24
Feb
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta biya Naira miliyan 613 ga ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya daga jihar su 414. Shugaban kwamitin tantancewa kuma babban sakataren ma’aikatar kuɗi ta jihar Muhammad Kabiru Abubakar ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ofishinsa. A cewarsa, kwamitinsa ya karvi bayanai sama da 4000 na waxanda suka amfana. Ya kuma kara da cewa an ɗora wa kwamitin ne domin tabbatar da waɗanda suka yi ritaya daga shekarar 2015 zuwa yau domin su ci gajiyar giratuti. Ya yi alƙawarin yin adalci wajen sauke aikin da aka bai…
