NiMet ta yi hasashen yiwuwar samun ruwan sama mai ƙarfi a wasu jihohi

Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta fitar da sanarwa mai ɗauke da hasashen yiwuwar samun ruwan sama mai ƙarfi a jihohi da dama a cikin wannan makon.

Ga abin da hasashen NiMet ya nuna kamar haka:

Hasashen ranar Talata:

Ana sa ran samun ruwan sama mai ƙarfi a wuraren da suka haɗa da jihohin Delta, Bayelsa, Rivers, Imo, Anambra, Akwa lbom, Cross River, Oyo, Ogun, Osun, Ekiti, Kogi, da kuma Ondo.

Sannan ana sa ran samun ruwan sama matsaikaici zuwa ƙasa a jihohi da suka haɗa da FCT, Kaduna, Filato, Nasarawa, Kwara, Edo, Abia, sai kuma Taraba.

Yayin da ake sa ran samun yanayi mai zafi a jihohi kamar Katsina, Kano da Borno.

Hasashen ranar Laraba:

Ana sa ran samun matsakaicin ruwan sama a sassan jihohin Kaduna, Nasarawa, FCT, Filato, Taraba, Oyo, Ekiti, Osun, Ondo, Kwara, Edo, Kogi, Anambra, Imo, Abia, Enugu, Ebonyi, Akwa lbom, da kuma Cross River.

Ana sa ran samun ruwan sama tsaka-tsaki zuwa ƙasa a jihohin Ogun, Lagos, Delta, Bayelsa, Rivers, Benue, Gombe, da kuma Adamawa.

Yayin da ake sa ran fama da yanayi mai zafi a wasu jihohin Arewa irin su Katsina, Kano, Yobe, Jigawa, Bauchi da Borno.

Hasashen ranar Alhamis:

Ana sa ran samun matsakaicin ruwan sama mai ƙarfi a sassan jihohin Ogun, Lagos, Osun, Ekiti, FCT, Kaduna, Neja, Nasarawa, Filato, Delta, Bayelsa, Rivers, Anambra, Imo, Abia, Akwa Ibom, Enugu, Ebonyi, Cross River, Taraba da Adamawa.

Sannan matsakaicin ruwa zuwa mara yawa a sassan jihohin Oyo, Kogi, Bauchi, Borno da kuma Gombe.

NiMet ta yi gargaɗin a wannan lokaci akwai yiwuwar fuskantar ambaliya da zezayar ƙasa da tsawa da kuma iska mai ƙarfi.