ukarofi

12738 Posts
2027: NNPP za ta tattauna kan yiwuwar marawa Tinubu baya ko shiga ƙawance a taronta na ƙoli 

2027: NNPP za ta tattauna kan yiwuwar marawa Tinubu baya ko shiga ƙawance a taronta na ƙoli 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar NNPP na shirin yanke hukunci kan muhimman abubuwa a taron Kwamitin Zartarwa na ƙasa (NEC) da za ta gudanar a ranar Alhamis, 28 ga Agusta, 2025 a birnin Abuja.  Jaridar Tribune ta rawaito cewa alamomi sun nuna za a ɗauki manyan matakai a wannan taro yayin da jam’iyyar ke tsara dabaru gabannin zaɓen 2027. A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson, ya fitar, an bayyana cewa taron zai tattauna kan babban taron jam’iyya, duba zaɓen cike gurbi na baya-bayan nan, da kuma tattauna dabarun wayar da kan…
Read More
APC ta dakatar da tsohon gwamnan Ogun Gbenga Daniel kan zarge-zargen cin hanci da rashawa

APC ta dakatar da tsohon gwamnan Ogun Gbenga Daniel kan zarge-zargen cin hanci da rashawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), reshen jihar Ogun, ta dakatar da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar Ogun ta Gabas, Gbenga Daniel. An dakatar da tsohon gwamnan ne tare da ɗaya daga cikin masu yi masa biyayya, Kunle Folarin bisa zargin rashin ɗa’a ga jam’iyyar. Nuberu Olufemi, mai magana da yawun jam’iyyar APC a Ogun, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (SWC) ya amince da dakatar da Daniel da Folarin a ranar Talata. Olufemi ya ce an kafa kwamitin ladabtarwa a gunduma ta 4…
Read More
Da wahala Kwankwaso ya goyi bayan Tinubu a 2027 – Buba Galadima

Da wahala Kwankwaso ya goyi bayan Tinubu a 2027 – Buba Galadima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Buba Galadima ya ce zai yi wahalar gaske Kwankwaso ya haɗa hannu da jam'iyyar APC domin samun nasarar Bola Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027. Buba Galadima ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da tashar Channels a shirinta na Politics Today wanda aka yi a ranar Litinin, inda ya ce gwamnatin Tinubu tana takalar Kwankwaso, musamman wajen goyon bayan Sarki Aminu Ado Bayero, duk da gwamnatin jihar ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta cire shi. Da aka tambaye shi cewa…
Read More
 PDP ta buƙaci kotu ta kori wasu ‘yan majalisar tarayya huɗu bisa zargin sauya sheƙa zuwa APC

 PDP ta buƙaci kotu ta kori wasu ‘yan majalisar tarayya huɗu bisa zargin sauya sheƙa zuwa APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Larabar da ta gabata ne Jam’iyyar PDP ta buƙaci babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin korar wasu ‘yan majalisa huɗu da ke wakiltar jihar Osun a majalisar dokokin ƙasar, bisa zarginsu da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar All Progressiɓes Congress, APC. PDP ta gabatar da buƙatar ne a wasu ƙararraki guda huɗu masu ɗauke da kwanan wata 20 ga watan Agusta wanda lauyanta Rapheal Oyewole ya shigar. ‘Yan majalisar dai sun haɗa da sanatoci biyu da ‘yan majalisar wakilai biyu. Su ne Sanata Francis Fadahunsi mai wakiltar Osun ta…
Read More
Sabon harin ’yan bindiga a Malumfashi: Ƙalubale ga jami’an tsaron Nijeriya

Sabon harin ’yan bindiga a Malumfashi: Ƙalubale ga jami’an tsaron Nijeriya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A cikin 'yan shekarun nan, matsalar 'yan bindiga na cigaba da zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta, musamman a arewacin ƙasar nan. Harin da aka kai garin Malumfashi a Jihar Katsina na daga cikin fitattun abubuwan da suka tayar da hankalin al'umma, suke kuma ƙara sanya tsoro da firgici a zukatan jama'a. Babu shakka wannan harin ya janyo asarar rayuka, rushewar tattalin arziƙi da barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma. Idan za a iya tunawa a ranar Laraba ne gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar masallata 32 a dalilin mummunan…
Read More
Rundunar sojin sama ta tarwatsa maɓoyar Babaro tare da ceto mutane 76 Katsina

