Labarai

Saƙon Kirsimeti: Mu haɗe kai mu yaƙi maƙiya cigaban ƙasa, kiran CDS ga ’yan Nijeriya

Saƙon Kirsimeti: Mu haɗe kai mu yaƙi maƙiya cigaban ƙasa, kiran CDS ga ’yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH An yi kira ga al’ummar Nijerya da su hade kai wajen yaki makiya cikgaban kasa a wannan lokuci na bukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara. Babban Hafsan Tsaron Kasa, Janar Christopher Musa ne ya yi wannan kira a cikin sakon taya murna da ya fitar a ranar Lahadi mai dauke da sa hannun Mukaddashin Daraktan Yada Larabai na rundunar soji, Birgediya Janar Tukur Gusau. “Yayin da muka bi sahun masu bikin Kirsimeti da sabuwar shekara a fadin duniya, ina yabo ga Sojojin Nijeriya da ’yan Nijeriya bisa jajircewarsu. Da fatan alherin da ke tattare da wannan lokaci ya…
Read More
Sarkin Kano ya ƙaddamar da kwamitin bikin shekara 90 da KOFA ta tsara yi a 2025

Sarkin Kano ya ƙaddamar da kwamitin bikin shekara 90 da KOFA ta tsara yi a 2025

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano          Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kaddamar da kwamitin shirye-shiryen bikin cika shekara 90 da kafuwar makarantar firamare ta Kofar Kudu, wace aka kafa a 1935 a gidan Sarkin Kano wanda qungiyar tsofaffun dalibai wato Kofar Kudu Old Pupils Primary School, (KOFA) karkashin shugabancin Kwamared Abubakar Shehu Kwaru ke shirin aiwatarwa da bikin a 2025 idan Allah ya kaimu lafiya. Kamar dai yadda Sarkin Kano ya kaddamar da wannan kwamiti a lokacin taron kungiyar na shekara 50 da dalibai karkashin shugabancin Alhaji Yusuf Aliyu Yakasai,  ya aji na shekarar 1972 wanda…
Read More
Matatar Fatakwal za ta fara aiki bayan shekaru

Matatar Fatakwal za ta fara aiki bayan shekaru

*Tinubu ya bada umarni maido da tsarin ciyar da dalibai Daga MAHDI M. MUHAMMAD Matatar mai fetur ta Fatakwal da ke Jihar Ribas za ta sake fara aiki bisa alqawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na tabbatar da samar da tace kayan a cikin gida a watan Disamba na 2023. Cigaban yana zuwa ne bayan shekaru da yawa da rufe matarar da kuma gyara kayan aikinta. Uku daga cikin matatun mai na Nijeriya a Fatakwal, Warri da Kaduna su na da qarfin tace ganga 445,000 a kowace rana, amma an rufe su tun a shekarar 2019. Sai dai kuma a…
Read More
Za mu hukunta likitocin da ke safarar ƙoda a Nijeriya – Gwamnati

Za mu hukunta likitocin da ke safarar ƙoda a Nijeriya – Gwamnati

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Nijeriya ta bayar da tabbacin daukar mataki kan likitoci da sauran mutanen da ke da hannu a harkar safarar koda. Jami'ar yada labarai ta ma'aikatar lafiya ta kasar, Ms Patricia Deworitshe ce ta bayar da tabbacin cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba a Abuja, babban birnin Nijeriya. A cewar jami'ar, gwamnati ta sanar da kudirinta na ladabtar da duk wanda aka kama da hannu a safarar koda bayan rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa kan yadda ake yin harkar a boye. Ta ce "ma'aikatar ta yi tir da irin wannan…
Read More
Nigeria Air: Majalisa ta gayyaci tsohon Ministan Sufurin Jirage – Sirika

Nigeria Air: Majalisa ta gayyaci tsohon Ministan Sufurin Jirage – Sirika

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin sufurin jiragen sama da ya gayyaci Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, domin ya yi ma ta bayanin halin da kamfanin dakon kaya na kasa, Nigeria Air, ke shirin yi, har zuwa lokacin da zai bar mulki. Ana sa ran tsohon ministan zai bayar da haske a kan batutuwa da dama da suka shafi aikin. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Hon. Tarkighir Dickson ya gabatar a zauren majalisar ranar Alhamis.Da yake gabatar da kudirin, ya ce tsohon ministan a shekarar 2016 ya ba da shawarar…
Read More
Fiye da mutum 50,000 ke zaman jiran shari’a a gidajen kurkukun Nijeriya – Jami’i

