Labarai

Adadin waɗanda aka kashe a Gaza ya ƙaru zuwa 31,819 — Abu Shawesh

Adadin waɗanda aka kashe a Gaza ya ƙaru zuwa 31,819 — Abu Shawesh

Daga BASHIR ISAH Ofishin jakadancin Falasɗin a Nijeriya, ya bayyana cewa yazu ran Laraba, 20 ga Maris, 2024 adadin Falasɗinawa da aka kashe Gaza ya kai 31,819, yayin da 73,934 sun jikkata, sannan kimanin mutum 8,500 sun ɓace ba tare da an san inda suke ba. Jakadan Falasɗin a Nijeriya, Abdullah M. Abu Shawesh, shi ne ya bayyana haka a cikin sanarwar manema labarai da ya fitar ranar Alhamis. Jakadan ya ce baya ga kisan kiyashi da yankin Gaza ke fuskanta daga Isra'ila, yankin na kuma fama da matsanancin ƙarancin abinci, wanda a cewarsa wannan shi ne irinsa na farko…
Read More
‘Ban fuskanci wata matsala ba wajen sauya jinsina’ – Bobrisky

‘Ban fuskanci wata matsala ba wajen sauya jinsina’ – Bobrisky

Daga BASHIR ISAH Matashin ɗan Nijeriyar nan da ya sauya jinsinsa zuwa mace, wato Bobrisky, ya ce komai ya tafi daidai na aikin sauya masa jinsi da aka yi daga namiji zuwa mace. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Bobrisky ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka yi masa aiki cikin nasara, yana mai cewa babu wata matsala da ya fuskanta a yayin aikin. A cikin saƙon nasa, ya bayyana godiyarsa ga likitocinsa na gida da ƙetare bisa ƙoƙarin da suka yi wajen sauya masa jinsi zuwa mace. Majiyarmu ta rawaito Bobrisky na cewa, “Komai na…
Read More
Matsalolin Nijeriya za su gushe ba da daɗewa ba – Idris

Matsalolin Nijeriya za su gushe ba da daɗewa ba – Idris

Daga BASHIR ISAH Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Mohammed Idris, ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su ƙara haƙuri sannan samu yaƙini game da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu saboda ƙoƙarin da take yi wajen magance matsalolin da suka addabi ƙasa. Idris ya ce gwamnati na aiki ba dare ba rana wajen daidaita lamurran ƙasa, tare da cewa za a shawo kan ƙalubalenbda suka addabi ƙasa nan ba da daɗewa ba. Ministan ya yi wannan kira ne a wajen taron buɗe-baki tare da 'yan jarida wanda Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa ta…
Read More
Gwamnati ta lissafa Mamu da wasu mutum 14 a matsayin masu ɗaukar nauyin ta’addanci

Gwamnati ta lissafa Mamu da wasu mutum 14 a matsayin masu ɗaukar nauyin ta’addanci

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta lissafa Tukur Mamu tare da wasu mutum 14 a matsayin masu ɗaukar nauyi ayyukan ta’addanci a ƙasa. Sashen tattara bayansn sirri kan hada-hadar kuɗi (NFIU) ya bayyana sunayen  mutum 15 da lamarin ya shafa, da suka haɗa da wasu mutum tara da cibiyoyin canji (BDC) shida da uma wani kamfani ɗaya. Bayanan NFIU sun nuna cewar Kwamitin Kafa Takunkumi na Ƙasa ya yi zama a ranar 18 ga Maris, inda a Ƙarshen zaman nasa ya bada shawarar kafa wa wasu takunkumi saboda samun da aka yi da hannu a ɗaukar nauyin ta’addanci. Ɗaya daga…
Read More
Ilimi ne ƙashin bayan cigaban Zamfara – Lawal

Ilimi ne ƙashin bayan cigaban Zamfara – Lawal

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ayyana ilimi a matsayin ƙashin bayan cigaban Jihar Zamfara. Lawal ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙincin ɗaliban makarantar Leadsprings International School a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau a ranar Laraba. Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce yayin ziyarar, ɗaliban sun miƙa wa Lawal muhimman ƙudurori guda bakwai don amfanin gaba. Suleiman ya ce ƙudurorin sun haɗa da raya babban birnin jihar, wato Gusau, inganta fannin tsaro, samar da kamfanin jirgin sama mallakar Zamfara, bunƙasa fasaha, bunƙasa fannin noma, ɓangaren kasuwanci da sauransu. Sa'ilin da…
Read More
Majalisar Dattawa ta amince da Dokar bai wa ɗalibai rance ta 2024

