Kasuwanci

Darussan da ya kamata Nijeriya ta koya daga ƙasashen Vietnam da Malaysia – Adesina

Darussan da ya kamata Nijeriya ta koya daga ƙasashen Vietnam da Malaysia – Adesina

Daga AMINA YUSUF ALI Wani rahoto ya bayyana cewa, Vietnam ta samu nasarar fitar da miliyoyin mutanen ƙasar daga cikin qangin talauci a shekaru 30 da suka wuce ta hanyar fitar da kayayyakinta zuwa ƙasashen waje, inji Akinwumi Adesina, shugaban Bankin Cigaban Afirka. Kasuwancin ƙasar Vietnam ya kama Dalar Amurka biliyan 380 a shekarar 2020. Don haka a cewar sa, ya kamata Nijeriya ta yi koyi da ƙasashen Asiya. Domin Najeriya jimillar kasuwancinta na ƙasar waje ya kama Dala biliyan 33.5 a shekarar 2020. Wato kaso 10 cikin ɗari na Vietnam. Sannan su kuma Najeriya kasuwancinta ya dogara kacokan da…
Read More
Discos na shirin ƙarin farashin wutar lantarki

Discos na shirin ƙarin farashin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH Alamu masu ƙarfi na nuni da cewar akwai yiwuwar 'yan Nijeriya su fuskanci ƙarin kuɗin wutar lantarki nan ba da daɗewa ba. Hakan zai faru ne biyo bayan buƙatar da gamayyar kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) mai ƙunshe da kamfanoni 11 ta nuna kan ƙarin farashin lantarkin. Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ce ta bayyana haka a ranar Juma'a, 14 ga Yulin 2023. A cewar NERC, Gwamnatin Tarayya ta ce buƙatar sake duba farashin ta taso ne kan buƙatar haɗa sauye-sauye a ma’aunin tattalin arziki da sauran abubuwan da suka shafi ingancin sabis, ayyuka…
Read More
Ba za mu iya aiwatar da ƙarin kaso 40 na kuɗin lantarki ba – PHEDC

Ba za mu iya aiwatar da ƙarin kaso 40 na kuɗin lantarki ba – PHEDC

Daga AMINA YUSUF ALI  Kamfanin rarraba hasken lantarki na garin Fatakwal (PHEDC) ya bayyana cewa, sam ba zai iya ƙarin kuɗin lantarki zuwa kaso 40% ba a dai-dai wannna lokaci.   Kamfanin ya ƙara da cewa, a yanzu haka sun samu nasarar yi wa kaso 57 na masu amfani da wutar mitoci, amma fa a cewar su har yanzu guda 285,000 daga cikinsu ba su da mitoci.  Manajan Daraktan kuma babban jami'in zartarwar  PHEDC, Dakta Benson Uwheru, shi ya bayyana haka a garin Fatakwal a ranar Larabar da ta gabata a yayin taron 'yan jarida na ranar bikin cika shekara guda…
Read More
Bankun sun canza ƙa’idar cirar kuɗi a ATM zuwa Naira 200,000

Bankun sun canza ƙa’idar cirar kuɗi a ATM zuwa Naira 200,000

Daga AMINA YUSUF ALI Watanni da dama bayan da bankuna sun ƙayyade adadin kuɗin da za a iya cira a ATM a rana guda, yanzu sun ƙara adadin zuwa Naira 200,000. A yanzu haka za a iya cire har Naira 200,000 a kowacce rana a na'urar ATM ɗin daga asusun mutum guda.  A jiya ne dai Bankin Zenith ya sanar wa masu ajiyarsa ta hanyar saƙon imel cewa, yanzu za su iya cire kuɗi daga asusunsu har Naira Naira 200,000 a kwacce rana daga na'urar ATM ɗin bankin a faxin ƙasar nan, ba tare da la'akari da bankin da aka…
Read More
Bankin Nijeriya ya samar da ma’aikacin mutum-mutumi a bankin

Bankin Nijeriya ya samar da ma’aikacin mutum-mutumi a bankin

Daga AMINA YUSUF ALI  Bankin FirstBank na Nijeriya ya ƙaddamar da wani mutum-mutumin ma'aikacin banki a reshensa na  Adetokunbo Ademola VI, (DXC) a Legas don kula da koken masu ajiyar bankin.  Folake Ani-Mumuney, Shugaban rukunin bankuna, da kasuwanci da hulɗar kamfanoni na FirstBank, shi ya bayyana haka a cikin wani jawabi da gabatar a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata.  A cikin jawabin nasa ya bayyana cewa, mutum-mutumin yana da girkakkiyar kyamara ta bidiyo da fasahar na'ura mai ƙwaƙwalwa wanda zai mayar da shi tamkar ɗaya daga cikin ma'aikata masu fara'a na reshen bankin.  Wannan wani yunquri ne irinsa…
Read More
Mai yiwuwa tsadar kayayyaki a Nijeriya ya ƙaru da kashi 25 a ƙarshen 2023 – Bankin Duniya