Fiye da mutum 50,000 ke zaman jiran shari’a a gidajen kurkukun Nijeriya – Jami’i

 Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An bayyana cewa akwai sama da mutum 50,000 tsare a kurkuku daban-daban cikin kasar nan, wadanda ke zaman tsammanin jiran a yanke masu hukunci a kotuna daban-daban. Wani jami’i ne ya tabbatar da haka, inda ya ce kashi 69 bisa 100 na wadanda ke tsare a gidajen kurkuku, duk jiran a yanke masu hukunci suke yi. Hukumar Kula da Gidajen Kurkukun Nijeriya (NCoS), ta ce akwai mutum 53,836 tsare a gidajen kurkuku daban-daban, wadanda ke zaman jiran a yanke masu hukunci a gidajen kurkuku 253 da ke cikin kasar nan. Wannan kididdiga dai za…
Read More
An dakatar da kansila a Kebbi bisa zargin rashin taɓuka aiki

An dakatar da kansila a Kebbi bisa zargin rashin taɓuka aiki

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Kansiloli bakwai daga cikin 11 da ke akwai a Karamar Hukumar Argungu da ke Jihar Kebbi sun tsige Hon Samaila Muhammad Felande, kansila mai wakiltar Mazabar Felande daga mukaminsa na Shugaban Kansiloli, wato Council Leader, bisa ga zargin rashin tabuka wani abin a-zo-a-gani wajen jagoranacin kansilolin. Kansila mai wakiltar mazabar Tungar Zazzagawa, Hon. Buhari Usman, ne ya bayyana haka jiya a garin Argungu bayan wani zama da suka yi. Ya bayyana cewa, daga cikin korafe-korafensu akwai shirya wani gangamin taro a gidan Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar, Tafidan Kabi, da ke garin…
Read More
Yadda Kotun Ƙoli ta ji ba’asin shari’ar zaɓen gwamnan Kano

Yadda Kotun Ƙoli ta ji ba’asin shari’ar zaɓen gwamnan Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A jiya Alhamis ne Kotun Koli ta jingine ranar yanke hukunci kan qarar da Jam’iyyar NNPP ta shigar ta na neman ta tabbatar da dan nasarar dan takararta, Abba Kabir Yusuf, a matsayin gwamnan Jihar Kano. A watan Satumba ne dai kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Kano ta kori Yusuf a matsayin gwamnan jihar. Daga bisani, NNPP da dan takararta suka kalubalanci hukuncin a Kotun Daukaka Kara. A ranar 17 ga Nuwamba, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin Kotun Kararrakin Zabe, sannan ta kara da cewa Yusuf ba dan Jam’iyyar NNPP ba…
Read More
An kashe wata mata saboda mafarki a Kano

An kashe wata mata saboda mafarki a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An gurfanar da wasu maza su biyar kan zarginsu da yin taron dangi wajen kashe wata mata saboda mafarkin da wata ta ba su labari a Jihar Kano. Kotun Jihar Kano mai lamba 14 da ke zamanta a titin Miller ta gurfanar da su ne kan zargin haɗa baki da kashe matar saboda zarginta da maita. Mai gabatar da ƙara, lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soronɗinki ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake zargin su biyar suka haɗu suka kashe wata mata mai suna Ɗahara Abubakar. Barista Lamido Abba Soronɗinki ya ce a garin…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya sanya hannu kan kasafin 2024

Gwamna Raɗɗa ya sanya hannu kan kasafin 2024

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya sanya hannu a kasafin kuɗi na shekara 2024. Sai da majalisar dokoki ta jihar ta shafe kwanaki talatin da uku tana ta tafka muhawara akai tare da gayyato kwamishinoni da shugabannin ma'aikatu kafin su amince da zartas da kasafin kuɗin. Gwamnan da ya sanya hannu a kasafi kuɗin a gaban babban joji na jiha mai shari'a Musa Danladi da Alƙalin Alƙalai Dr kabir Abubakar. Sauran sun haɗa da 'yan majalisar dokoki na jiha da 'yan majalisar zartaswa ta jiha da kuma manyan jami'an gwamnatin jihar. Gwamna Dikko…
Read More