04
Dec
Daga AMINA YUSUF ALI Malam Badamasi Aliyu Abdullahi masani ne a kan dabarun tafiyar da sana'a da tattalin arziki. Ga wasu shawarwari da ya bayar a kan sana'a kamar haka: Son koyo da neman ilimi. Masu sana'a da ke da aƙida ta son cigaba suna son koyo ko sanin wani sabon abu da ya danganci harkar sana'arsu. Sun yarda cewa duniya kullum cigaba ake samu kuma cigaba a harkokin kasuwanci yana da kyakkyawar alaƙa da neman ilimi sana'a, fahimtar tattalin arziƙi, fahimtar ƙudurorin gwamnati, koyon amfani da sabbin dabaru, sabbin kayan aiki da sauransu. 2. Kallon ƙalubale a matsayin taki.…
