Labarai

An yi garkuwa da wakilan jaridun Blueprint da The Nation a Kaduna

An yi garkuwa da wakilan jaridun Blueprint da The Nation a Kaduna

A jiya ne muka samu rahoton garkuwa da wakilan Jaridar Blueprint da The Nation tare da iyalansu a gidajen su dake Danhono cikin garin kaduna. Ƙungiyar yan Jaridu ta ƙasa ita ta fitar da wannan sanarwa da sa hannun shugaban ta. Sun bayyana wannan hari a matsayin rashin imani tsantsa. Abdulraheem Aodu shine wakilin Jaridar Blueprint, yayin da Abdulgaffar Alabelewe shine wakilin The Nation. Sai dai masu garkuwar sun sako matar wakilin Blueprint saboda ba ta da lafiya sosai. Ƙungiyar ƴan jaridun reshen kaduna sun yi kira da gwamnati da jami'an tsaro da su hanzarta wanjen ganin an kuɓutar da…
Read More
‘Yan siyasar Arewa sun zama ‘yan amshin-Shata a gwamnatin Tinubu – Lukman

‘Yan siyasar Arewa sun zama ‘yan amshin-Shata a gwamnatin Tinubu – Lukman

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman, ya ragargaji ‘yan siyasar Arewa da ke cikin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, cewa an sun yi sototo, su na kallo an maida su ‘yan-amshin-Shata. Lukman wanda kwanan nan ya fice daga APC, ya ce, “an maida ‘yan siyasar Arewa “an-amshin-Shata a gwamnatin Tinubu, waɗanda hatta shi kan sa amshin ba su iya ba. Ga shi kuma su na sane da cewa wanda suke wa amshi shi ma bai san makamar aikin sa ba.” Ya ce ‘yan Arewa sun samu cikakkiyar damar…
Read More
Zargin auren jinsi: Gwamnatin Tarayya ta shigar da Jaridar Daily Trust ƙara kotu

Zargin auren jinsi: Gwamnatin Tarayya ta shigar da Jaridar Daily Trust ƙara kotu

Gwamnatin tarayya ta sanar cewa a shirye take tsab, domin shigar da Jaridar Daily Trust ƙara saboda rahoton da tayi akan Yarjejeniyar SamoaYarjejeniyar ta buƙaci kasashe dole su kula, da kuma bada kariya ga yan daudu, masu auren jinsi kafin a bada bashin. Sai dai jaridar daily trust ta rawaito cewa malamai da kuma kungiyoyin sa kai sun yi Allah wadai da wannan al'amari. Ministan yaɗa labarai ya fito ya maida martani, inda yace Najeriya ta saka hannu ne ga Yarjejeniyar bayan yin watsi da duk wani sashe da yaci karo da al'adu da kuma dokokin Nijeriya. Ya ƙara da…
Read More
COAS ya raba kayan sawa da takalma ga yara marasa galihu 400 a Zamfara

COAS ya raba kayan sawa da takalma ga yara marasa galihu 400 a Zamfara

Daga Sanusi Muhammad, Gusau A ci gaba da kokarin inganta hadin gwiwar rundunar sojoji da farar hula, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar TA Lagbaja, ya raba wa yara marasa galihu 400 tufafi da takalma a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Kwamanda rundunar ta daya, 1 brigade Gusau, Brig. Janar S. Ahmed wanda ya wakilci babban hafsan soji a lokacin rabon kayan da aka gudanar a asibitin kwararru na Yariman Bakura dake Gusau ya ce, taron wani bangare ne na bikin ranar sojoji ta shekar 2024, yayinda sojojin Najeriya ke gudanar da ayyukan gaggawa ga al'ummomin da ke zaune a…
Read More
Layin mai ya dawo Abuja, yayin da ake sayar da litar mai N850

Layin mai ya dawo Abuja, yayin da ake sayar da litar mai N850

Dogon layi a gidajen mai ya fara dawowa a babban birnin tarayya Abuja, Niger da wasu sassa na Jihar Niger. Hakan na faruwa ne bayan gidajen mai da dama sun rufe gidajen man su. Wannan dawowar layin mai, ya sanya tsoro cikin mutane , masu abun hawa da fasinjoji. Wannan yayi sanadiyar ana sayar da mai nera 850 a kan duk lita ɗaya a wasu gidajen man. Masu bunburutu anga sun dawo bisa hanya, wannan alama ce da ke nuna man ya fara wahala. A bunburutu aƙalla lita na kai wa har nera 1000. Mutane da dama na kokawa kan…
Read More

