26
Oct
Darakta Janar na Hukumar Bunƙasa Ilimi da Al’adu ta Duniya (UNESCO), Ms. Audrey Azoulay, ta ce a shekarar 2023, kashi 60% na al'ummar duniya mai jimlar mutane biliyan 4.75, sun rungumi amfani da shafukan sada zumunta wajen bayyana abubuwan da suka shafe su da neman amsoshin tambayoyi da sauran mu’amala. Ms. Audrey, wanda Darakta na Hukumar UNESCO ta Nijeriya, Mista Diallo Abdourahamane, ya wakilta, ta bayyana hakan a yayin bikin Ranar Amfani da Kafofin Yada Labarai da Yaɗa Bayanai ta bana, ranar Laraba, a Abuja. Ta yi bayani a kan alfanun hanyoyin sadarwa na zamani da kuma ƙalubalen da suke…
