01
Mar
Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ta ce ta yi wa 'yan jihar su 2,213 magani kyauta albarkacin shirinta na kula da lafiya kyauta da take gudanarwa. Gwamnatin ta ce kawo yanzu ta kammala kashi na uku na shirin wanda aka samar domin kyautata lafiyar 'yan jihar musamman masu fama da rashin lafiya. Wannan bayani na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta ce kashi na uku na shirin ya gudana ne daga ranar 23 zuwa 25 na Fabrairun 2024. “Gwamnatin Gwamna…
