Labarai

Remi Tinubu da matar Shettima sun je ta’aziyyar rasuwar Janar Lagbaja a Legas

Daga BELLO A. BABAJI Matar shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu ta je gaisuwar ta'aziyyar rasuwar shugaban sojojin ƙasa, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja. Matar mataimakin shugaban ƙasa, Hajiya Nana Shettima da ta mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA), Hajiya Ribaɗu. Matar Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Misis Oghogho Musa ita ta tarbe su. A lokacin da ta ke jajenta wa iyalan mamacin, Remi Tinubu ta yi kira gare su da su kasance masu haƙuri tare da kwaikwayon kyawawan halayen da ya bari. Ta nemi ƴaƴan marigayin da su tsayu wajen cimma kyawawan manufofinsu na rayuwa. Janar Lagbaja ya mutu…
Read More
Kamala Harris ta kira Donald Trump a waya domin taya shi murna

Kamala Harris ta kira Donald Trump a waya domin taya shi murna

Yar takarar shugabancin ƙasar Amurka a jam’iyyar Democrat kuma mataimakiyar shugaban ƙasa, Kamala Harris, ta kira zaɓaɓben shugaban ƙasa Donald Trump, inda ta amince da shan kaye. Harris ta taya Trump murna kan nasarar da ya samu a zaɓen 2024, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS News ta bayyana. A cikin kiran, Harris ta jaddada muhimmancin miƙa mulki cikin lumana da shugabanci na kowa da kowa a Amurka. An bayyana cewa za ta yi jawabi ga magoya bayanta a jami'ar Howard nan gaba. A nasa ɓangaren, Trump ya gode wa magoya bayansa tare da yabawa ƙoƙarin da suka yi.…
Read More
Kwamishinan ‘yan sandan Katsina ya umarci jami’ansa su himmatu wajen inganta tsaro

Kwamishinan ‘yan sandan Katsina ya umarci jami’ansa su himmatu wajen inganta tsaro

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan 'yan sanda a Jihar Katsina CP Aliyu Abubakar Musa yayi wani taron gaggawa da manyan jami'an 'yan sanda na hedkwata da na ƙananan hukumomin domin duba yadda suke gudanar da harkokin tsaro a jihar. Ya bayyana cewa taron ya zama dole ganin yadda a ke samun yawaitar ƙaruwar satar wayoyin wutan lantarki a faɗin jihar da yace haka na faruwa ne sakamakon ƙarancin wutan lantarki. Kwamishinan yayi gargaɗin cewa rundunar 'yan sanda ba zata zuba ido ta ga wasu ɓata gari na yin zagon ƙasa da lalata kayan hukumar wutan lantarki a jihar ba.…
Read More

Jamus ta buƙaci Isra’ila ta bari a kai kayan tallafi Arewacin Gaza

Daga BELLO A. BABAJI Ƙasar Jamus dake Nahiyar Turai ta yi kira ga Isara'ila da ta bari a kai ƙarin kayan agaji na jinƙai zuwa Arewacin Gaza a ƙasar Palestine. Kakakin Ma'aikatar waje ta Jamus ya bayyana hakan a inda ya ce, "Mu na kiran gaggawa ga Gwamnatin Isra'ila ta yi abin da yake wajibi ne a kanta ƙarƙashin dokar ƙasa-da-ƙasa." Jakadan Palestine a Nijeriya, Abdallah Abu Shawesh ya ce watanni 13 kenan da ake cigaba da buɗe wuta da tarwatsa garuruwa da hana a kai kayan tallafi ga Falasɗinawa. Ya ce, su na kira ga Jamus da ta daina…
Read More

Gwamnan Zamfara ya dakatar da cire kuɗaɗe ba bisa doka ba a albashin ma’aikata a jihar

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya umarci a gaggauta dakatar da duk wasu rage-rage da ake yi wa albashin ma'aikata ba bisa ƙa'ida ba a jihar. Hakan na zuwa ne bayan da ma'aikata suka yi ta gabatar da ƙorafe-ƙorafe game da rage-rage da ake samu daga ofishin biyan albashi na jihar. Cikin wata takarda da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, Dauda Lawal ya ce ya ɗauki matakin ne don tabbatar da inganci ga ɓangaren kula da albashin ma'aikatan sakamakon haramtattun hanyoyi da ake bi wajen zaftare musu kuɗaɗe. Gwamnan ya kuma umarci kwamishinan kuɗi da…
Read More
Tinubu ya ɗage taron majalisar zartarwa saboda rasuwar Lagbaja

