Kasuwanci

Kamfanin Google ya naɗa ɗan Nijeriya muƙamin Mananjan Darakta na Afirka 

Kamfanin Google ya naɗa ɗan Nijeriya muƙamin Mananjan Darakta na Afirka 

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Talatar da ta gabata ne dai kamfanin Google ya ba da sanarwar naɗin wani ɗan Nijeriya, Alex Okosi a matsayin Manajan Darakatan Google na Afirka domin taimaka wa kasuwanci da tattalin arziki su bunƙasa.  Mataimakin Shugaban EMEA na Google, Meir Brand shi ya hayyana hakan a wani jawabi. Sannan ya ce, a yanzu Mista Okosi shi ne zai ja ragamar ayyukan Google a Afirka. Mista Brand ya ƙara da cewa, wannan muƙami kuma zai taimaka wa biliyoyin masu amfani da shafin na Google su samu ƙarin abubuwa daga gare shi.   “Alex shugaba ne na…
Read More
Farashin mai ya kusa sakkowa a Nijeriya – Bincike

Farashin mai ya kusa sakkowa a Nijeriya – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI Akwai yiwuwar farashin man fetur a Nijeriya ya yi raga-raga in dai har farashin ɗanyen man fetur a duniya ya cigaba da faɗowa. A tarihi dai an riga an san cewa duk lokacin da farashin mai ya ɗaga a duniya, to farashin man fetur yana ƙaruwa a gidajen mai a Nijeriya ma. Alal misali ma wannan tsadar man fetur da ake fama da ita a Nijeriya ta afku ne sanadiyyar tashin farashin ɗanyen man fetur a duniya a karo na farko a watan Mayun shekarar 2023. Saboda haka, ake tunanin a halin yanzu da farashin ɗanyen…
Read More
Za mu kai ziyarar ba-zata ga bankunan da ake zargi da cinikin Dala ta haramtacciyar hanya – Gwamnnan CBN

Za mu kai ziyarar ba-zata ga bankunan da ake zargi da cinikin Dala ta haramtacciyar hanya – Gwamnnan CBN

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi barazanar gurfanar da bankunan da suke cinikayyar Dala ba bisa ƙa'ida ba. Wato ta haramtacciyar hanya. Sannan kuma a gurfanar da wannan banki da ya karya doka a gaban kuliya. Gwamnna riƙon ƙarya na CBN, Folashodun Shonubi, shi ya bayyana haka a wata lacca da aka gabatar a kan samar da mafita ga tattalin arzikin Nijeriya, wanda aka yi a Abuja. Taron ya mai da hankali a kan yadda za a katange shigar da kuɗaɗen gwamnati zuwa haramtacciyar hanya tare da shigar da su inda ya dace don kawo cigaban…
Read More
Kirifto Karansi: Tsakanin mutanen MTFE da ƙwararru

Kirifto Karansi: Tsakanin mutanen MTFE da ƙwararru

Daga ƊANLADI Z. HARUNA Kasuwanci, musamman na yanar gizo, yana tattare da kasada da ganganci da kuma tarangahuma. Wasu ma sun ce kasuwancin intanet tamkar cinikin biri a sama ne. Don haka masu bincike suke ɗora nazarinsu akan cewa kasuwancin intanet ya sha bambam da na zahiri. Domin shi a mafi yawan lokuta, daji ne da ba shi da ƙyaure. Kowacce irin harkar intanet na ɗauke da wasu alamu da a zahiri ana iya alaƙanta su da damfara ko rashin tabbas. Ta haka idan an samu matsala, ana shan wahala kafin a warware ta. Wannan kenan. Bayyanar MTFE, ya zo…
Read More
Hukumomin Kwastam, NCC, da ma’aikatu 61 na tarayya za su fara tattara haraji ƙarƙashin inuwa guda

Hukumomin Kwastam, NCC, da ma’aikatu 61 na tarayya za su fara tattara haraji ƙarƙashin inuwa guda

Daga AMINA YUSUF ALI 'Yan kwamitin shugaban ƙasa a kan haraji da gyara al'amurran tattalin arziki na Nijeriya sun bayyana cewa, daga yanzu hukumar Kwastam da sauran hukumomi da ma'aikatu guda 62 na gwamnatin Tarayya za su daina amsar haraji kai-tsaye. Shugaban kwamitin mai suna, Taiwo Oyedele, shi ya yi wannan jawabi a wata tattaunawarsa da gidan talabijin ɗin Channels Television a wani shiri da suka saba gudanarwa duk ranar Laraba. Ya ƙara da cewa, hukumar tattara haraji ta tarayya ita ce za ta cigaba da harajin dukkan waɗannan hukumomi da ma'aikatu. Oyedele, ya bayyana cewa, Nijeriya tana daga cikin…
Read More
Matsin tattalin arziki: Masu amfani da intanet a Nijeriya sun ragu ya zuwa miliyan 159.49 – NCC

