Labarai

’Yan sanda sun kama mahaifin da ya harbe ɗansa saboda abinci

’Yan sanda sun kama mahaifin da ya harbe ɗansa saboda abinci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sanda a Jihar Abiya ta kama wani mutum da ake zargi da harbe ɗansa bayan da ya fusata saboda ya cinye abinci. Lamarin ya faru ne a yankin Eziama Lokpaukwu da ke ƙaramar hukumar Umunneochi a jihar Abiya. Shaidu sun ce ɗan ya shiga gidan inda ya ɗauki abincin da aka ajiye a tukunya tare da cinyewa. Lamarin ya fusata mahaifinsa saboda rashin neman izini kafin cinye abincin sai kuma suka ce ya shiga ɗaki tare da harbe ɗansa. Mutanen yankin sun fusata inda suka damke mahaifin tare da ƙulle shi kafin…
Read More
Za mu yi iyakar ƙoƙari wajen kare mutuncin ’yan Arewa a Ogun – Sabbin sarakunan Hausawa

Za mu yi iyakar ƙoƙari wajen kare mutuncin ’yan Arewa a Ogun – Sabbin sarakunan Hausawa

Daga DAUDA USMAN a Legas Waɗansu sababbin tagwayen sarakunan al'ummar Hausawa mazauna cikin garin Muwe da ke cikin jihar Ogun sun bayyana cewar za su yi iyakar ƙoƙarinsu wajen kare martabar masarautar al'ummar Hausawan Muwe tare da kawo ci gaban Hausawan yankin baki ɗaya. Sababbin sarakunan sun yi wannan furuci ne a garin Muwe jim kaɗan bayan tashi daga taron naɗa su muƙamai daban-daban a cikin garin Muwe kuma suka bayyana wa jaridar Manhaja farin cikinsu dangane da wannan al'amari. Taron naɗin sarautun wanda ya gudana a garin na Muwe a ranar Lahadin makon jiya sunayen sababbin tagwayen sarakunan da…
Read More
’Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 a Taraba

’Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 a Taraba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan sanda da mafarauta sun kuɓutar da mutum 49 da aka yi garkuwa da su a sansanin masu garkuwa da mutane da ke tsaunin Gongomaliki a yankin ƙaramar hukumar Yorro da ke jihar Taraba. Kwamishinan 'yan sandan jihar, David Iloyanomon, ne ya bayyana haka cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai a birnin Jalingo. Kwamishinan ya ce jami'an sun samu nasarar kuɓutar da mutanen ne bayan samun bayanan sirri game da ayyukna ɓata-garin a yankin. “Wannan na daga cikin yunƙurin da hukumarmu ke yi na kakkaɓe ayyukan ɓata-gari, musamman garkuwa da mutane…
Read More
Maɗaba’ar Kano ta samu kayan aiki da za ta zama ta ɗaya a Arewa – DMD Adamu

Maɗaba’ar Kano ta samu kayan aiki da za ta zama ta ɗaya a Arewa – DMD Adamu

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Maɗaba'ar Gwamnatin Kano KPPC mai buga muhimman takardun sirrin gwanati da sauran takardun amfanin al'umma da wallafe-wallafe na gwamnati da na kamfanoni da sauran al'umma yanzu haka ta farfaɗo da ga dogon suman da ta yi na rashin aikin yi da rashin kayan aiki wanda yanzu ta samu kayan aikin da za ta iya zama ta ɗaya Arewacin Nijeriya kamar yadda Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake son ganinta, wanda hakan ce tasa daga zuwansa ya ba su  dama da busa mata rai ta farfaɗo ta hanyar bada damar a cewa dukka abinda muke…
Read More
Masu ruwa da tsaki sun koka kan garƙame iyakar Nijar

Masu ruwa da tsaki sun koka kan garƙame iyakar Nijar

Daga Jamil Gulma a Kebbi  Tun lokacin da Shugaban Ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tunubu, wanda kuma shine Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ya ayyana cewa, akwai yiwuwar ƙaddamar da yaƙi da sojojin da suka hamɓarar da zavavven Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadu Bazoum, idan sulhu ya gagara, ba shakka wannan ya tayar da  hankalin dubban ’yan Nijeriya mazauna ƙasar ta Nijar da kuma al'ummomin da ke zaune kan iyakokin ƙasashen biyu kuma ya sanya su shiga wani yanayi na tashin hankali. Wakilin Bleuprint Manhaja ya zagaya  waɗansu garuruwa da ke maƙotaka da Nijar din kuma ya zanta da mazauna waɗannan…
Read More
Masu zanga-zanga sun daka wawa kan babbar mota mai ɗauke da taliyar BUA a Zaria

