Labarai

Gyaran masallacin Idi: Sanata Barau zai kashe sama da Naira miliyan 400 a Bichi

Gyaran masallacin Idi: Sanata Barau zai kashe sama da Naira miliyan 400 a Bichi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Sanatan Kano ta Arewa kuma mataimaki shugaban majalisar datttawa ta ƙasa, Barau Jibrin Maliya, ya bada umarni fara aikin zagaye babban masallaci Idi na Masarautar Bichi tare da saka interlocks. Da yake jawabi lokacin ƙaddamar da aikin jagoran tafiyar gidan Sanata Barau I. Jibrin na ƙaramar hukumar Bichi Sani Muƙaddas Barden Bichi wanda Alh. Garba Ɗandawaki ya wakilta, ya ce Sanatan ya bada umarnin yin aikin ne saboda kishinsa ga addinin Musulunci. Ya ce ba yi mamakin irin wannan aikin Allah da Sanata Barau Jibrin zaiyi ba, domin daman aikin sa ne ya saba a…
Read More
Yanzu-yanzu: An ceto ɗaliban tsangaya da aka yi garkuwa da su a Sakkwato

Yanzu-yanzu: An ceto ɗaliban tsangaya da aka yi garkuwa da su a Sakkwato

Kimanin makonni biyu da suka gabata ne aka 'yan bindiga suka sace yaran su 15 a wata makatrantar tsangaya da ke kauyen Gidan Bakuso a yankin Kaeamae Hukumar Gada. MANHAJA ta kalato cewa, 'yan bindigar da suka yi awon gaba da yaran sun bukaci a a biya su Naira miliyan 20 kafin su sako yaran. Shigaban makaranar, Liman Abubakar, shi ne ya bayyana wa majiyarmu haka a ranar Talata. Ya zuwa hada wannan labari, babu wani cikakken bayani kan ko sai da aka biya kudin fansa kafin aka sako yaran ko kuwa a'a.
Read More
’Yan sanda sun yi karar Jaruma Amal kotu bayan kotu ta wanke ta

’Yan sanda sun yi karar Jaruma Amal kotu bayan kotu ta wanke ta

Daga AISHA ASAS  Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya Shiyya ta Ɗaya (wato Zone 1) ta kai ƙarar fitacciyar jaruma a Kannywood, Amal Umar, gaban kotu kan zargin bayar da toshiyar baki ga wani ɗan sanda da ke binciken ta kan zargin aikata wata almundahanar kuɗi da ake zargin da sa hannunta a ciki, duk da cewa, kotu ta wanke jarumar tun a watannin baya. A jiya Alhamis ne aka gurfanar da jarumar a kotun Majistare mai lamba 24 da ke Jihar Kano.  Da yake jawabi a gaban manema labarai, Kakakin Rundunar 'Yan Sanda Na Shiyya Ta Ɗaya, CSP Bashir Muhammad, ya…
Read More
Ramadan: Dubban ‘yan Nijeriya za su rasa Umara sakamakon matakin hana biza da Saudiyya ta ɗauka — Rahoto

Ramadan: Dubban ‘yan Nijeriya za su rasa Umara sakamakon matakin hana biza da Saudiyya ta ɗauka — Rahoto

Daga BASHIR ISAH Akwai yiwuwar bana 'yan Nijeriya da dama ba za su samu yin Hajjin Umar ba a wannan wata na Ramadana. Hakan ba ya rasa nasaba da matakin da Ƙasar Saudiyya ta ɗauka na dakatarwa ko taƙaita da bayar da bizar zuwa yin Umara a ƙasar. Wannan al'amari ya tada hankalin jama'a musamman masu niyyar zuwa Umara domin ninka ibadarsu a watan Azumin Ramdan. Haka su ma kamfanonin shirya tafiye-tafiye zuwa Hajji da Umara sun nuna damuwarsu kan matakin wanda tuni ya haifar musu da asara sakamakon sauke musu bukin na masaukan da suka kama a biranen Makka…
Read More
Falastinawa a Gaza na fama da matsananciyar yunwa – Ofishin jakadancinsu a Nijeriya

