12
Nov
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce duk takardun kuɗi (tsofaffi da sababbi) suna nan a kan doka. Wannan na zuwa ne sakamakon fargabar da ake ciki cewa tsofaffin takardun kuɗi za su daina aiki nan da watan Disamba 2023. Wata sanarwar da mai magana da yawun bankin CBN, Isah Abdulmunin ya fitar a ranar Laraba, ta ce bankin bai bayar da umarnin janye tsofaffin takardun kuɗi ba daga wajen al'umma. Bankin ya ce, “An kuma samu rahotannin damuwa da wasu jama’a ke nunawa kan halacci ko rashinsa na tsoffin takardun kuɗin Naira. “Don kauce wa shakku,…
