Labarai

Ahmad Musa ya yi tsokaci kan ajiye aiki da Super Eagles

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa ya warware batun cewa ya yi murabus daga buga wa ƙungiyar wasan. Musa bai buga wasa ko ɗaya ba ciki wasannin 7 da Super Eagles ta yi a gasar kofin Nahiyar Afirka da aka buga na wannan shekarar inda ta ƙare a ta biyu. Ahmed Musa, wanda tsohon ɗan wasan gaba na Leicester City ne, ya buga wasa na ƙarshe daga farkonsa ne wa Super Eagles tun a shekarar 2021, a wani wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya da Nijeriya ta yi da ƙasar Cape Vade wanda ta yi…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori ƙarar shuwagabannin ƙananan hukumomi na ɓangaren Wike

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kotun ɗaukaka ƙara reshen jihar Ribas, ta kori ƙararraki biyu da shuwagabannin ƙananan hukumomi da ke ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike suka shigar bayan da ta ce ba su cika ƙa'idojin sauronsu ba. Hon. Enyiada Cookey-Gam da wasu mutum shida suka shigar da su masu ɗuake da lambobi kamar haka; CA/PH/137M/2024 da kuma CA/PH/145M/2024 inda a ciki su ke ƙalubalantar karamar kotu kan hukuncinta na ƙara wa'adin shugabancin majalisar da suka nema. Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce ƙalubalen nasu basu gamsar da tsare-tsaren doka ba don haka, ta yi watsi da su. Ɗaya daga cikin…
Read More
Gwamnan Zamfara ya sami kyautar Shugaban Ƙasa ta NEAPS

Gwamnan Zamfara ya sami kyautar Shugaban Ƙasa ta NEAPS

Daga USMAN KAROFI Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya sami kyautar NEAPS ta Shugaban ƙasa sabida ayyukan da gwamnatin shi ta assasa kuma ta kammala a cikin shekara guda Kyautar NEAPS wani sashi ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya. Kamar yadda wata sanarwar ta fito daga bakin mai magana da yawun Gwamnan Sulaiman Bala Idris, ya shaida cewa an yi wannan bikin bada kyautar ne, ranar Asabar a babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa. Sanarwar ta shaida Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shi ya bada kyautar ga Gwamna Dauda Lawal a madadin Shugaba Tinubu. Sanarwar ta cigaba ta nuna cewa…
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Yadda ƴan majalisa na ɓangaren Fubara da na Wike ke mabambantan zama a Ribas

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ana cigaba da dambarwar siyasa jihar Ribas yayinda ɓangarori biyu na majalisar dokokin jihar ke gudanar da mabanbantan zama a ranar Litinin. A ranar Lahadi ne ƴan ɓangaren gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ƙarƙashin jagorancin Victor Oko-Jumbo na majalisar, suka gayyaci Emmanuel Frank Fubara domin tantance shi a matsayin wanda za bai wa muƙamin kwamishina kuma ɗaya daga cikin mamba majalisar zartarwa ta jihar. Sai dai, a gefe guda, ƴan majalisu da ke ɓangaren tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, ƙarƙashin jagoranci Martin Amaewhule za su yi nasu zaman a rana ɗaya da ƴan Fubara.…
Read More

Badaƙalar biliyan N80.2: EFCC ta gano shirin Yahaya Bello na ficewa daga Nijeriya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), ta ce gano shirin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello na ficewa zuwa ƙasar Maroko daga Kamaru sakamakon zargin badaƙalar biliyan N80.2 a kan sa. Tsohon gwamnan wanda akwai batutuwa 19 na laifuka da ake zargin sa da aikatawa cikin har da badaƙalar kuɗi, zamba cikin aminci da kuma sauya akalan waɗansu kuɗaɗe da adadin su ya kai kimanin Naira biliyan 80.2. Duk da cewa ya musanta aikata laifukan, gwamnan ya ƙi amincewa a lokuta mabanbanta ya bayyana a gaban Alƙali Emeka Nwite. A ranar 27 ga…
Read More

‘Yan sanda sun tabbatar da garkuwa da ƴan jarida biyu da iyalansu a Kaduna

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI 'Yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da sace wasu ƴan jarida biyu tare da iyalansu da aka yi a ranar Asabar da misalin ƙarfe 10:30 na dare. Mai magana da yawun rundunar Mansir Hassan ya faɗi hakan a yayain wata hira da 'News Agency of Nigeria' inda ya ce jami'ansu na ƙoƙari wajen ganin an ceto su daga waɗanda suka yi garkuwa dasu wanda a yanzu haka an watsa tawagar ƴan sandan a yankunan da ake tsammanin suna nan. Mansir ya ce, ɗaya da cikin su shi ne Abdulgafar Alabelewa, shugaban wakilan 'Chapel' na ƙungiyar ƴan…
Read More
An kama dagaci da kansila kan zargin satar taransifoma

An kama dagaci da kansila kan zargin satar taransifoma

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da dakatar da dagacin garin Majidadi da ke yankin ƙaramar hukumar Akko, Mohammed Majidadi bisa zargin hannu a sace wata taransifoma. Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya fitar, ya ce majalisar ƙaramar hukumar Akkon ta kuma dakatar da kansilan mazaɓar Kumo ta Gabas, Abdullahi M. Panda bisa wannan zargi. A baya-bayan nan ne dai rundunar 'yan sandan jihar ta yi baje kolin mutanen biyu da ta ce ta kama bisa zargin haɗa baki da ɓarayi wajen sayar da taransifomar lantarkin Garin Majidadi. Sanarwar ta ce, an…
Read More

Gwamnan Zamfara ya aika saƙon gaisuwar sabuwar shekara ga al’ummar Musulmi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya aika saƙon fatan alkhairi ga al'ummar Musulmin jihar bayan shiga shekarar Hijira ta fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), 1446. Gwamnan, ya yi kira ga al'ummar Musulmi a jihar da ma Nijeriya baki ɗaya da su cigaba da yi wa ƙasa addu'a domin samun zaman lafiya a dukkan sassan da ake fama da matsalolin tsaro. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce sabuwar shekarar Musuluncin lokaci ne na yin nazari ga abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabata. Yau Lahadi ce ranar…
Read More

Kuto ta umarci Sadiya Farouk ta yi bayanin yadda aka sarrafa biliyan N729 ga talakawa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Babbar kotun jihar Legas ta umarci tsohuwar ministar ma'aikatar jinƙai da ci gaban ƙasa, Sadiya Farouk ta yi bayani dalla-dalla kan yadda ta sarrafa Naira biliyan 729 ga talakawan Nijeriya miliyan 24.3 a cikin wata shida. Cikin bayanan da kotun ta buƙaci tsohuwar ministar ta yi sun haɗa da; adadin waɗanda suka ci moriyar kuɗin, jihohin da aka bai wa kasafi da kuma nawa aka bai wa kowacce. Alƙali Deinde Dipeolu ya yi hukuncin bayan da cibiyar tabbatar adalci da Mulki Nagari (SERAP) ta buƙaci a yi hakan ƙarƙashin dokar ƴancin sanarwa ta FHC/L/CS/853/2021. Mataimakin Daraktan…
Read More