Matsin tattalin arziki: Masu amfani da intanet a Nijeriya sun ragu ya zuwa miliyan 159.49 – NCC

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ( NCC), ta bayyana cewa, masu amfani da intanet a Nijeriya sun ragu i zuwa miliyan 159.49 daga watan Yunin 2023. Wata majiya ta bayyana cewa, kuma bisa dukkan alamu hakan yana da nasaba da matsin tattalin arzikin da ƙasar ta shiga a dalilin cire tallafin mai. A wani rahoto da hukumar ta NCC ta wallafa a shafinta na intanet, ta bayyana cewa, yanzu masu amfani da intanet ɗin sun ragu zuwa miliyan 159.49 wanda a baya suke adadin miliyan 159.59. Wato an samu raguwar masu amfani na kaso wajen 0.06 a…
Read More
Ƙarfafa ɓangaren kasuwanci ne mafita ga samar da aiki a Nijeriya – Malagi

Ƙarfafa ɓangaren kasuwanci ne mafita ga samar da aiki a Nijeriya – Malagi

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa ingantaccen fannin kasuwanci zai taimaka gaya wajen samar da guraben aiki a Nijeriya. Ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun ministocin Shugaba Bola Tinubu kuma mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja. Malagi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa don tantancewa a matsayin minista. Da yake jawabi, Malagi ya shawarci Hukumar Kula da Gidajen Talabijin da Rediyo ta Ƙasa (NBC) da ta bi diddigin lasisin gudanarwar da aka bai wa masu son kafa gidajen yaɗa labarai a faɗin ƙasa. Game…
Read More
Gwamnati za ta soke wasu manhajojin ba da rance saboda cuzguna wa ‘yan Nijeriya

Gwamnati za ta soke wasu manhajojin ba da rance saboda cuzguna wa ‘yan Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce za ta soke manhajojin ba da rance gida biyu saboda suna cuzguna wa 'yan Nijeriya. Gwanatin ta bayyana cewa, su dai waɗannan manhajoji da za ta dakatar da su manhajoji ne halastattu da aka yi wa rajista kuma sannan ta saki wani jerin sunayen haramtattun manhajojin ba da rance da suke aiki a ƙasar nan. Hukumar kare masu amfani da kaya/mai saye (FCCPC) ta bayyana haka a ranar alhamis ɗin da ta gabata. Inda suka ƙara da bayyana sunayen manhajojin rancen na yanar gizo waɗanda suka ƙi yin rajista a ƙarƙashin…
Read More
Ɗangote zai haɗe kamfanoninsa na gishiri, shinkafa da kuma na sukari a waje guda

Ɗangote zai haɗe kamfanoninsa na gishiri, shinkafa da kuma na sukari a waje guda

Daga AMINA YUSUF ALI NASCON kamfanin samar da gishiri a ƙarƙashin rukunin kamfanonin Ɗangote yana shawarar haɗewa tare da wasu kamfanonin abinci guda biyu daga cikin rukunin kamfanonin nasu. Wato kamfanin shinkafa da na sukarin Ɗangote. Za a tattauna a kan wannan al'amari a samar masa matsaya a taron kwamitin daraktocin kamfanonin da za a gudanar nan gaba a cikin wannnan watan. Wannan haɗaka da ake sa ran yi tana zuwa ne watanni 31 bayan babban kamfanin da yake hamayya da kamfanin Ɗangoten, BUA Group, ya ba da sanarwar yin wannann haɗaka ta haɗe kamfanoninsa na shinkafa, sukari, fulawa, man…
Read More
An ƙara kuɗin fetur a Nijeriya

An ƙara kuɗin fetur a Nijeriya

A halin da ake ciki, 'yan kasuwa sun cilla farashin fetur daga N537 zuwa N617 kan lita guda a wasu gidajen mai mallakar Kamfanin Fetur na Ƙasa (NNPCL). An ga wani gidan mai mallakar NNPC s ranar Talata a Abuja yana sayar da fetur N617 kan kowace lita. Ya zuwa haɗa wannan labari babu wani bayani a hukumance daga ɓangaren NNPC ko makamancin haka dangane da ƙarin kuɗin man. Tun bayan da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai baki ɗaya a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki a watan Mayu, farashin man ya cilla sama…
Read More