Masu zanga-zanga sun daka wawa kan babbar mota mai ɗauke da taliyar BUA a Zaria

Daga BASHIR Wasu masu zanga-zanga a yankin Dogarawa a Zaria, jihar Kaduna, sun daka wawa kan wata babbar motar kamfanin BUA mai ɗauke da kayan taliya a kan babbar hanyar Zaria zuwa Kano. Wannan na zuwa ne kimanin mako guda bayan da wasu jama'a suka daka wawa kan wata babbar mota mai ɗauke da kayan abinci a yankin Sulej, Jihar Neja. Majiyarmu ta ce motar BUA ɗin ta baro Kaduna ne da nufin zuwa Abuja inda 'yan daban suka tare hanya suka far mata. Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma'a da misalin ƙarfe 3.15 na…
Read More
Sojojin Nijeriya na iya murƙushe ‘yan ta’adda – Gwamna Sule

Sojojin Nijeriya na iya murƙushe ‘yan ta’adda – Gwamna Sule

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce sojojin Nijeriya na da ƙarfin da za su iya lalata duk wasu masu ɗauke da makamai da ke dagula zaman lafiyar al’umma. Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a yayin gudanar da ayyukan jin daɗin jama’a na Afirka ta Yamma na 2023 na rundunar sojojin Nijeriya ta IV a ƙaramar hukumar Doma ta jihar. Gwamnan ya yaba da kokarin sojoji da sauran jami’an tsaro a yaƙin da suke yi da garkuwa da mutane, ‘yan fashi da sauran matsalolin tsaro a ƙasar nan.…
Read More
An kashe mai juna biyu a turmutsutsun sayen shinkafar Kwastom

An kashe mai juna biyu a turmutsutsun sayen shinkafar Kwastom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mutane bakwai, ciki har da mace mai juna biyu sun rasu a yayin turereniyar sayen shinkafar da Hukumar Kwastam ta yi gwanjo a kan N10,000 kowane ƙaramin buhu a Jihar Legas. Wasu da dama kuma sun jikkata a turereniyar da ta barke a lokacin da wasu bata-gari suka yi yunƙurin shiga ofishin hukumar da ke gwanjon shinkafar da ƙarfin tuwo. Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da hukumar ta fara gwanjon shinkafar a ofisinta da ke yankin Yaba. Gwanjon shinkafar da hukumar ke yi wani ɓangare na yunƙurinta rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin tsadar…
Read More
MOPPAN ta nuna damuwa kan murabus ɗin Kwamandan Hisba

MOPPAN ta nuna damuwa kan murabus ɗin Kwamandan Hisba

*Ta buƙaci Daurawa ya sake nazari kan matakin da ya ɗauka Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Nijeriya (MOPPAN) ta nuna damuwarta kan ajiye muƙami da Sheikh Aminu Daurawa ya yi a matsayin Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Kano. MOPPAN ta ce Daurawa ya ajiye muƙamin nasa ne bisa dalilin rashin ƙwarin gwiwa daga ɓangaren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ta fitar a ranar Juma'a mai ɗauke da sa hannun Sakataren Hulɗa da Jama'a na Ƙasa, Al-Amin Ciroma. MOPPAN ta bakin Shgugabanta na Kasa, Habibu Barde, ta ce tana…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Shugaban Hisbah, Sheikh Daurawa ya ajiye muƙaminsa

Da Ɗumi-ɗumi: Shugaban Hisbah, Sheikh Daurawa ya ajiye muƙaminsa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Hukumar Hisbah a Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar da ajiye muƙaminsa a matsayin Babban Kwamandan Hisbah, tare da nuni davrashin ƙwarin gwiwa daga ɓangaren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf. Daurawa ya ce duk da ƙoƙarin da yake yi wajen kyauta tarbiyya a jihar a matsayinsa na shugaban Husbah, amma cewa ya karaya da yanayin kamalaman gwamnan. Faifan bidiyonnya ya yaɗa a shafinsa na soshiyal midiya, Malamin ya ce, "Yanzu haka ina Jihar Kaduna ina ganawa da 'yan majalisa ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar don tattauna aiwatar da dokar yin gwaji kafin aure a Kano…
Read More