Labarai

HOTUNA: Yadda CP Gumel da tawagarsa suka yi rangadi yayin zaɓen cike giɓi a Kano

HOTUNA: Yadda CP Gumel da tawagarsa suka yi rangadi yayin zaɓen cike giɓi a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano mai kula da aikin zaɓe, CP Usaini Mohammed Gumel, tare da sauran haɗakar jami'an tsaro da ke jihar Kano yayin da tawagarsu ke rangadin duba wasu ƙananan hukumomi dan tabbatar da an samu kwanciyar hankali yayin gudanar da zaɓen cike giɓi da ya guda ranar Asaba. A cikin tawagar akwai Shugaban DSS, Sibul Difens, Hukukar Kiyaye Haɗurra, Sojoji da sauran hukumomin tsaro. Wuraren da tawagar ta ziyarta sun haɗar da Zangon Marikita a Rimin Kebe a ƙaramar hukumar Ungoggo, sai Kwaciri Gabas Alasawa da ke ƙaramar hukumar Fagge da sauransu.…
Read More
Jami’an DSS sun cafke Malam Baffa Hotoro a Kaduna

Jami’an DSS sun cafke Malam Baffa Hotoro a Kaduna

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun yi nasar cafke Malamin addinin Musuluncin nan, Malam Baffa Hotoro, da ake zargi da yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad S.A.W. An cafke Malam Baffa Hotoro ne a garin Kaduna a ranar Asabar kamar yadda rahotanni suqka tabbatar. A 'yan kwanakin nan dai malamin na wasu wa'azuzzuka tare da yin kalamai a kan Annabi SAW da ake kallon za su iya tayar da tarzoma a jihar Kano.
Read More
An kashe ɓarawon akwatin zaɓe a Kebbi

An kashe ɓarawon akwatin zaɓe a Kebbi

Sojoji sun harbe wani da ake zargi da yunƙurin sace akwatin zaɓe har lahira a rumfar zaɓen Bajida 001 cikin Ƙaramar Hukumar Fakai a Jihar Kebbi. Bayanai daga yankin sun ce, an harbe matashin ne a lokacin da yake ƙoƙarin ƙwace akwatin zaɓe daga hannun jami'an zaɓe yayin zaɓen cike giɓi da INEC ta shirya a ranar Asabar. An ce ɓata-garin ya yi basajar shi jami'in tsaro ne domin samun damar aikata mummunan nufinsa. Haka nan, an yi zargin ya yi yunƙurin ƙwace bindigar wani soja a rumfar zaɓen kafin daga bisani aka alburshe shi har lahira. A cewar ganau,…
Read More
Kano: ‘Yan daba sun kai hari rumfar zaɓe a Kurna

Kano: ‘Yan daba sun kai hari rumfar zaɓe a Kurna

'Yan daba sun kai hari rumfar zaɓe mai lamba 030 cikin Gundumar Alasawa Kwaciri, Kurna Gabas a yankin Ƙaramar Hukumar Fagge, Jihar Kano. Bayanai sun ce sun kai harin ne ɗauke da makamai tare da tarwatsa masu zaɓe inda kowa ya tsere neman mafaka. An yi sa'a 'yan sanda a yankin sun yi aikinsu wajen kwantar da tarzomar inda suka kora 'yan dabar da kuma bai wa jama'a da ma jami'an zaɓe kariya kana aka ci gaba da zaɓe yadda aka tsara. Sai dai babu wanda ya jikkata sakamakon harin. A ranar Asabar Hukumar Zaɓe, INEC, ta gudanar da zaɓen…
Read More
Mabiya Shi’a sun gudanar da jerin-gwano kan tunawa da ranar Ƙudus ta duniya

Mabiya Shi’a sun gudanar da jerin-gwano kan tunawa da ranar Ƙudus ta duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Juma'a ne ’yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky, waɗanda aka fi sani da mabiya Shi'a a Nijeriya suka gudanar da jerin-gwano don tunawa da ranar Ƙudus a Jihar Kaduna. Ana yin jerin-gwanon duk shekara-shekara ne na goyon bayan Falasɗinawa da ake gudanarwa a ranar Juma'ar ƙarshe ta watan Ramadan don nuna goyon baya ga Falasɗinawa da adawa da Isra'ila da yahudawan sahyoniya. Ana kuma gudanar da ranar Qudus a wasu ƙasashe da dama musamman a ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashen Musulmi, inda ake gudanar da zanga-zangar nuna adawa da mamayar da Isra'ila…
Read More
APC ta lashe zaɓen Sanatan Kudancin Yobe