Tinubu ya ɗage taron majalisar zartarwa saboda rasuwar Lagbaja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci ɗage taron majalisar zartarwa ta tarayya zuwa wata ranar da za a sanar nan gaba. Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba. Ya ce, “An ɗage taron majalisar ne da aka shirya yi yau domin girmama Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban hafsan sojojin ƙasa wanda ya rasu a daren Talata.” Janar Lagbaja ya yi aiki a matsayin babban hafsan sojojin ƙasa tun ranar 19 ga watan Yuni, 2023, har zuwa rasuwarsa a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024. Shugaba Tinubu…
Read More

Gwamnan Kaduna ya yaba wa Shugaba Tinubu kan sakin yara masu zanga-zanga

Daga IBRAHIM IMAM IKARA A ranar Talata ne Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya marabci yaran jihar daga Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima bayan umarnin Shugaba Tinubu kan a gaggauta sakin su ba tare da sharaɗi ba. Malam Uba Sani ya bayyana a shafinsa na kafafen sada zumunta cewa mataimakin shugaban ƙasa ne ya ba shi yaran bayan janye tuhumar da ake yi musu na cin amanar ƙasa a zanga-zangar watan Agusta, 2024. Yaran sun bayyana wa gwamnan cewa, wasu ne suka yi amfani da su wurin haifar da gagarumin tashin hankali a Kaduna ma Nijeriya, sakamakon haka ne gwamnatin…
Read More
Tinubu ya sanar da rasuwar hafsan sojojin Nijeriya, Lagbaja, a hukumance

Tinubu ya sanar da rasuwar hafsan sojojin Nijeriya, Lagbaja, a hukumance

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban hafsan sojojin Ƙasa, wanda ya rasu yana da shekara 56. Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa Lagbaja ya rasu ne da daren Talata a birnin Legas, bayan fama da rashin lafiya. An haifi Lagbaja a ranar 28 ga watan Fabrairu, 1968. Shugaba Tinubu ne ya naɗa shi a matsayin babban Hlhafsan Slsojojin Ƙasa a ranar 19 ga watan Yuni, 2023. "Ya fara aikin soji ne tun bayan shiga makarantar horas da sojoji ta NDA a shekarar…
Read More
Tirela ta halaka mutum biyu da jakuna 40 a Jigawa

Tirela ta halaka mutum biyu da jakuna 40 a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Wata tirela ta kife a jiya ranar kasuwar Shuwarin a daidai lokacin da kasuwar take tsakiyar ci, ta halaka mutane biyu ta kuma murƙushe jakuna 40. Motar mai lamba kamar haka NGU 498XA ta ƙwace a hannun direban a lokacin da yake ƙoƙarin yin wani hawa kusa da gadar Sama dake daf da kasuwar ta Shuwarin, amma direban ya kasa sarrafata ta faɗi a ƙasa wanwar. Tirelar tana ɗauke da jakuna kamar 100 da dawaki wadda ta taso daga Fataskum zuwa Enugu, wanda wani mai suna Muhd Hassan ya ke tuƙawa ta ƙwace aka…
Read More

Kotu ta dakatar da CBN daga rufe asusun kuɗaɗen ƙananan hukumomi a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Babbar Kotun Kano ta bada umarnin dakatar da babban bankin Nijeriya (CBN), da Antoni-Janar na Ƙasa (AGF) da Hukumar Kasafin Kuɗin Haraji (RMAFC) daga riƙe kuɗin wata-wata na ƙananan hukumomi 44 dake faɗin jihar. Hakan na zuwa ne bayan da Shugaban Ƙungiyar Ma'aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE), Ibrahim Muhammed da wasu ƴan jihar guda biyar da suka haɗa da; Ibrahim Shehu, Ibrahim Abubakar, Usman Isa, Sarki Kurawa da Malam Usman Imam suka shigar da ƙarar a ranar 1 ga watan Nuwamba. Waɗanda suka shigar da ƙarar sun koka ne game da cewa akwai yiwuwar ake…
Read More