Labarai

Makamai da ƙwayar biliyan N13.9 muka kama a Ribas – Kwastom

Makamai da ƙwayar biliyan N13.9 muka kama a Ribas – Kwastom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Hukumar Kwastom ta Nijeriya, Bashir Adeniyi Adewali ya ce kimar makamai da miyagun ƙwayoyi da suka kama a rana guda a Jihar Ribas ya kai Naira biliyan 13.9. Bashir Adewali ya bayyana cewa makaman biliyan N4.171 suka kama a Tashar Jiragen Ruwa ta Onne da ke Jihar Ribas a ranar Litinin. Makaman a cewarsa sun haɗa da bibdigo guda 844 da kuma harsasai masu rai guda 12,500, waɗanda aka ɓoye suba cikin kayan daki da aka shigo da su daga ƙasar Turkiyya. A tashar jiragen ruwan ne kuma jami’an hukumar kwastom suka kama…
Read More
JAMB ta bankaɗo ɗalibai 3,000 da suka kammala karatun jami’a na bogi

JAMB ta bankaɗo ɗalibai 3,000 da suka kammala karatun jami’a na bogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta ƙasa (JAMB) a Nijeriya ta bankaɗo daliban da suka kammala karatun jamia na bogi 3,000 da kuma mallakar takardun shaidar kammala karatu ba bisa ƙaida ba a duk faɗin ƙasar. Magatakardar hukumar, Farfesa Ishaƙ Oloyede ne ya bayyana hakan kuma ya ce waɗannan mutane ba su taɓa zuwa jami’a ba, wanda hakan ya nuna irin cin hanci da rashawa da ake samu a harkar ilimi. Oloyede ya soki yadda wasu cibiyoyin karatu suke shigar da ɗalibai makarantu ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa abin…
Read More
Gwamnatin Kano ba ta hana ’yan kasuwar IBB sana’arsu ba – Hon. Wise

Gwamnatin Kano ba ta hana ’yan kasuwar IBB sana’arsu ba – Hon. Wise

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana Gwamnan Jihar Kan, .Alhaji Abba Kabir Yusuf da cewa mutum ne mai tausayi da imani duk lokacin da aka ce wata matsala ta shafi al;umma ba wai ;yan kasuwar kaɗai ba  zai zauna ya samu sukuni ba sai ya tabbatar ya warware matsalar. Hon. Alhaji Isa Wise, Babban Mataimaki na biyu ga Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf kan harkokin kasuwanci ne ya shaida hakan ga yan jarida. Ya ce dalilin da ya sa aka cire teburan yan kasuwar a kewayen filin Idi shine don samar da sarari lokacin sallar idi domin…
Read More
Ana cece-kuce kan rufta Nijeriya yarjejeniyar auren jinsi

Ana cece-kuce kan rufta Nijeriya yarjejeniyar auren jinsi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu malamai sun koka akan Gwamnatin Tarayya, domin sanya hannu akan yarjejeniyar nan mai cece-kuce ta Samoa, wacce ake zargin ta na ƙunshe da amincewa da tsarin auren jinsi. A cewarsu, yarjejeniyar tana ɗauke da wasu sharaɗai da suka ƙunshi cewa ƙasashe masu tasowa dole su yarda da ’yancin ’yan luwadi da ’yan maɗigo da kuma ’yancin yin auren jinsi ɗaya. Yarjejeniyar an samar da ita a tsibirin Samoa, inda aka sanya ma ta hannu a ranar 15 ga Nuwamba, 2023, amma tun lokacin yarjejeniyar ke samun suka daga addinai da dama, saboda hakan…
Read More
Binciken Ganduje: Kotu ta ba shugabannin kwamiti kwana biyu su sauka

Binciken Ganduje: Kotu ta ba shugabannin kwamiti kwana biyu su sauka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta umarci alƙalan babbar kotun  jihar, Mai Shari’a Faruk Lawal Adamu da Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, wa’adin awa 48 su sauka daga shugabancin kwamitocin binciken da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa domin bincikar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje. Alƙalan biyu ne ke jagorantar kwamitoci biyu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa don bincikar Gwamnatin Ganduje kan zargin karkatar da kuɗaɗe da kadarorin gwamnati da kuma kwamitin bincike kan rikicin siyasa da ɓacewar mutane daga 2015 zuwa 2023. Mai Shari’a Simon Amobeda, ya umarci Hukumar Kula da…
Read More
Majalisa na aiki don tabbatar da ’yancin ƙananan hukumomi da masarautu – Abbas

