13
Oct
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai kira taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya ba kwanaki 44 da kammala zaman majalisar da aka gudanar a ranar 28 ga watan Agusta. Hakan ya cigaba da haifar da ayar tambaya kan ko hakan na iya shafar harkokin mulki ko a'a? Majalisar Zartaswa ta Tarayya, wadda shugaban ƙasa ke jagoranta, ita ce Majalisar Zartarwa ta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya kuma wani ɓangare na zartarwa. Matsayin tsarin mulki na FEC, kamar yadda yake ƙunshe a cikin Dokar Ayyuka na Ministoci, ita ce ta zama ƙungiya mai ba da shawara ga shugaban ƙasa. A…
