24
Aug
Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta ce sojojin sama sun kai samame, inda suka samu nasarar tarwatsa maɓoyar ɗan bindiga Babaro tare da ceto mutum 76 da aka yi garkuwa da su. A wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida na Katsina, Nasir Mu'azu ya fitar, ya ce Babaro da yaransa ne suka kai hari a Gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina. Ya ce, "sojojin saman Najeriya ne suka kai harin ta sama a tsaunin Pauwa da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara, inda suka samu nasarar ceto mutum 76 ciki har da mata da…