An yi auren tsohuwar jarumar Kannywood, Sadiya Gyale

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar juma'a, 5 ga Yuli, 2024 ne aka ɗaura auren tsohuwar tauraruwar Kannywood, Sadiya Gyale da angonta mai suna Mustafa Umar Kawu bayan sallar juma'a, a masallacin sharaɗa 'Phase 3' da ke jihar Kano. Sadiya Muhammad, wacce aka fi sani da Sadiya Gyale, ta kasance ɗaya daga cikin taurarin da ke da basira wajen yin shiri mai kyau a kowane ɓangare aka saka ta a fim. Tauraruwar ta yi baya da harkar fim ne bayan da aka yi aurenta na farko a shekarar 2015 da wani Barista Abubakar da ke aiki a jihar Kaduna. Sai…
Read More

An mayar da wutar lantarkin Jami’ar Ɗangote bayan katse ta da KEDCO ya yi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kamfanin raba wutar lantarki na jihar Kano, KEDCO ta sake haɗa wa Jami'ar kimiyya da fasaha ta Ɗangote da ke Wudil wutar lantarkinta bayan da aka biya Naira miliyan 100. Mataimakin Shugaban makarantar (VC), Farfesa Musa Yakasai ya tabbatar da haka a wata hira ta waya da gidan 'News Agency Nigeria' a ranar juma'a inda ya ce KEDCO ta mayar da wutar ne da misalin ƙarfe 4 na yamma bayan da aka biya kuɗin. KEDCO ta katse wutar ne bayan ikirarin cewa akwai bashin Naira miliyan 248 a kan jami'ar. Sannan, a watan, duk da an…
Read More
Masoud Pezeshkian ya lashe zaɓen ƙasar Iran

Masoud Pezeshkian ya lashe zaɓen ƙasar Iran

Masoud Pezeshkian ne yayi nasarar lashe zaɓen da aka gudanar a ƙasar Iran. Masoud ya sami wannan nasarar ne bayan doke abokin hamayyar sa Saeed Jalili. An ayyana Masoud a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun kaso 53.3% na kuri'un da aka kaɗa. Abokin hamayyar shi, ya samu kaso 44.3.Wannan zaɓen shine zagaye na biyu bayan da ba a samu yawan adadin da ake bukata ba na cin zaɓen. Wannan zaɓen an yi shi ne, bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar a wani haɗarin jirgi a watan Mayu. Shugabannin ƙasashe irinsu Rasha, China da Indiya sun taya sabon shugaban murna.
Read More

Buɗaɗɗiyar wasiƙa kan halifofin sharholiya

Daga NASIR ABDULLAHI GAYAWA Zuwa ga Dakta Lawi Abubakar AtikuUnguwar Sanka, Kano1 ga Yuli, 2024 Assalamu Alaikum, Wataƙila Maulana ya yi mamakin samun wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa. Sunana Nasir Abdullahi Gayawa, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Jihar Kano; ɗalibi mai neman digiri na biyu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Houari Boumedeine, Bab Zouer, a Algiers, Algeria. Na ziyarce ku a birnin Algiers, lokacin bikin tunawa da Shaykh Abdulkarim Al-Maghili, a Disamban 2022 inda muka tattauna abubuwa da dama ciki har da matsalolin da ƴan uwa ke takaicin afkuwar su a ɗariƙarmu ta Tijjaniyya. Kasa samun ku a waya da rashin…
Read More
Gamsuwa da gwamnatin Abba ya sa ƙasashaen labarawa suka bai wa al’ummar Kano tallafin ilimi – Sheikh Tijjani Auwalu

Gamsuwa da gwamnatin Abba ya sa ƙasashaen labarawa suka bai wa al’ummar Kano tallafin ilimi – Sheikh Tijjani Auwalu

Daga MUHAMMADU MAJITTABA a Kano Kwamishinan Al'amuran Addini na Jihar Kano Hon. Tijjani Sani Auwalu ya bayyana cewa gamsuwa da yadda gwamnatin Kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf ne musabbabi kuma dalilin da ya sa wasu ƙasashan Musulmi Larabawa kamar irin su Misra, Kuwait, Maroko, Turkiyya, Saudiyya da sauransu, suka yarda su zo, su bai wa gwamnatin Kano tallafin bunƙasa ilimi domin amfanin al'ummar Kano a wannan lokacin. Bayanin hakan ya fito ne daga baki Sheikh Tijjani Sani Auwalu a lokacin hira da manema labarai a birnin Kano, inda ya ce yanzu haka akwai wata gidauniyya da ake kira Alfijir…
Read More