25
Aug
Daga ABDUL’AZIZ ABDUL’AZIZ Neman wani bayani ya kai ni shafin daukar ma'aikata na su Civil Defence da Immigration wanda aka rufe a satin nan. Kawai sai na ci karo da bayanan da suka fitar na masu neman aiki. Jaddawalin abu ne mai ɗaukar hankali ko ma tada hankali. Ya tuna min wata tattaunawa da muka yi kwanannan a shafin Prof Abdulrazak Ibrahim akan matsalolin yankin Arewa, musamman yadda muke barin jaki kullum ana dukan taiki. A cikin jihohi goma mafiya yawan masu neman aiki (applicants) jihohin tara na farko duk na Arewa ne; ta 10 ɗin ce kawai daga Kudu…
