dutsi da kewaye sun karrama Shugaban ƙaramar hukumar Dutsi, Hon Abdulrazak Adamu Kayawa, da kyautar katon Rago da kuma Alƙur’ani mai tsarki, a matsayin yabo da godiya bisa irin ayyukan alheri da ci gaba da yake gudanarwa a yankin. Taron karramawar ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Hakimin Dutsi, tare da Dattijo Alhaji Jabiru Ibrahim Dutsi, inda manyan mutane, malamai, matasa da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin suka halarta. A cewar wasu daga cikin al’ummar yankin, Hon. Abdulrazak Adamu Kayawa ya gudanar da muhimman ayyuka da suka hada da, gina fanfuna da…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya jagoranci tawagar gwamnatin Katsina zuwa taron makamashi a ƙasar Maroko

Gwamna Raɗɗa ya jagoranci tawagar gwamnatin Katsina zuwa taron makamashi a ƙasar Maroko

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya tabbatar da ƙudirin gwamnatin sa na inganta harkar wutar lantarki ta hanyar haɗin guiwa da amfani da sabbin fasahohi. Dikko ya faɗi haka ne a lokacin da ya halarci taron kwana biyu tare da gwamnonin Kano da Jigawa da jami'an kamfanonin KEDCO da Future Energies Africa a birnin Marrakech na ƙasar Maroko. Taron ya mayar da hankali kan yadda za'a samar da wuta ga yankunan da ba su da hasken lantarki, inganta tashoshin samar da lantarki, kawar da ƙarancin lantarki, da kafa hukuma ta bai ɗaya da za…
Read More