Rundunar sojin sama ta tarwatsa maɓoyar Babaro tare da ceto mutane 76 Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta kai mummunan farmaki a maɓoyar fitaccen shugaban ɓarayin daji, Babaro, a tsaunin Pauwa da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara, inda ta ceto mutane 76 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da yara. Babaro da tawagarsa na daga cikin waɗanda ake zargi da shirya kai mummunan harin baya-bayan nan a Unguwar Gidan Mantau, ƙaramar hukumar Malumfashi. Harin da sojojin saman suka kai a Ƙanƙara,sun lalata sansanin da ya dade yana zama barazana ga al’ummomin yankin. Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta tabbatar da cewa, cikin…
Read More
Kwamitin faɗakar da al’umma mahimmanci mallakar katin zaɓe ya ziyarci shugaban hukumar zaɓe na Kano

Kwamitin faɗakar da al’umma mahimmanci mallakar katin zaɓe ya ziyarci shugaban hukumar zaɓe na Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Kwamitin da gwamnatin Jihar Kano ta kafa Kan faɗakar da al'ummar Jihar Kano batun mahimmancin mallakar Katin zaɓe a jiya Juma'a ƙarƙashin Shugabancin kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin Gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fara ziyartar shugaban hukumar zaɓe na Jihar Kano Ambassada Zango A Abdu. Da yake jawabi yayin ziyarar Shugaban kwamitin Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya yace dalilin wannan ziyara itace samun haɗin gwiwa wajen yadda aikin wannan kwamiti zai kasance matsayin su na hukumar zaɓe bai ɗaya ta Jihar Kano. Kwamared Ibrahim Waiya ya kuma bayyana cewa mai girma Gwamna Abba Kabir…
Read More
Ƙungiyar gwamnonin PDP ta yi Allah-wadai da kashe-kashen da ake yi a jihohi

Ƙungiyar gwamnonin PDP ta yi Allah-wadai da kashe-kashen da ake yi a jihohi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da yadda ƴan ta'addan su ke ci gaba da kashe-kashen al'umma a jihohin Katsina, Filato, Neja da Benuwai da kuma wasu sassan Nijeriya. Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara kula da rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa. Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ƙarshen taronsu a Gusau yau Asabar. Hakazalika a ranar 9 ga watan Agustan shekarar 2025 ne aka gudanar da zaɓen cike gurbi na ƙasa baki ɗaya, ƙungiyar…
Read More
Gwamna Sule ya raba motoci masu aiki da wutar lantarki ga mabuƙata a Nasarawa

Gwamna Sule ya raba motoci masu aiki da wutar lantarki ga mabuƙata a Nasarawa

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya raba wasu sabbin motocin zamani masu aiki da wutar lantarki guda 50 da wasu adaidaita sahu suma masu aiki da wutar lantarki 100 ga matasa da marasa galihu don bunƙasa tattalin arziki da kuma samar da ayukan yi a jihar. Gwamna Sule a jawabin sa yayin da yake rarraba motocin ga waɗanda suka amfanar a Lafia, fadar jihar ya bayyana cewa rabon na da manufar samar ma waɗanda suka amfana ɗin damar gudanar da ayukan sufuri da motoci da kuma adaidaita sahun a matsayin kasuwanci, don haka…
Read More
An yi kira ga shugaban NLC na ƙasa ya bada tasa gudunmawar wajen samar da tsaro a Arewacin Nijeriya

An yi kira ga shugaban NLC na ƙasa ya bada tasa gudunmawar wajen samar da tsaro a Arewacin Nijeriya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamred Mannir Suleiman tsohon shugaban ƙungiyar ma'aikatan kiwon lafiya na ƙasa reshen Jihar Katsina a wata hira da manema labarai a Katsina ya bayyana. Ya ce wajibi ne shugaban ƙungiyar ƙwadago na ƙasa Mr Joe Ajero ya bi ta ƙungiyar sa wajen lalubo hanyoyi da za a bi a dawo da zaman lafiya a Arewacin ƙasar. "Ina kira ga ƙungiyoyin ƙwadago,addinai, siyasa da manyan Arewa su haɗu cikin gaggawa domin lalubo hanyoyi da za a bi a magance ta'addanci tun kafin durƙushewar Arewacin ƙasan,"Inji kwamred Suleiman. Kwamred Mannir Suleiman wanda harwala yau shine shugaban ƙungiyar…
Read More