Majalisar Dattawa ta amince da Dokar bai wa ɗalibai rance ta 2024

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dattawa ta Nijeriya ta amince da Dokar bai wa ɗalibai rancen karatu ta 2024 wanda ɗalibai a manyan makarantu za su ci gajiya. Majalisar ta amince da hakan ne bayan da ta karɓi rahoton Kwamitin Majalisar kan Manyan Makarantu da asusunTETFUND. Shugaban Kwamitin, Sanata Muntari Dandutse (APC – Katsina ta Kudu), shi ne ya gabatar da rahoton yayin zaman malajisar a ranar Laraba. Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar dattawa da ta wakilai buƙatar neman soke dokar bai wa ɗalibai rancen karatu (ga…
Read More
Zargin $300m: Majalisar Wakilai ta yi barazanar tsare ministan lafiya muddin ya ƙi amsa gayyatarta

Zargin $300m: Majalisar Wakilai ta yi barazanar tsare ministan lafiya muddin ya ƙi amsa gayyatarta

Daga BASHIR ISAH Kwamitin Majalisar Wakila kan yaƙi da zazzaɓin Maleriya, HIV/AIDS da Tarin Fuka, ya bai wa Ministan Lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, sa’o’i 72 kan ya bayyana a gabanta ko kuma ta sa a kamo shi. Gayyatar ta shafi har da Babban Sakatariyar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, wato Daju Kachollom. Majalisar ta buƙaci Pate da Kachollom su abayyana a gabanta ne domin amsa tambayoyi kan zargin karkatar da Dala miliyan 300 da aka ware domin yaƙi da zazzaɓin maleriya tun daga 2021. Kwamitin ya yanke shawara kan cewar a damƙo Babbar Sakatariyar muddin ta ƙi amsa gayyata, saboda…
Read More
Sojoji sun ceto mutum 16 a hannun ‘yan bindiga a Katsina

Sojoji sun ceto mutum 16 a hannun ‘yan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Jami'an soji dake da sansani a Marabar Mai-Gora sun samu nasarar ceto waɗansu mutane da 'yan bindiga suka sace tare da yin garkuwa da su tun kimanin kwanaki 46 da suka wuce. Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da mata 10 da kuma ƙananan yara shida. Sojoji sun taki wannan nasarar ce a lokacin da suke gudanar da sintiri a garin Rimi. Wadanda aka ceto ɗin, na daga cikin mata 54 da barayin daji suka sace a hanyar Gamji zuwa Ɗandume a farkon watan Fabarairun da ya gabata. Sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina,…
Read More
Farfesa Suleiman na NSUK ya taka rawar gani – Dokta Suleiman

Farfesa Suleiman na NSUK ya taka rawar gani – Dokta Suleiman

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Shugaban Kwalejin Nazarin Kiwon Lafiya na Jihar Nasarawa da ke garin Keffi, Dokta Abdullahi Suleiman Mohammed, ya ce babu shakka takwaransa na Jami'ar Jihar (NSUK), wato f'Farfesa Suleiman Bala Mohammed, ya taka rawar gani wajen haɗa kawunan shugabannin manyan makarantun da ke faɗin Jihar. Dokta Suleiman ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattauna da wakilin mu a ofishin sa dake kwalejin ranar Laraba ta wannan makon Ya ce Farfesa Suleiman wanda wa'adin mulkin sa zai ƙare a watan Maris da ake ciki, kafin yanzu ya yi ƙoƙarin haɗa kawunan takwarorinsa don ci…
Read More
Gobara ta laƙume gidaje a Legas

Gobara ta laƙume gidaje a Legas

Daga BASHIR ISAH Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da aukuwar gobara a wasu jerin gine-gine guda uku kusa da ke Dosumu- Idomota, a yankin Lagos Island a Jihar Legas. Majiyarmu ta ce gine-ginen da lamarin ya shafa, benaye ne masu hawa uku da huɗu. Ya zuwa haɗa wannan labari, NEMA ta ce ba a kai ga gano dalilin tashin gobarar ba. Jami’in NEMA, Ibrahim Farinloye, ya ce hukumar ta fuskantar ƙalubale wajen ƙoƙarin kashe gobarar.  “Muna fuskantar babban ƙalubale wajen samun ruwan da za a yi amfani da shi wajen kashe gobarar,” in ji shi. Ya…
Read More