APC ta lashe zaɓen Sanatan Kudancin Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Babban jami'in hukumar INEC, Dr. Abacha Melemi na Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gashua (FUGA), shi ne ya jagoranci zaɓen 2023 a lokacin da yake sanar da sakamakon a yau a garin Potiskum. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta INEC ta ayyana Sanata Ibrahim Mohammed Bomai a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wanda ya gudana yau Asabar, a Yobe ta kudu. Sanata Bomai na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 69,596 inda ya doke abokin takararsa na jam'iyyar PDP, Hon. Halilu Mazagane, mai ƙuri'u 68,885. Sauran sun haɗa da Hon. Yerima Adamu na ADC 652, Hon. Jauro…
Read More
2023: Tinubu ya shiga jerin mutane 100 mafi tasiri a duniya

2023: Tinubu ya shiga jerin mutane 100 mafi tasiri a duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓen Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya shiga cikin jerin mutane 100 da suka fi tasiri a mujallar Time Magazine ta 2023. A duk shekara-shekara Mujallar Time na fitar da jerin mutane 100 mafi tasiri da suke bada gudunmuwa a duniya, ba tare da la'akari da sakamakon ayyukansu ba. Jerin sunayen mutanen 2023 da mujallar ta fitar jiya Alhamis, sun kasu ne zuwa ɓangarori kamar haka: Jagorori, shugabanni, masu fasaha, masu ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma ginshiƙai. Tinubu, wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a Nijeriya a ranar 25 ga watan Fabrairu, an…
Read More
An kori ’yan sandan da suka harba harsashi a iska lokacin rakiyar Mawaƙi Rarara

An kori ’yan sandan da suka harba harsashi a iska lokacin rakiyar Mawaƙi Rarara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta kori wasu jami’ai uku da suke rakiya da gadin fitaccen mawaƙin Kano nan, Alhaji Dauda Kahutu Rarara, daga bakin aiki bisa samun su da laifin harbi ba bisa ƙa'ida ba, cin zarafin mutane, rashin ɗa’a, da almubazzaranci da harsashi. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi, jami'an uku, Sufeta Dahiru Shuaibu, Sajan Abdullahi Badamasi, da Sajan Isah Danladi sub kasance tare da Rarara akan aikin rakiya. “A yayin da suke gudanar da aikinsu a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023 a ƙauyen Kahutu da ke Jihar Katsina, jami’an…
Read More
Abba Kyari: Abokin harƙallar Hushpuppi, Woodberry ya amsa laifin zamba

Abba Kyari: Abokin harƙallar Hushpuppi, Woodberry ya amsa laifin zamba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shahararren ɗan damfara ta yanar gizo kuma amini ga Hushpuppi, Olalekan Jacob Ponle, wanda aka fi sani da ‘Woodberry’, kuma ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da aikata almundahanar kuɗi tare da gawurtaccen ɗan sandan Nijeriyan nan, ACP Abba Kyari, a Amurka, ya amsa laifin damfarar mutane ta wayar tarho, sannan ya kuma amince ya biya Naira biliyan 3.6 (dala miliyan 8) tare da miƙa motoci da agogonni ga gwamnatin ƙasar waje. Woodberry, sanannen abokin ɗan damfaran yanar gizo ne da ake tsare da shi yanzu, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, a kwanan…
Read More
Abba Gida-Gida ya shawarci shugabanin ƙananan hukumomin da za a gudanar da zaɓen cike giɓi a yankinsu

Abba Gida-Gida ya shawarci shugabanin ƙananan hukumomin da za a gudanar da zaɓen cike giɓi a yankinsu

Daga RABI'U SANUSI a Kano Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya sake bai wa shugabannin ƙananan hukumomin jihar kano 44 da sauran manyan ma’aikatansu shawarar kauce wa kuskuren yin amfani da su wajen ɗibar kuɗaɗen ƙananan hukumomin kan zaɓen da za a sake a wasu yankuna a jihar. Wannan batun na ƙunshe ne a wata sanarwa da Kakakin sabon Gwamnan, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ga manema labarai ranar Alhamis. Sanarwar ta ce, Gwamnan mai jiran gado na da cikakkiyar masaniyar cewa gwamnati mai barin gado tana shirin fitar da kuɗaɗe da…
Read More