Shugabancin Bayelsa: Kotu ta soke cancantar shiga takarar ɗan takarar APC, Sylva

Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja, ta soke cancantar shiga takara ta ɗan takarar jam’iyyar APC, Cif Timipre Sylva, a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa mai zuwa.

A ranar Litinin kotun a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Donatus Okorowo, ta yanke wannan hukuncin.

Ya zuwa ranar 11 ga watan Nuwamban 2023 ne ake sa ran gudanar da zaɓen gwamna a jihar ta Bayelsa.

Alƙalin ya ce tun da an taɓa rantsar da Sylva sau biyu a matsayin gwamnan jihar kuma ya yi mulki na tsawon shekara biyar, sake shiga takarar gwamna a jihar hakan ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.

Ya ƙara da cewa, Sylva bai cancanci tsayawa takara ba a zaɓe mai zuwa a jihar, idan kuwa ya shiga ya kuma ci zaɓe hakan na nufin zai shafe sama da shekara 8 a ofis a matsayin gwamnan jihar wanda hakan kuwa ya saɓa wa doka.

Okorowo ya ci gaba da cewa, doka ta haramta zaɓen wani a matsayin gwamna sama da sau biyu, kuma duka jam’iyyun da shari’ar ta shafa sun yarda cewa sau biyu ana zaɓen Sylva a matsayin gwamnan jihar.

Ya ce muddin aka ƙyale Sylva ya tsaya takara a zaɓe mai zuwa, hakan na nufin mutum na iya shiga takara na duk adadin da ya ga dama ke nan.