22
Feb
Daga UMAR GARBA a Katsina Pantami ya buƙaci matasa da su mayar da hankali akan sana'ar fasahar ƙirƙira a madadin dogaro da takardar shaidar kammala karatu. Ministan Sadarwa na Nijeya, Isah Aliyu Pantami ya buƙaci gwamnati, matasa da sauran al'ummar ƙasar nan akan su mayar da hankali wajen koyon sana'ar ƙirƙire-ƙirƙiren fasahar zamani a madadin mayar da hankali a kan takardar shaidar kammala karatu don samun ayyukan dogaro da kai. Pantami ya bayyana haka ne a sakatariyar gwamnatin jihar Katsina a wajen wani taron bada kyaututtuka ga waɗanda suka yi nasara a gasar zaƙulo matasa masu baiwar ƙirƙirar fasahar zamani…