Mai yiwuwa tsadar kayayyaki a Nijeriya ya ƙaru da kashi 25 a ƙarshen 2023 – Bankin Duniya

Daga BASHIR ISAH Bankin Duniya ya yi hasashen cewa bayan cire tallafin mai da aka yi a Nijeriya, mai yiwuwa hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya ƙaru da kashi 25 cikin 100 ya zuwa ƙarshen 2023. A cikin rahoton da ya haɗa game da ci gaban da Nijeriya ta samu na watan Yuni 2023, Bankin ya ce galibi hauhawar farashin zai shafi kayan abinci ne sakamon tsadar kuɗin mota da ake fuskanta tun bayan cire tallafin mai. Bankin ya ce yanzu hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya kai kashi 22.41 wanda hakan ya jefa Nijeriya cikin jerin ƙasashen da suka…
Read More
Batun farashin fetur zai ƙaru zuwa N700 ba gaskiya ba ne – IPMAN

Batun farashin fetur zai ƙaru zuwa N700 ba gaskiya ba ne – IPMAN

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Dillalan Fetur Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (IPMAN) da ta masu dakon mai, wato ADITOP a taƙaice, sun ƙaryata batun cewa akwai shirin cilla kuɗin fetur zuwa Naira 700 kan lita guda. Sun ƙaryata batun ne a wata zantawa da aka yi da su ranar Asabar a Abuja. Ƙungiyoyin sun ce babu ƙamshin gaskiya cikin rahotannin da aka yaɗa a kan batun ƙarin farashin man. A cewarsu, yanayin kasuwa ke tilasta ƙarin kuɗin fetur, kuma duba da yanayin kasuwar canji a halin yanzu babu buƙatar ƙarin farashin man sai dai hasashe kawai. Wasu 'yan kasuwa sun…
Read More
AEDC zai yi ƙarin kuɗin wutar lantarki a Yuli

AEDC zai yi ƙarin kuɗin wutar lantarki a Yuli

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya ba da sanarwar zai ƙara kuɗin wuta ya zuwa 1 ga watan Yulin 2023. Cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi da daddare, AEDC ya ce buƙatar ƙarin wutar ta taso ne duba da yadda darajar Naira ke hawa da sauka a kasuwar canji. Sanarwar ta ce: “A sani, daga ranar 1 ga Yuli, 2023, za a yi ƙarin farashin wutar lantarki sakamakon hawa da saukar da farashi ke yi a kasuwar canji. “Farashin canji a ƙarƙashin ƙa'idojin MYTO na 2022 da ya kasance N441/$1 a da, yanzu yana…
Read More
Bill Gates ya buƙaci Nijeriya ta inganta hannun jarin cigaban al’umma

Bill Gates ya buƙaci Nijeriya ta inganta hannun jarin cigaban al’umma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hamshaƙin attajirin duniya kuma Shugaban Gidauniyar Bill da Melinda Gates, Bill Gates, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta inganta saka hannun jari wajen samar da mafita mai kyau ga mutane ƙasar. Ya bayyana hakan ne a yayin taron samar da ƙirƙire-ƙirƙire na matasa na Pan-African a ranar Laraba a Legas, a wani ɓangare na ziyarar da ya kai Nijeriya. Taron yana da taken: "Ci gaban Afirka: Sake Ƙarfafa Matasa a Kimiyyar Ƙirƙirar Ƙirƙirar." Gates ta ce, Nijeriya na cike da haziƙan mutane da dama, amma ya yi nuni da cewa zai yi wuya a iya cika…
Read More
CBN ya cire takunkumi a asusun banki na Dala, ya mayar da shi $10,000 kullum

CBN ya cire takunkumi a asusun banki na Dala, ya mayar da shi $10,000 kullum

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya cire takunkumin da ya sa a asusun bankin Dala. Inda ya lara kuɗin da za a iya zubawa zuwa Dalar Amurka $10,000 a kullum. Wannan bayani yana ƙunshe a wani jawabi da aka wallafa bayan ganawa da kwamiitin ma'aikatan banki a ranar Lahadin da ta gabata. 18 ga Yuni, 2023. An shirya taron ne saboda niyyar samar da sababbin dokoki da za a ƙaddamar a harkar bankin. Sabuwar dokar ta soke iyakar da aka sanya a kan hada-hadar asusun banki na Dala a shekarar 2021. Don yin biyayya ga wani umarni…
Read More