29
Sep
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ma’aikatan da suka yi zanga-zanga sun kulle Ministan Ayyuka da Gidaje na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Mista Dave Umahi, a cikin ofishinsa da ke Abuja. An ce ministan ya hana ma’aikatan da suka zo aiki a makare samun damar shiga ma’aikatar. ’Yan ƙungiyar da suka hada da ma’aikatar gidaje da ayyuka sun yanke shawarar kulle ma’aikatar, tare da hana shiga da fita da kuma hana ministan fita daga ofishin. Sun kuma yi ikirarin cewa ya hana injiniyoyi da daraktoci yin aikinsu, kuma tun bayan naɗa shi ya ke karya ƙa’idojin aikin gwamnati, ta hanyar…
