23
Aug
Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi kira ga ’yan Najeriya da su tashi tsaye wajen yin rijista da karɓar Katin zaɓe na dindindin (PVC), domin tabbatar da rawar da ya dace su taka a dimokuraɗiyyar ƙasa. Shugaban jam’iyyar na Gombe, Malam Ɗanladi Yau, ya bayyana hakan ne bayan taron kwamitin zartarwa na jiha da aka gudanar a Gombe ranar Juma’a. Ya ce mallakar katin zaɓe ba kawai alhakin ɗan ƙasa ba ne, har ila yau shi ne babban makami da zai bai wa ’yan ƙasa damar canza makomar ƙasar. “Abin da ya kamata…
