Labarai

Ambaliyar ruwa ta raba mutane 563 da muhallansu a Adamawa

Ambaliyar ruwa ta raba mutane 563 da muhallansu a Adamawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ambaliyar ruwan sama ta raba mutane 563 da ke Unguwan Tana a Ƙaramar Hukumar Yola ta Gabas a jihar Adamawa. Mutanen da iftila’in ya shafa, a yanzu haka sun samu mafaka a makarantar sakandare ta je ka ka dawo ta GDS da ke yankin Limawa-Jimeta, a Yola babban birnin jihar. Shugaban makarantar Musa Hassan Jada ya bayyana cewa, mutanen da abin ya shafa sun tare a ajujuwa bakwai na makarantar. Kazalika, mataimakin gwamnan jihar Kaletapwa George Farauta, ya ziyarci Unguwan Tana domin duba irin varnar da ambaliyar ruwan ta janyo. Bugu da ƙari, George…
Read More
Kotu ta tabbatar da zaɓen Gwamna Idris na Kebbi

Kotu ta tabbatar da zaɓen Gwamna Idris na Kebbi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Jihar Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ofemai Ofem, ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar tana ƙalubalantar nasarar Gwamna Nasir Idris. Da yake yanke hukuncin a gaban lauyoyi da jiga-jigan jam’iyyar APC, tun da farko alƙalin ya yi fatali da zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan jihar Umar Tafida, bayan da ya miƙa takardar shaidar makarantar da ya halarta a matsayin shaida. A game da kura-kuran zaɓe, kotun ta ce kimanin shaidu 17 daga hukumar zaɓe ta INEC sun tabbatar da cewa zaɓen ba shi…
Read More
Taɓarɓarewar Tsaro: Majalisar Dattawa ta gayyaci Ribadu da shugabannin tsaro

Taɓarɓarewar Tsaro: Majalisar Dattawa ta gayyaci Ribadu da shugabannin tsaro

*Kotun soji ta samu Janar Muhammed da laifin karkatar da miliyoyin Dala Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar Dattawan Nijeriya ta ƙuduri aniyar yi wa hafsoshin tsaron ƙasar kiranye, saboda taɓarɓarewar tsaro a ƙasar, musamman Arewacin Nijeriya. Majalisar Dattijai ta ɗauki matakin ne a jiya Alhamis bayan tattaunawa kan batutuwan yin garkuwa da wasu ɗalibai mata guda biyar na Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma dake Jihar Katsina a ranar Laraba bayan da Sanata Yar’Adua mai wakiltar yankin Katsina ta Tsakiya a majalisar ya gabatar da ƙudirin. Waɗanda za a gayyace sun haɗa da; Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Sojin…
Read More
Chicago: Zan dangana idan Kotun Ƙoli ta tsarkake Tinubu – Atiku

Chicago: Zan dangana idan Kotun Ƙoli ta tsarkake Tinubu – Atiku

*Ɗan takarar PDP ya ce ba don kansa yake wa Tinubu tone-tone ba*Siyasarka ta zo ƙarshe – APC ga Atiku*Ba na tsoro domin Buhari ya gama kassara kasuwancina a Nijeriya, inji Atiku Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi iƙirarin cewa, idan har Kotun Ƙolin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu tsarkakke ne shi, duk da satifiket ɗin da shi Atikun ya amso daga Jami’ar Chicago dake Birnin Ilinious, don ƙalubalantar sahihancin zaɓensa a 2023, to zai dangana ya haƙura…
Read More
Tawagar UAE ta gana da Tinubu domin ƙara haɗa hulɗar ƙasashen biyu

Tawagar UAE ta gana da Tinubu domin ƙara haɗa hulɗar ƙasashen biyu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tawagar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta isa Abuja domin kammala tattaunawa kan yiwuwar ɗage takunkumin hana bai wa 'yan Nijeriya bizar shiga ƙasar. Tawagar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wacce ta ƙunshi jami’an jihohi irinsu Alshehhu Rasheed, Teo Teck San, Almannaei Khalid, Alhosani Talal, da Janahi Asma sun isa Nijeriya a ranar Lahadi. Tawagar da ake sa ran za ta gana da shugaba Bola Ahmed za ta kuma tattauna batun fara zirga-zirgar jiragen sama tsakanin ƙasashen biyu. Idan za a iya tunawa, UAE a shekarar 2022, ta janye kamfanoninta na jiragen sama, Emirates da Etihad Airways, daga aiki…
Read More
Mutane takwas sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kebbi

