Labarai

Gidauniyar Ɗangote ta ƙaddamar da tallafin kayan abinci a Kano

Gidauniyar Ɗangote ta ƙaddamar da tallafin kayan abinci a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci da Gidauniniyar Dangote za ta raba wa al’ummar Nijeriya domin rage musu raɗaɗin rayuwa da suke fuskanta. Da yake ƙaddamar da rabon tallafin a gidan Gwamnatin Kano a ranar Asabar, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga kwamitin da za su gudanar da rabon kayan abincin su zamo masu gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da tallafin ya isa ga mabuƙatan da aka tanadi abincin domin su. Yusuf ya kuma ce tuni tallafin kayan abincin ya isa ga…
Read More
EFCC ta ƙwato wa ’yan fanshon Kano gidajen Kwankwasiyya da tsofaffin gwamnoni suka sayar

EFCC ta ƙwato wa ’yan fanshon Kano gidajen Kwankwasiyya da tsofaffin gwamnoni suka sayar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta'annati, EFCC, ta shiyyar Abuja, ta miqa takardun gidaje 324 da aka ƙwato na ’yan fansho na Jihar Kano ga waɗanda abin ya shafa. Wannan cigaban dai ya biyo bayan wani bincike da hukumar EFCC ta gudanar kan wani asusun fansho na Naira Biliyan 4.1 da gwamnatocin Jihar Kano da suka shuɗe guda biyu suka hana ’yan fansho. Binciken Hukumar EFCC ya biyo bayan koke da wata qungiya mai suna “Concerned Kano State Workers and Pensioners” ta shigar a kan zargin karkatar da kuɗaɗen ’yan fansho a…
Read More
Ɗaliban Kuriga sun shaƙi iskar ‘yanci

Ɗaliban Kuriga sun shaƙi iskar ‘yanci

Daga BASHIR ISAH Bayanai daga Jihar Kaduna na nuni da cewa, ɗaliban firamaren da aka yi garkuwa da su kwanan baya a yankin Kuriga a jihar, sun shaƙi iskar 'yanci. Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, shi ne ya ba da sanarwar hakan a shafinsa na Facebook ranar Asabar da tsakar dare Idan za a iya tunawa, MANHAJA ta rawaito a ranar 8 ga Maris wasu 'yan bindiga suka kai hari yankin Kuriga, cikin Ƙaramar Hukumar Chilun a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da yara sama da 200. Sai dai Gwamnan bai yi wani cikakken bayani kan sako yaran…
Read More
Jihohin Kebbi, Sakkwato, Oyo da Ebonyi na kan gaba a yaran da ke gararamba a titi – Rahoto

Jihohin Kebbi, Sakkwato, Oyo da Ebonyi na kan gaba a yaran da ke gararamba a titi – Rahoto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Nijeriya na fuskantar mawuyacin hali na rashin ilimi, inda miliyoyin yara ke rasa ‘yancinsu na samun ilimi. Manhaja ta lura da cewa duk da karatun firamare a hukumance na ‘kyauta’ kuma wajibi ne, yara da yawa ba sa zuwa makaranta a faɗin jihohi. Wannan rashin samun ilimi yana kawo cikas ga ci gaban mutum da ci gaban ƙasa baki ɗaya. Idan dai ba a manta ba, batun yaran da ba sa zuwa makaranta ba ya watsu a duk faɗin Nijeriya, domin kuwa rahotanni da bayanai sun nuna an sha bayar da gagarumin bambanci tsakanin…
Read More
Mai yiwuwa Tinubu ya sanar da albashi mafi ƙaranci a Ranar Ma’aikata ta Duniya

Mai yiwuwa Tinubu ya sanar da albashi mafi ƙaranci a Ranar Ma’aikata ta Duniya

Daga BASHIR ISAH Alamu bayyanannu na nuni da cewa, akwai yiwuwar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da sabon albashi mafi ƙaranci a ranar 1 ga watan Mayu mai zuwa. Kuma zai yi hakan ne albarkacin bikin Ranar Ma'aikata ta Duniya wanda akan gudanar a ranar farko ga watan Mayu duk shekara. Majiyarmu ta ce, Kwamitin Albashin na Ƙasa na aiki tukuru don tabbatar da an cimma dukkan sharuɗɗan da aka shimfiɗa dangane da sabon albashi mafi ƙarancin. Majiya ta kusa da kwamitin ta ce, "Kwamitin Albashi zai sake zama ya zuwa makon gobe. Zama ne wanda kwamitin zai karɓi…
Read More
Na fi tunanin sojojin haya ne suka kashe sojoji 17 a Delta – Akpabio