Majalisa na aiki don tabbatar da ’yancin ƙananan hukumomi da masarautu – Abbas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya ce, Majalisa ta 10 a ƙarƙashin jagorancinsa ta ɗauki matakai da nufin tabbatar da ayyukan da tsarin mulki ya amince da su ga masarautun gargajiya da kuma cin gashin kan ƙananan hukumomi a Nijeriya. Shugaban Majalisar, wanda ya bayyana hakan a wajen bikin kwana biyu na ‘taron mako’ da ake yi na murnar cika shekaru 10 da kafuwar Majalisar ta 10, ya ce, a cigaba da manufofin majalisar na kafa wasu kwamitoci na musamman guda biyu da za su tafiyar da aikin na aiwatar da ’yancin…
Read More
Dole masu POS su yi rijista kafin ƙarewar wa’adi – Hukumar CAC

Dole masu POS su yi rijista kafin ƙarewar wa’adi – Hukumar CAC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gabanin cikar wa’adin yin rajistar kasuwanci na dole tare da Hukumar Kula da Kamfanoni ta Nijeriya, CAC, Jakadan Hukumar, Michael Nwabufo, ya buƙaci masu sana'ar POS da masu ƙananan sana’o’i su gaggauta yin rajista da hukumar. Nwabufo, manajan tallar hukumar, ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar kwanan nan a Legas cewa dole ne masu POS su guje wa rikice-rikice ta hanyar tabbatar da rajistar su kafin wa'adin. Da yake ƙarin haske kan mihimmancin wa'adin, wanda ya rage saura kwanaki biyar, Nwabufo ya ƙarfafa 'yan kasuwa da su yi amfani da manhajar CAC Special…
Read More

EFCC ta tsaurara tsaro a Abuja, Legas da Ibadan bisa shirin yi wa hukumar zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), ta ɗauki matakin tsaurara tsaro a ofisoshinta da ke Abuja, Lagas da Ibadan, babban birnin jihar Oyo, biyo bayan raɗe-raɗin cewa an shirya za a yi mata zanga-zanga a ranar juma'a 5 ga watan Yuli. Jaridar 'The Nation' ta ruwaito cewa, a jihar Legas, an sanya wasu jami'an hukumar tare da 'Yan sandan farin kaya na DSS a dukkan hanyoyin da za su kai zuwa ofishinta da ke hanyar Awolowo a ƙaramar hukumar Ikoyi. Haka nan a jihar Oyo, wani mai suna Steve ya sanya a shafinsa…
Read More

Sarki Sanusi ya yaba wa Gwamnan Kano bisa bai wa ‘yan fansho da ilimin yara mata muhimmanci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya jinjina wa gwamna Abba Kabir Yusuf kan warware matsalolin biyan ƙuɗaden fansho da kuma bada muhimmanci ga ilimin yara mata. Sanusi ya yi hakan ne la'akari da yadda mutane da dama suka shiga matsanancin rayuwa da talauci wanda rashin biyan su kuɗaɗensu na fansho da giratuti ya zama dalilin samun kansu a wannan hali. A kwanakin baya ne, gwamnan ya sa a ka ware Naira biliyan 11 domin biyan waɗanda ke karɓar kuɗin fansho ciki har da waɗanda aka riƙe mu su na tsawon lokaci, inda Sarkin ya yaba…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta dakatar jirage masu zaman kansu 10

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da harkokin jirage masu zaman kansu (NCAA), ta dakatar da zirga-zirga da ayyukan wasu jirage guda 10 biyo bayan da su ka gaza sabonta tantancewarsu daga gare ta. Wata sanarwa da NCAA ta saka a shafinta na 'Twitter' wanda ke ɗauke da sa hannun daraktanta kan hulɗa da jama'a da kula da abokan hulɗa, Micheal Achimugu, ta ce ta bayar da umarni ga waɗanda ke mallakan jirage domin amfanin kansu da su sake zuwa a tantance su wanda wa'adin hakan ya kamata a ce ya ƙare tun ranar 19 ga watan Afrilu, 2024. Achimugu…
Read More