Falastinawa a Gaza na fama da matsananciyar yunwa – Ofishin jakadancinsu a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ofishin Jakadancin Falastinu a Nijeriya ya bayyana cewa, a rana ta 167 na yaƙin kisan ƙare dangi da ake yi wa al'ummar Falastinu, mutanen Gaza mata da qananan yara na fama da matsananciyar yunwa, rashin ingantaccen kiwon lafiya da sauran wahalhalu. Jakadan Falastinu a Nijeriya, Abu Shawesh ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis.  Sanarwar ta ce, "Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres da Babban jami'in kare haqqin bil'adama na Majalisar Ɗinkin Duniya Volker Turk sun bayyana irin matsananciyar wahalar da ake fama da ita a garin…
Read More
An sace fasinjoji a hanyar Ƙanƙara dake Katsina 

An sace fasinjoji a hanyar Ƙanƙara dake Katsina 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ’yan bindiga sun yi sace fasinjoji da dama a wani harin da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara da ke Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis bayan da ’yan bindigar dajin suka tare wata mota ƙirar bas mai cin mutane 18 mai lamba 14B-300-KT cike maƙil da fasinjoji mallakar hukumar kula da sufuri ta Jihar Katsina (KSTA). Wani ganau ya shaida wa majiyarmu ta wayar tarho cewa, galibin fasinjojin da ke cikin motar sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Funtuwa a kan hanyarsu ta zuwa Katsina, Babban Birnin Jihar Katsina.…
Read More
Minista ya tono yadda aka riƙe wa gwamnati kuɗin samar da mitar lantarki tsawon shekara 21

Minista ya tono yadda aka riƙe wa gwamnati kuɗin samar da mitar lantarki tsawon shekara 21

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Kula da Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa wani kamfani mai zaman kansa, Messrs Ziklagsis ya riƙe har Naira biliyan 32 da aka biya a asusunsa a shekarar 2003 domin samar da mitoci miliyan uku da aka riga aka biya. Ministan, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin sadarwa da hulɗa da manema labarai, Bolaji Tunji, ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya ta ƙulla yarjejeniya da Messrs Ziklagsis Network Limited da Unistar International a shekarar 2003 kan samar da mitoci miliyan uku don rabon wutar lantarki…
Read More
Gina al’umma: Tsakaninmu da Gwamna Buni sai godiya – Hon. Lawan Bukar

Gina al’umma: Tsakaninmu da Gwamna Buni sai godiya – Hon. Lawan Bukar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Bursari a Jihar Yobe, Hon. Lawan Bukar ya bayyana cewa ba su da abinda za su ce wa gwamnan jihar Mai Mala Buni sai sam-barka, domin a cewarsa yana iyakacin ƙoƙarinsa na ganin ya sauke nauyin da al'ummar jihar ta ɗora masa. Bukar ya ce Gwamna Buni ya tallafa wa kananan hukumomin jihar wajen ƙarfafa wa da inganta rayuwar jama'a musamman masu ƙaramin ƙarfi da gidajen marayu; samar da aikin yi ga matasa a ƙaramar hukumar Bursari da suka haɗa da: Samar da ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya a cikin…
Read More
Kayan miliyoyin Naira sun kone a gobarar kasuwar Legas

Kayan miliyoyin Naira sun kone a gobarar kasuwar Legas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kayayyaki da darajarsu ta kai na miliyoyin Naira sun kone kurmus a ranar Larabar da ta gabata, yayin da wata gobara ta tashi a wasu shaguna a sashen Nnamdi Azikiwe da Docemo na Kasuwar Idumota a Jihar Legas. Gobarar ta shafi gine-gine guda uku da suka haɗa da benaye biyu da wani gini mai hawa uku a kasuwar waɗanda suka shahara  wajen sayar tufafi da jaka da takalma. Hukumar kashe gobara ta jihar Legas da sauran masu bada agajin gaggawa sun isa wurin, inda suka yi ta koƙarin aikin kashe gobarar. "Hukumomin kashe gobara a Ebute…
Read More
Tinubu zai tsige ministocin da suka gaza kataɓus

Tinubu zai tsige ministocin da suka gaza kataɓus

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Nijeriya Bola Tinubu yana shirin fara wani tsari mai matakai uku domin tantance ƙoƙarin ministoci, shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati. Manufar ita ce samar da wani shafi da zai ba jama'a damar yin bayanai game da koƙarin ministocin da ba da shawarar waɗanda za a riƙe da waxanda za a kora. Wannan yunkuri na zuwa ne yayin da Gwamnatin Tinubu ke tunkarar bikin cika shekara gyda a kan madafun iko a ranar 29 ga Mayu, 2024. Wasu majiyoyi masu ƙarfi a fadar shugaban kasa sun ce Shugaban kasar Tinubu zai ƙaddamar da wannan shafi ne…
Read More