Labarai

‘Za mu ci gaba da zanga-zanga’ — cewar NLC

‘Za mu ci gaba da zanga-zanga’ — cewar NLC

*Ganawarsu da gwamnati ba ta haifar da ɗa mai ido ba Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce za ta ci gaba da zanga-zangarta tun da ba a cimma maslaha ba a taron da suka yi da Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin. Ɓangarorin biyu sun gana ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja da zummar lalubo bakin zare dangane da zanga-zangar da NLC ke kan gudanarwar domin nuna rashin jin daɗinta da halin tsadar rayuwar da 'yan ƙasa ke fuskanta. Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya ce "Za a ci gaba da zanga-zangar, kuma haƙƙi…
Read More
Tsadar Rayuwa: NLC na zanga-zanga a sassan ƙasa

Tsadar Rayuwa: NLC na zanga-zanga a sassan ƙasa

Daga BASHIR A halin da ake ciki, haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta shirya zanaga-zangar lumana a sassan ƙasa domin nuna rashin jin daɗinta game da ƙuncin rayuwar da 'yan ƙasa ke fuskanta. Bayanan da MANHAJA ta kalato a ranar Talata sun nuna an hangi masu zanga-zangar a yankin Ikeja, Jihar Legas. Inda aka ga da damansu ɗauke da kwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban kamar "A kawo ƙarshen yunwa da talauci yanzu" da dai sauransu. A Jos babban birnin Filato ma haka lamarin yake, a nan ma an ga ɗaruruwan masu zanga-zangar sun mamaye wasu manyan hanyoyin birnin.…
Read More
‘Yar Nijeriya ta lashe Gasar Karatun Ƙur’ani ta ƙasa da ƙasa

‘Yar Nijeriya ta lashe Gasar Karatun Ƙur’ani ta ƙasa da ƙasa

Daga BASHIR ISAH Wata matashiya mai suna Hajara Ibrahim Dan’azumi daga Jihar Gombe ta lashe Gasar Karatun Ƙur'ani ta Mata zalla ta Ƙasa da Ƙasa da aka gudanar a ƙasar Jordan. Hajara Ibrahim wadda ɗalibar makarantar Islamiyyar Abubakar Siddiq ce kuma 'yar aji biyu a Jami'ar Jihar Gombe, ta zo ta ɗaya ne a rukunin masu karanta izifi 60 da Tajwid a tsakanin ƙasashe 39 da suka fafata a gasar. Wannan shi ne karo na 18 da ake shirya wannan gagarumar gasar karatun Ƙur'ani ta mata zalla a ƙasar ta Jordan. Yayin gasar wadda ta gudana daga 17 zuwa 22…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 17, sun kashe ɗaya a Katsina

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 17, sun kashe ɗaya a Katsina

Daga SANUSI MUHAMMAD Wasu gungun ‘yan ta’adda sun kai farmaki garin Burdugau da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi a jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da mutane sama da 17 tare da kashe mutum ɗaya. Wakilinmu ya rawaito cewa, yayin farmakin ‘yan bindigan sun isa garin ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren Lahadi inda suka shiga gida-gida. Majiya ta ce 'Sun yi awon gaba da ɗaruruwan dabbobin da suka haɗa da awaki, tumaki, shanu, sun yi garkuwa da mata sama da 17, musamman matan aure da wasu 'yan mata, sun kashe mutum ɗaya da aka fi sani da suna Uban…
Read More
Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin NARTO da NURTW a Nasarawa – Muhammadu Maikwarya

Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin NARTO da NURTW a Nasarawa – Muhammadu Maikwarya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Sabon Shugaban Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri, NURTW, na ƙasa reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Muhammadu Maikwarya ya bayyana cewa, ba shakka kawo yanzu da ya kama aikinsa a matsayin sabon shugaban ƙungiyar ta Nasarawa ana cigaba da samun kyakkyawar dangantaka tsakanin ƙungiyar tasa da takwararta ta NARTO. Alhaji Muhammadu Maikwarya ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa da ke hedikwatar NURTW a birnin Lafiya, fadar gwamnatin jihar ranar Litini na mako da ake ciki. Ya ce kasancewa shi shugaban NARTO a jihar ɗan uwa ne a gunsa sannan dukan…
Read More
Zancen banza ne ‘yan bindiga ke yi na cewar za su kai mani hari – Raɗɗa

