Labarai

Gwamna Dikko ya ƙaddamar da dakarun tsaron al’umma a Katsina

Gwamna Dikko ya ƙaddamar da dakarun tsaron al’umma a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da Dakarun Tsaron Al'umma na Jihar Katsina (Katsina Community Watch Corps) gami da muhimman kayan aiki domin dawo da tsaro a faɗin jihar. Shafin Katsina Post ya rawaito cewa an gudanar da bikin ƙaddamawar ne a babban filin wasa na Muhammadu Dikko da ke cikin birnin Katsina ranar Talata. Kalika, bayan ƙaddamar da dakarun su 1,500, Gwamnan jihar ya kuma ƙaddamar da motoci masu sulke ƙirar Hilux guda 70 da kuma babura 700 domin yaƙi da ta’addanci a lungu da saƙo na jihar Katsina. Taron ya samu halartar fitattun mutane da shugabannin…
Read More
NiMet ta yi hasashen yiwuwar samun ruwan sama mai ƙarfi a wasu jihohi

NiMet ta yi hasashen yiwuwar samun ruwan sama mai ƙarfi a wasu jihohi

Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta fitar da sanarwa mai ɗauke da hasashen yiwuwar samun ruwan sama mai ƙarfi a jihohi da dama a cikin wannan makon. Ga abin da hasashen NiMet ya nuna kamar haka: Hasashen ranar Talata: Ana sa ran samun ruwan sama mai ƙarfi a wuraren da suka haɗa da jihohin Delta, Bayelsa, Rivers, Imo, Anambra, Akwa lbom, Cross River, Oyo, Ogun, Osun, Ekiti, Kogi, da kuma Ondo. Sannan ana sa ran samun ruwan sama matsaikaici zuwa ƙasa a jihohi da suka haɗa da FCT, Kaduna, Filato, Nasarawa, Kwara, Edo, Abia, sai kuma Taraba. Yayin da…
Read More
NECO ta bayyana lokacin fitar da sakamakon jarrabawar SSCE na 2023

NECO ta bayyana lokacin fitar da sakamakon jarrabawar SSCE na 2023

A wannan Talatar ake sa ran Hukumar Shirya Jarrabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarrabawar da ɗaliban da suka kammala sakandare suka rubuta na 2023. Wannan na zuwa ne bayan shafe dogon lokaci ɗalibai da iyayensu na dakon sakamakon domin ganin sakamakon da aka samu. Sai dai da alama jinkirin da aka samu wajen fitar da sakamakon na haifar da cikas wajen ɗaukar sabbin ɗalibai a jami'o'i da ma sauran manyan makarantu. Kuma hakan ya haifar da ɗar-ɗar ga ɗaliban da ma iyayen nasu. Tun bayan kammala jarrabawar a farkon watan Agustan da ya gabata, NECO ta yi…
Read More
Da sana’ar sayar da soson wanka mu ke samun rufin asiri a Ogun – Alhaji Ya’u

Da sana’ar sayar da soson wanka mu ke samun rufin asiri a Ogun – Alhaji Ya’u

Daga DAUDA USMAN a Legas Wani ɗan kasuwa mai gudanar da harkokin kasuwancin sayar da sosan wanka wanda ake kiransa da suna Kakan a Jihar Ogun, Alhaji Ya'u Samaila, ya bayyna cewa, da wannan sana'ar su ke samun rufin asiri a Ogun. Alhaji Ya'u, wanda ya kasance ɗan asalin ƙaramar hukumar Samaila ne da ke cikin Jihar Kano mazaunin Ogun, kuma shugaban Ƙungiyar Masu Sana'ar Kasuwancin Sosan Wanka Kakan a garin Ibafo ta Ogun ya bayyana cewa, shi da sauran 'yan Kasuwa masu sana'ar kasuwancin sosan kakan a garin Ibafo su na ƙara samun nasarori a wajen gudanar da harkokin…
Read More
Kotu ta yanke hukuncin kisa a kan ɗan sandan da ya kashe Bolanle Raheem a Legas

