NECO ta bayyana lokacin fitar da sakamakon jarrabawar SSCE na 2023

A wannan Talatar ake sa ran Hukumar Shirya Jarrabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarrabawar da ɗaliban da suka kammala sakandare suka rubuta na 2023.

Wannan na zuwa ne bayan shafe dogon lokaci ɗalibai da iyayensu na dakon sakamakon domin ganin sakamakon da aka samu.

Sai dai da alama jinkirin da aka samu wajen fitar da sakamakon na haifar da cikas wajen ɗaukar sabbin ɗalibai a jami’o’i da ma sauran manyan makarantu.

Kuma hakan ya haifar da ɗar-ɗar ga ɗaliban da ma iyayen nasu.

Tun bayan kammala jarrabawar a farkon watan Agustan da ya gabata, NECO ta yi alƙawarin fitar da sakamakon a tsakanin kwanaki 45, alƙawarin da hukumar ta kasa cikawa.

Kafin wannan lokaci, an yayata cewar NECO za ta fitar da sakamakon a Satumban da ya gabata, amma hakan bai tabbata ba. Sannan aka kuma cewa a ranar 5 ga watan Oktoba za a saki samakon, nan ma aka ji shiru.

Sai dai majiyarmu ta ce akwai tabbacin NECO za ta fitar da sakamon a wannan Talatar wanda hakan zai kawo ƙarshen zaman jira da ɗalibai da iyaye ke yi.