Labarai

NNPCL ya ayyana dokar ta-ɓaci a harkokin man fetur na Nijeriya – Kyari

NNPCL ya ayyana dokar ta-ɓaci a harkokin man fetur na Nijeriya – Kyari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kamfanin man fetur na gwamnatin Nijeriya NNPCL ya ce ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin haƙowa da kuma fitar da ɗanyen mai daga ƙasar. Shugaban kamfanin, Mele Kyari, ya ce sun ɗauki matakin ne da zimmar haɓaka yawan man da ake haƙowa, yana mai cewa bincikensu ya nuna "Nijeriya za ta iya haƙo fiye da ganga miliyan biyu duk rana". "Mun ayyana yaƙi ne a kan ƙalubalen da muke fuskanta a harkokin haƙo fetur. Mun shaida wa abokan hulɗarmu, muna da kayan aikin aiwatar da hakan kuma mun san abin da za mu yi,"…
Read More
 Masu yi wa Tinubu zangon-ƙasa ba su da kishin Nijeriya — Matawalle

 Masu yi wa Tinubu zangon-ƙasa ba su da kishin Nijeriya — Matawalle

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana wadanda ke shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a 2027 a matsayin ’yan siyasa marasa kishin ƙasa. Ya kuma kara da cewa babu wani taron-dangi da zai hana shugaban ƙasa tsayawa takara da kuma lashe zaɓen 2027. Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan yunƙurin da wasu ‘yan siyasar Arewa ke yi na kushe gwamnatin Tinubu, inda su ke bada misali da salon mulkinsa. Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike ya fitar,…
Read More
Wasu manoma a Ɗanja sun nemi gwamnatin Jihar Katsina ta biya su diyyar gonakinsu

Wasu manoma a Ɗanja sun nemi gwamnatin Jihar Katsina ta biya su diyyar gonakinsu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wasu manoma a Ƙaramar Hukumar Ɗanja sun nemi gwamnatin Jiihar Katsina da ta biya su diyyar gonakinsu da ta karɓa tsawon shekara biyar. Mai magana da yawun manoman, Shugaba Ɗan'azumi ya faɗi haka a lokacin da yake miƙa takardar koke ga wakilin Sarkin Kudun Katsina hakimin Ɗanja.                                          Manoman da wakilin hakimin Sarkin Fulani Ɗanja Alhaji Yazid Sadiƙ, wakilin manoman ya ce Naira miliyan goma ne adadin kuɗin da gwamnati za ta basu amma har yanzu…
Read More

Majalisar dokokin Ribas ɓangaren Fubara za su ƙalubalanci hukuncin kotu kan nasarar Amaewhule

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wani ɓangare na majalisar dokokin jihar Ribas ƙarƙashin jagoranci Vickto Oko-Jumbo ya ce ba su amince da hukuncin kotun ɗaukaka kara ba biyo bayan sanar da Martins Amaewhule a matsayin halstaccen kakakin majalisar. Oko-Jumbo wanda shi ɗan bangaren gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ne ya faɗi hakan a yayin wani zaman majalisar a Fatakwal, babban birnin jihar. A ranar Alhamis ne kotun ta yi watsi da hukuncin babbar kotun jihar wacce ta sanar cewa Amaewhule da wasu ƴan majalisu 24 ba sa cikin mambobin majalisar dokokin jihar. Kotun ɗaukaka ƙarar, ta ce babbar kotun jihar ba ta…
Read More
Tinubu ya yi kuskure wajen aiwatar da cire tallafin fetur, inji Moghalu

Tinubu ya yi kuskure wajen aiwatar da cire tallafin fetur, inji Moghalu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Farfesa Kingsley Moghalu, ya ce cire tallafin man fetur da rage darajar Naira da Shugaba Bola Tinubu ya yi, manufofin suka ƙara tagayyara Nijeriya. Farfesan a fannin tattalin arziki ya ce duka tallafin man fetur da kuma canja fasalin naira da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnan CBN, Godwin Emefiele suka yi ba ita ce manufa mafi dacewa ga ƙasar nan ba. Moghalu ya ce abin da ya dame shi su ne cire tallafin man fetur da kuma hauhawar Dalar Amurka akna naira. Kuma Shugaba Tinubu ya…
Read More
Farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi a Kaduna, Kano da Katsina

Farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi a Kaduna, Kano da Katsina

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Dangane da yanayin da duniya ke ciki, NIjeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyakin abinci da ba a tava yin irinsa ba. Binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya fitar a jihohin Kaduna, Kano da Katsina ya nuna cewa ba bar Nijeriya a baya ba. Misali, wani bincike da NAN ta gudanar a Kaduna ya nuna cewa an samu qaruwar farashin shinkafa, biredi, sikari, garri, naman sa da kwai da dai sauran su, waxanda su ne ginshiqin abinci a gidaje. Haka nan, hauhawar farashin ya yi tasiri a rayuwar yawancin gidaje, domin kuwa yanzu suna fuskantar…
Read More
Dalilinmu na kai farmaki ga kadarorin masu ta’ammali da ƙwayoyi – Marwa

Dalilinmu na kai farmaki ga kadarorin masu ta’ammali da ƙwayoyi – Marwa

Daga MAHD M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, Mohamed Buba Marwa ya bayar da hujjar matakin da hukumar ta ɗauka na bin kadin kadarorin ɓarayin shanu da masu safarar miyagun ƙwayoyi a cigaba da ɗaukar matakin da ya dace na yaƙi da miyagun ƙwayoyi. Marwa ya bayyana dalilin da ya sa hukumar ta sake yin sabon yunƙuri a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Laraba 19 ga watan Yuni 2024 don fara gudanar da ayyuka na tsawon mako guda don murnar zagayowar ranar yaƙi da muggan ƙwayoyi da safarar miyagun ƙwayoyi…
Read More
Gyaran tsarin mulki: Majalisar dokoki ta ’yantar da ƙananan hukumomi daga gwamnoni

Gyaran tsarin mulki: Majalisar dokoki ta ’yantar da ƙananan hukumomi daga gwamnoni

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar Dokokin Nijeriya a ranar Talatar da ta gabata ta bayar da cikakken ’yancin cin gashin kan harkokin kuɗi da na mulki ga ɗaukacin ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin Nijeriya ta hanyar yi wa sashe na 124 na Kundin Tsarin Mulkin ƙasar kwaskwarima. Sashen ya tanadi samar wa ƙananan hukumomi cikakken 'yanci ba tare da tsangwama daga gwamnatocin jihohi ba. Gyaran dokar dai na ɗaya daga cikin wasu 22 da majalisar wakilai ta amince da ita a makon jiya kuma majalisar ta amince da ita a ranar Talata. Ɓangarorin biyu sun ta hanyar kwamitin taro…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Ronaldo da Pepe sun yi adabo da gasar Turai bayan doke Portugal da Faransa ta yi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayinda shahararren ɗan ƙwallon ƙafan duniya Christiano Ronaldo da takwaransa na ƙasar Portugal, Pepe ke shirin bankwana da buga wasa, ƴan wasan sun yi rashin nasara a hannun Faransa a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a gasar kofin Nahiyar Turai na 2024. Portugal ta sha kaye ne a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida bayan shafe mintuna 120 ba a samu wanda ya zura ƙwallo ba, inda daga baya Faransa ta doke ta da ci 5 da 3. Wannan ita ce gasar kofin ƙasashe ta ƙarshe da ƴan wasan biyu su ka sha alwashin ajiye aikinsu da…
Read More
Babban ɗan Kwame Nkrumah ya rasu 

Babban ɗan Kwame Nkrumah ya rasu 

Dakta Francis Nkrumah, babban ɗan shugaban Ghana na farko, Osagyefo Dr. Kwame Nkrumah, ya rasu, yana da shekaru 89 a duniya. Mawallafin Indiya kuma editan Ɓijay Prashad ne ya tabbatar da mutuwarsa, wanda ya ba da labarin ta kafafen sada zumunta ranar Lahadi, 30 ga Yuni, 2023. “Dakta Francis Nkrumah (1935-2024) ya rasu, wanda ya kasance babban ɗan Kwame Nkrumah. Ya yi rayuwarsa a matsayin likitan yara, wanda majinyatansa ke matuƙar ƙaunarsa. Dakta Nkrumah ya ci gaba da zama a Ghana bayan juyin mulkin da aka yi wa mahaifinsa, kuma ya ci gaba da aiki a matsayin likita, kuma masanin…
Read More