Mutane takwas sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Bayanai daga garin Yawuri da ke Jihar Kebbi sun bayyana cewa aƙalla mutane takwas ne suka rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a garin Yawuri farkon makon nan. Wani jami'in hukumar kula da harkokin ruwa ya bayyana wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, jirgin mai ɗauke da mutane kimanin 30 da ya taso daga Agwara da ke jihar Neja ya ɗauko fasinja daga ƙauyukan Gebbe, Kasabo da kuma Mago maƙare da buhunan abinci kimanin tamanin da kaya da dabbobi daga jihar Neja zuwa Yawuri wajen cin kasuwa inda ya kife. Shugaban ƙaramar…
Read More
Mu taimaki Minista Malagi

Mu taimaki Minista Malagi

Masu hikimar magana su na cewa duk wadatar mutum za a iya taimakon sa, haka duk talaucin mutum zai iya taimakon wani. Shi taimako ya danganta daga mutum zuwa wanda zai ma taimakon wani addu'a ce za a taya masa. Wani kuɗi ne, buƙatar wani kuma abin yi ne, buƙatar duka dai mu lura da yadda sabon minista na ɓangaren labarai Alhni Muhammed Idris Malagi ya zamo mai ayukka da yawa, kai ka ce baya ga minista a ɓangaren labarai da kuma wayar da kai, tamkar shi ne mai magana a madadin shugaban ƙasa Tinubu. Duk wanda ya ke sauraren…
Read More
Majalisar Dattawa ta fara bincike kan kisan ‘yan Nijeriya 250 a Habasha

Majalisar Dattawa ta fara bincike kan kisan ‘yan Nijeriya 250 a Habasha

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattijai ta matsa ƙaimi domin gudanar da bincike kan kashe-kashe da ɗaure ‘yan Nijeriya sama da 250 a ƙasar Habasha. Hakan ya biyo bayan wani ƙudiri mai taken, ‘Akwai buƙatar a gaggauta bincike kan kashe-kashen da aka yi wa ‘yan Nijeriya sama da 250 a ƙasar Habasha ba bisa ƙa’ida ba, wanda shugaban marasa rinjaye, Sanata Simon Mwadkwon, ɗan Jam’iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) mai wakiltar Filato ta Arewa, da Sanata Victor suka ɗauki nauyi. Da yake gabatar da ƙudirin, Mwadkwon ya buƙaci majalisar dattijai da ta umurci kwamitocin ƙasashen waje da su…
Read More
‘Yan Nijeriya na iya neman fasfo ta yanar gizo daga watan Disamba

‘Yan Nijeriya na iya neman fasfo ta yanar gizo daga watan Disamba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce ana ci gaba da sauye-sauye domin sauƙaƙa aikin fasfo tare da yiyuwar 'yan Nijeriya su fara gabatar da aikace-aikacen samum fasfo ɗin ta yanar gizo tun daga watan Disamba. Da yake magana a gidan talabijin na Channels Television a shirin 'Siyasa A Yau' a Laraba, Tunji-Ojo ya bayyana cewa, ɗaya daga cikin sauye-sauyen da ma'aikatar ke aiwatarwa a fannin sarrafa fasfo shi ne kawo ƙarshen tsarin neman fasfo cikin wahala. “Ni da kaina na faɗi haka ga masu samar da ayyukan; Na faɗa yau, na fadi…
Read More
Gwamna Lawal ya karɓi baƙuncin ahalin da ayyukan ‘yan ta’adda suka jefa cikin mawuyacin hali a Zamfara

Gwamna Lawal ya karɓi baƙuncin ahalin da ayyukan ‘yan ta’adda suka jefa cikin mawuyacin hali a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya karɓi baƙuncin matar nan Hauwa'u tare da 'ya'yanta wanda ayyukan 'yan bindiga suka jefa cikin mawuyacin hali a jihar. Cikin wani faifan bidiyon da aka yaɗa kwanan nan, an ga yadda Hauwa'u tare da 'ya'yanta suna cin ciyawa a matsayin abinci don tsira da rayuwarsu. Mai magana da yawun Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya faɗa a ranar Alhamis cewa, halin da matar da 'ya'yanta suka tsinci kansu ya nuna akwai buƙatar gaggawa wajen maganace silar faruwar hakan da kuma taimaka wa rayuwarsu. Ya ƙara da cewa, baƙuncin matar da 'ya'yanta da Gwamnan…
Read More