Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Sarkin Dutse ya riga mu gidan gaskiya

Da Ɗumi-ɗumi: Sarkin Dutse ya riga mu gidan gaskiya

Allah ya yi wa Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Dr. Nuhu Muhammad Sunusi CON, rasuwa. Kwamishinan Ayyuka na Musamman a Jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara ne ya tabbatar da rasuwar sarkin. Sarkin ya rasu ne a Abuja bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya kuma ya rasu yana da shekara 79. Sakatare na musamman ga marigayin, Wada Alhaji Dutse ya tabbatar wa BBC cewa ana sa ran yin jana’izar sarkin ne a ranar Laraba a Dutse An haife marigayin a shekarar 1945 a ƙauyen Yargaba da ke Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Read More
Bankuna za su ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira ko bayan ƙarewar wa’adin da ya ƙayyade – Emefiele

Bankuna za su ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira ko bayan ƙarewar wa’adin da ya ƙayyade – Emefiele

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewa bankuna za su ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira bayan ƙarewa wa’adin da bankin ya ƙayyade. Kwanan nan CBN ya tsawaita wa’adin ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira da kwana 10 biyo bayan ƙorafe-ƙorafen ‘yan ƙasa. Da yake jawabi a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan sha’anin sabbib takardun Naira, Emefiele ya ce bankuna za su ci gaba da karɓar tsoffin takardun N1,000 da N500 da kuma N200 bayan ƙarewar wa’adin da aka tsayar ɗin. Ya ce bisa la’akari da Sashe na 20 da ƙaramin sashe…
Read More
Emefiele ya bayyana gaban Kwamitin Majalisa

Emefiele ya bayyana gaban Kwamitin Majalisa

A wannan Talatar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai mai bincike kan batun ƙarancin sabbin takardun Naira. Kwamitin ya gayyaci Emefiele ne domin jin dalilin da ya sa ake fuskatantar ƙarancin sabbin takardun na Naira a faɗin ƙasa. Lamarin da ya jefa 'yan ƙasa cikin wani mawuyacin hali. Ƙarin bayani na nan tafe…
Read More
Diezani ta kama hanyar ƙwato kadarorinta

Diezani ta kama hanyar ƙwato kadarorinta

Daga WAKILINMU Tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, ta kama hanyar maido da kadarorinta da gwamnati ta ƙwace Ta yi hakan ne ta hanyar shigar da ƙara inda ta buƙaci wata Babbar Kotun Tarayya da ta janye umarnin da ta bai wa Hukumar Yaƙi da Rashawa (EFCC) na ƙwace mata kadarorinta. Ta shigar da buƙatar ce tana mai neman Kotun ta dakatar da EFCC daga sayar da kadarorin da ta ƙwace mata. “An yaudari kotunan ne wajen ba da umarnin kwace kadarorinta ta hanyar danniya ko kuma rashin bayyana gaskiyar abin ga duniya,” in ji ta. Kamfanin Dillancin Labarai…
Read More
Buhari ya ƙaddamar da tashar dakon kaya ta tsandauri a Kano

Buhari ya ƙaddamar da tashar dakon kaya ta tsandauri a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da tashar dakon kaya ta tsandauri wacce aka fi sani da Dala 'Inland Dry Port' a unguwar Zawaciki, Jihar Kano. Shugaba Buhari ya isa wajen ne da misalin ƙarfe 10:32 na safiyar Litinin tare da rakiyar wasu daga cikin ministocinsa. Shugaban ya samu tarbar Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da Ministan Sufuri, Jaji Sambo da Manajan Daraktan tashar ta Dala Inland, Ahmad Rabiu da kuma shugaban tashar Alhaji Abubakar Sahabu. Sauran manyan baki da su ka halarci taron sun hada da Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Jiragen…
Read More
Ko Kanawa sun yi lale da ziyarar Buhari?

Ko Kanawa sun yi lale da ziyarar Buhari?