Zancen banza ne ‘yan bindiga ke yi na cewar za su kai mani hari – Raɗɗa

Daga Umar Garba a Katsina Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana cewar tun da ya zama gwamnan jihar Katsina ba qaramar hukumar da ta gagare shi shiga saboda tsoron ta'addacin 'yan bindiga a jihar. "Zancen banza ne 'yan bindiga ke yi cewar za su kai mani hari, ba inda ɗan ta'adda zai hana ni zuwa a Katsina, ba kuma hanyar da zai hana ni bi." Inji gwamnan. Raɗɗa na mayar da martani ne lokacin da yake zantawa da majiyar jaridar Manhaja ta DW, game da wani rahoto dake cewa 'yan bindiga na shirin kai ma shi hari…
Read More
Mun sha alwashin inganta fannin ilimin Zamfara – Lawal

Mun sha alwashin inganta fannin ilimin Zamfara – Lawal

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bada tabbacin gwamnatinsa ta bada himma wajen samar da ilimi mai nagarta a Zamfara. Ya bayyana hakan ne sa'ilin da yake jawabi a wajen gasar wasannin motasa jiki na bana wadda makarantar Almufida International Academy ta shirya a Gusau, babban birnin jihar. Kakakin Gwamana, Sulaiman Bala Idris, ya ce mamallakin makarantar ya karrama Gwamna Lawal da kambar yabo ta 'Grand Commander of Friends of the College' (GCFC). Da yake jawabi, Lawal ya nuna gamsuwarsa dangane da bajintar da ɗaliban makarantar suka nuna a gasar tare da yaba wa hukumar makaranta…
Read More
Buƙatar samar da ’yan sandan jihohi

Buƙatar samar da ’yan sandan jihohi

Ƙirƙirar 'yan sandan jihohi dai ta kasance batun da ya daɗe ana muhawara a kai a Nijeriya. Bayan kwashe shekaru masu yawa, shugabannin Nijeriya sun samu matsaya kan batun samar da rundunar 'yan sanda jihohi a ƙasar. A makon da ya gabata, Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin jihohi 36 suka tattauna kan batun samar da 'yan sandan jihohi don magance matsalolin tsaro da ke barazana ga ƙasar, waɗanda suka haɗa da satar mutane da fashi da makami da suka zama ruwan dare. Ƙudirin samar da 'yan sandan jihohi a Nijeriya ya tsalake karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai domin…
Read More
Tashin kayan masarufi na barazanar durƙusar da kasuwanci – ‘Yan kasuwar Kano

Tashin kayan masarufi na barazanar durƙusar da kasuwanci – ‘Yan kasuwar Kano

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Gamayyar shugabannin ƙungiyoyin 'yan kasuwar Kano da suka yi wani gangami da kira da gwamnatin Bola Tinubu sun shawarci gwamnatin Njeriya da ta ɗauki matakin gaggawa ko kuma kasuwanci ya durkushe gabaki ɗaya a Nijeriya musamman a wannan lokaci da dala ta haura Naira 1500 kuma ta ke ta hauhawar kamar motar da birkin ta ya tsinke ana gudu a 180 na ma’aunin tuƙin mota. Gamayyar ƙungiyoyin na shugabannin 'yan kasuwar Kano kimanin 30 da suka yi gangami a taron da suka gabatar a ranar Lahadi da ta gabata ƙarƙashin shugabancin shugaban gamayyar ƙungiyoyin 'yan…
Read More
ECOWAS ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa Nijar, Burkina Faso, Mali, Guinea

ECOWAS ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa Nijar, Burkina Faso, Mali, Guinea

ECOWAS ta yanke shawarar ɗage wasu takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Guinea. Ƙungiyar ta cimma wannan matsaya ne a wajen taronta da ta shirya ranar Asabar a Abuja. Sai dai ɗage takunkumin ba na baki ɗaya ba ne, wasu ne daga cikin takunkuman da ECOWAS ɗin ta kafa wa ƙasashen da lamarin ya shafa. Idan ba a manta ba, a watan Janairun da ya gabata Nijar da Mali da Burkina Faso suka sanar da ficewarsu daga ƙungiyar ECOWAS sakamakon takunkuman da aka kafa musu biyo bayan juyin mulkin da ya faru a ƙsashen.
Read More