23
Oct
Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai ƙasar Nijeriya ta taka matsayi na 4 na ƙasashen da suka fi kowa cin bashi a jerin sunayen ƙasashe na IDA na Bankin Duniya (ƙasashe masu yin rance a bankin). A yanzu haka ana bin ƙasar bashin Dalar Amurka biliyan 14.3. Nijeriya ta daɗe a wannan matsayi nata na huɗu a jerin ƙasashe da ke ƙungiyar (IDA) masu rancen. Tun bayan da ta baro matsayi na 5 a Yunin shekarar 2022. Duk da Nijeriya ta kasance mai matsayi na 4, ta tara wa kanta bashin Dalar Amurka biliyan 1.3 a cikin shekara…