Daga BASHIR ISAH A ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyar aiki na kwana biyu a Jihar Kano domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Jihar ya aiwatar. Sai dai, da alama Kanawa ba su yi ɗaukin ziyarar Buharin ba saɓanin abin da aka saba gani a baya. Kafin ziyarar tasa, an abato Gwamnan Jihar, Abdullahi Ganduje, ya ce, ya nemi Shugaba Buhari ya ɗage ziyarar da ya shirya yi a Kano sakamakon jama'a na cikin mawuyacin hali saboda canjin kuɗi da aka yi. Rahotani, hotuna da ma bidiyoyi sun nuna yadda a wasu titunan jihar galibi yara kaɗai…
Read More
Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya dawo aiki

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya dawo aiki

Daga WAKILINMU Daraktan ayyuka na Hukumar Jiragen Ƙasa ta Ƙasa (NRC), Niyi Alli ne ya sanar da hakan ranar Litinin. Sanarwar da ya fitar ta nuna tsarin lokutan da jirgin zai riƙa zirga-zirgar jagilar fansinjoji. Sanarwar ta ce, “Ranar Talata, 31 ga Janairun 2023 jirgin zai kama aiki bisa tsari kamar haka: KA2 zai bar Rigasa da ƙarfe 0700 AK1 zai bar Idu da ƙarfe 10.00 KA4 zai bar Rigasa da ƙarfe 13.00 AK3 zai bar Idu da ƙarfe 16.00. “Sai dai a ranar Laraba, KA2 zai bar Rigasa da ƙarfe 0700 yayin da AK 3 zai bar Idu da…
Read More
Tsoffin takardun Naira: Majalisa ba ta aminta da ƙarin wa’adin da CBN ya yi ba

Tsoffin takardun Naira: Majalisa ba ta aminta da ƙarin wa’adin da CBN ya yi ba

Daga WAKILINMU Majalisar Wakilai ta ce ba ta aminta da tsawaita wa’adin amfani da tsohuwar Naira da ƙarin kwanaki 10 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi ba. Kwamitin Majalisar mai ruwa da tsaki kan sha’anin sauya fasalin wasu takardun Naira, ya ce dole CBN ya yi abin da ya kamata kamar yadda yake ƙunshe a sassa na 20, 3, 4 da kuma 5 na Dokar Babban Bankin Ƙasar. A cewar Kwamitin, “Tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira da kwana 10 ba shi ne mafita ba. “A matsayinmu na Kwamitin Majalisa ba za mu amince da wani abu sabanin…
Read More
Gwamna Tambuwal ya yaba wa Shugaba Buhari bisa kawo ƙarshen matsalar tsaro

Gwamna Tambuwal ya yaba wa Shugaba Buhari bisa kawo ƙarshen matsalar tsaro

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yaba wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa ƙoƙarinsa na haɗa guiwa da jihohin ƙasar nan domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan. Gwamna Tambuwal, wanda shine shugaban dandalin gwamnonin ƙasar nan, haka ma ya jinjina wa rundunar sojin ƙasar nan, bisa haɗa guiwa da gwamnonin jihohin ƙasar nan domin yaƙi da wannan matsalar. Tambuwal ya bayyana hakan ne dai lokacin da ya karvi baƙuncin manyan jami’an soji mahalarta kwas na 45 na kwalejin soji dake Jaji Kaduna suka kai masa ziyarar godiya na zaɓar Sakkwato domin gabatar da lamuransu.…
Read More
Ganduje ya buƙaci Buhari ya ɗage ziyarar Kano saboda matsin da canjin kuɗi ya haifar

Ganduje ya buƙaci Buhari ya ɗage ziyarar Kano saboda matsin da canjin kuɗi ya haifar

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar cewa ya aike wa Fadar Shugaban wasiƙar neman ɗage ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya kaiwa jihar. Ganduje ya ce ya yi hakan ne saboda matsin da jihar ta faɗa sakamako wa’adin daina amfani da tsoffin takardun Naira da CBN ya ƙayyade. Ya ƙara da cewa, batu tsaro ma na daga cikin dalilan da suka sanya ya buqaci ɗage ziyarar ta Buhari zuwa jihar. Gunduje ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawarsu tare da malamai da ‘yan majalisa da shugabannin siyasa da kuma ’yan kasuwar jihar a Fadar Gwamnatin…
Read More