Kotu ta yanke hukuncin kisa a kan ɗan sandan da ya kashe Bolanle Raheem a Legas

Babbar Kotun Jihar Legas ta yanke wa ɗan sanda, ASP Drambi Vandi, hukuncin kisa bayan da ta same shi da laifin kashe lauyar nan, Mrs Omobolanle Raheem a Legas. A ranar Litinin Kotun mai zamanta a yankin Igbosere a Legas, ta ce dakataccen jami'in zai baƙunci lahira ne ta hanyar rataya. Aƙalin kotun, Ibironke Harrison, ya ce mai gabatar da ƙara, wato Gwamnatin Jihar Legas, ta gabatar wa kotun ƙwararan hujjojin da suka tabbatar da aikata laifin da ake zargin jami'in da shi. “Kotu ta sami wanda ke kare kansa da laifi guda ɗaya, wato kisa. Za a rataye ka…
Read More
Sunday Igboho ya shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe shekara biyu a gidan yarin Jamhuriyar Benin

Sunday Igboho ya shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe shekara biyu a gidan yarin Jamhuriyar Benin

An sako jagoran neman kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, bayan shafe shekara biyu yana tsare a gidan yarin ƙasar Benin. Igboho ya tabbatar da sakin nasa ne a shafinsa na Instagram inda ya wallafa cewa, “Sako ni daga Jamhuriyar Benin." Majiyarmu ta ce Igboho ya yaba wa waɗanda suka taka rawa wajen sako shi da aka yi, da suka haɗa da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da fitaccen marubucin nan, Wole Soyinka da Farfesa Banji Akintoye da Ayo Adebanjo da sauran sarakunan gargajiya. Idan dai ba a manta ba, a ranar 19 ga…
Read More
Gwamnatin Kano ta rufe asibiti mai ma’aikata biyu rak

Gwamnatin Kano ta rufe asibiti mai ma’aikata biyu rak

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani asibiti mai zaman kansa mai suna Choice Clinic, bayan da aka gano ma'aikata biyu rak asibitin ke da su, wato nas ɗaya da mai shara ɗaya. Majiyarmu ta ce wannan na zuwa ne bayan da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar (PHIMA) ta rufe asibitin Reach Clinic kan laifin saɓa dokokin aiki. Da yake jawabi jim kaɗan bayan rufe asibitin, Daraktan hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar (PHIMA), Farfesa Salisu Ibrahim Ahmad, ya ce sun samu asibitin Choice Clinic na zama a gini guda…
Read More
Oyedele ga ‘yan Nijeriya – Gara ma ku yi fatan kar matatun mai su yi aiki a Nijeriya

Oyedele ga ‘yan Nijeriya – Gara ma ku yi fatan kar matatun mai su yi aiki a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Ɗaya daga cikin mataimakan da Shugaba Tinubu ya naɗa, Mista Taiwo Oyedele ya gaya wa 'yan Nijeriya cewa, su yi fatan kar Allah ya sa matatun man fetur su yi aiki a Nijeriya. Shugaban kwamitin shugaban ƙasa na tsare-tsaren kuɗi da saita haraji My MistaTaiwo Oyedele, shi ya isar da wannan gargaɗi ga 'yan Nijeriya. Ya ƙara da cewa, da zarar matatun sun fara aiki, litar man Nijeriya sai ta kere ta ko'ina a duniya tsada. Oyedele ya yi wannan jawabi ne a taron murnar ranar samun 'yancin kan Nijeriya da aka gudanar a ranar Litinin…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe mutum 10 a Zamfara

Bayanai daga Jihar Zamfara sun ce mutum 10 sun mutu sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai kan wasu motoci a hanyar Magami zuwa Gusau a ranar Asabar. An ce yayin harin, mahara sun ƙona motoci guda uku kana sun yi awon gaba da wasu fasinjoji da dama. Manhaja ta kalato cewar harin ya auku ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana a yankin Dogon Tsauni a daidai lokacin da motocin ke hanyarsu ta zuwa Gusau daga Magami. Jaridar Premium Times ta ce an kwashi waɗanda suka ji rauni yayin harin zuwa babbar asibitin…
Read More
Kotun Ƙoli ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncin shari’ar belin Kanu

Kotun Ƙoli ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncin shari’ar belin Kanu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A jiya Alhamis ne Kotun Ƙolin Nijeriya ta tsayar da ranar 15 ga watan Disamba domin yanke hukunci kan ƙarar da Gwamnatin Tarayya ta shigar a kan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke tuhumar da ake wa shugaban ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, tare da bayar da umarnin a sake shi. A zaman sauraron ƙarar na jiya Alhamis, wasu mutane biyar na Kotun Ƙoli ƙarƙashin jagorancin Kudirat Kekere-Ekun sun dage sauraron ƙarar don yanke hukunci bayan ta ɗauki taƙaitaccen bayani daga lauyoyi daga ɓangarorin. A yayin da take ci…
Read More