26
Dec
Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haDuwa a wani makon a shafinku na zamantakewa a jaridarku mai farin jini Blueprint Manhaja. A wannan maudu'i da za mu tattauna a wannan mako, za mu duba yadda ake yawaitar samun samari da 'yammata/zarawa marasa aure a garin nan. Kasashen Hausa cike suke da wadannan matsaloli. Kuma kowa ka tava cikin wadannan matasan sai ya ce ai ya rasa miji ko matar aure ne. Wasu lokutan ma har a kafafen sadarwa ko dandalin sada zumunta na yanar gizo daban-daban za ka ga an ba da cigiyar mutum yana neman matar aure…
