23
Aug
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya ce lokaci ya ƙure wa tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi kan yunƙurinsa na neman takarar shugabancin Nijeriya. Wike wanda ya bayyana haka a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels Politics Today, ya ce ’yan Nijeriya ba za su zaɓi Amaechi a zaɓen 2027 ba. Amaechi wanda yake cikin haɗakar jam'iyyar ADC waɗanda ke yunƙurin ƙalubalantar shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani na kujerar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a 2022. Amaechi dai ya fice daga jam'iyyar APC zuwa…