Na fi tunanin sojojin haya ne suka kashe sojoji 17 a Delta – Akpabio

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio ya bayyana cewa mutanen da suka yi wa sojojin qasar 17 kisan gilla a jihar Delta na iya zama sojojin haya ba wai mutanen yankin Neja Delta ba. Ya bayyana haka ne a zaman majalisar na ranar Talata, kwana biyar kenan bayan faruwar mummunan harin. Akpabio ya yi tsokacin ne lokacin da majalisar ta yanke shawarar kafa kwamiti domin gano abin ya janyo kashe sojojin. Ya ce "Ba na son na yanke hukunci cewa waɗannan mutanen daga yankin Neja Delta suka fito saboda muna mutunta mata da zama…
Read More
Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 106 a mako guda — DHQ

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 106 a mako guda — DHQ

*Ana ci gaba da farautar waɗanda suka kashe sojoji 18 a Delta Daga BASHIR ISAH Babban Ofishin Tsaro (DHQ) da ke Abuja ya ce ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen farauto ɓata-garin da suka kashe sojoji a Jihar Delta. Mai magana da yawun rundunar, Manjo-Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a ranar Juma'a. Ya ce faɗi-tashin da sojoji ke ci gaba da yi na yaƙi da ta'addancin, suna yi ne don amfanin ƙasa. A cewarsa, ”A ci gaba da ayyukan yaƙi da matsalolin tsaro sojoji sun ceto mutane da dama waɗanda aka yi garkuwa da su tare…
Read More
Sakamakon cire tallafin mai: Adadin fetur da ake amfani da shi a Nijeriya ya ragu da lita biliyan guda – Idris

Sakamakon cire tallafin mai: Adadin fetur da ake amfani da shi a Nijeriya ya ragu da lita biliyan guda – Idris

Daga BASHIR ISAH Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Muhammad Idris, ya bayyana cewa, adadin man fetur da ake amfani da shi a Nijeriya ya ragu da lita biliyan ɗaya, kwatankwacin kashi 53 na adadin man da ake amfani da shi gabanin cire tallafin mai. A cewarsa, hakan ya faru ne sakamakon tallafin fetur da gwamanti ta cire a watan Mayun Bara. Ya bayyana haka ne a wajen buɗe-baki tare da 'yan jarida da aka shirya kwanan nan a Kano. Idris ya ce, la'akari da yawan raguwar amfani da fetur da aka gani, hakan na nuni da…
Read More
Hedikwatar Tsaro na neman su Dogo Gide, Simon Ekpa, Bello Turji da sauransu ruwa a jallo

Hedikwatar Tsaro na neman su Dogo Gide, Simon Ekpa, Bello Turji da sauransu ruwa a jallo

Daga BASHIR ISAH A ƙalla 'yan bindiga, ɓarayin daji da tsageru 97 ne Babban Ofishin Tsaro da ke Abuja ya bayyana a matsayin waɗanda yake nema ruwa a jallo. Ofishin ya ce waɗanda yake neman suna da hannu wajen aikata manyan laifuka da tada zaune tsaye a sassan ƙasa. Har wa yau, waɗanda lamarin ya shafa ya haɗa da shugaban wani ɓangare na tsagerun IPOB, wato Simon Ekpa. Mai magana da yawun rundunar soji, Manjo-Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana sunaye da hotun waɗanda rundunar ke farautarsu. MANHAJA ta rawaito a makon jiya cewa, Babban Ofishin tsaro na shirin…
Read More
Gwamnati ta dakatar da karɓar kashi 25 kan motocin da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba

Gwamnati ta dakatar da karɓar kashi 25 kan motocin da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba

Daga BASHIR ISAH Ministan Tattalin Arziki kuma mai sanyo ido kan fannin kuɗi, Mr. Wale Edun, ya unarci Hukumar Kwastom da ta dakatar da karɓar kashi 25 daga hannun masu shigo da motoci daga ƙetare ba bisa ƙa'ida ba. Kakakin hukumar na ƙasa, Abdullahi Maiwada, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a. Kwanan nan ne Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar buɗe dama na tsawon kwana 90 don shigowa da wasu keɓaɓɓun motoci. Da ma dai hukumar kan amshi kashi 25 kan motocin da aka shigo da su ba bisa ƙa'ida ba a matsayin…
Read More