Labarai

Kotu ta yanke wa wasu tsoffin jami’an SARS hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yanke wa wasu tsoffin jami’an SARS hukuncin kisa ta hanyar rataya

Daga BASHIR ISAH Babban Kotu mai zamanta a Fatakwal ta yanke wa wasu tsoffin jami'an Runduna ta Musamman Mai Yaƙi da Fashi da Makami (SARS) su biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya. Kotu ta yanke musu hukuncin ne bayan da ta kama su da laifin aikata kisa. Idan ba a manta ba, a baya an gurfanar da jami'an SARS biyar da suka haɗa da ASP Samuel Chigbu, Shedrack Ibibo, Magus Awuri, Ogoligo da kuma Olisa Emeka kan kisan wani Michael Akor da Michael Igwe a lokacin da suke tsare da su bisa zargin satar katin waya a yankin Ƙaramar Hukumar…
Read More
Babu wanda ya ƙara farashin man fetur a Nijeriya – NNPC

Babu wanda ya ƙara farashin man fetur a Nijeriya – NNPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban kamfanin mai na NNPCL Malam Mele Kyari ya ce babu wanda ya ƙara farashin mai a Nijeriya. Shugaban ya musanta iƙirarin da wasu ƙungiyoyin masu dakon mai suka yi a baya na cewa an qara farashi. Mele ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a ranar Talata kan matsalar ƙarancin mai da ake fama da ita a Nijeriya. Cikin matsalolin da aka ambato da ake ganin su suke kawo tarnaƙi ga man sun haɗa da ɓangaren jigilar man da kuma ɓangaren farashin da aka gaza samun…
Read More
Kotun Musulunci a Kano ta raba auren Asiya Ganduje da maigidanta

Kotun Musulunci a Kano ta raba auren Asiya Ganduje da maigidanta

Daga RABIU SANUSI a Kano Asiya Abdullahi Umar Ganduje wadda ta kasance 'yar Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta garzaya kotu ta hannun lauyanta, inda take neman kotun ta kawo ƙarshen auren dake tsakaninta da mijinta, Inuwa Uba, inda ta bayyana cewar za ta mayar masa da sadakin da ya ba ta Naira dubu hamsin. Da yake yanke hukuncin, Mai Shari'a Malam Abdullahi Halliru, ya ce hujjojin da aka gabatar a zaman shari'ar sun tabbatar da cewar mai ƙarar ta karɓi Naira dubu hamsin. Sai dai a nasa ɓangaren, lauyan wanda ake ƙara, Umar I Umar, ya yi…
Read More
Babu mahalukin da nake tsoro, cewar El-Rufai ga manyan Fadar Shugaban Ƙasa

Babu mahalukin da nake tsoro, cewar El-Rufai ga manyan Fadar Shugaban Ƙasa

Daga WAKILINMU Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya kalubalancin ’yan Fadar Shugaban Ƙasa da yake zargi da zagon-ƙasa ga takarar Bola Tinubu a zaɓen Shugaban Ƙasa mai zuwa. Tun a ranar Laraba El-Rufai ya fara tayar da ƙura da zargin cewa akwai jami’an Fadar Shugaban Ƙasa da ke neman yi wa takarar Tinubu ƙafar ungulu. A wata hirarsa da BBC Hausa, an ji shi yana cewa, “Na rantse babu mahaluƙin da nake tsoro a duk faɗin ƙasar nan. “Don ana ganin girman mutum ba tsoronsa ake ji ba; amma idan muna girmama mutum sannan yana nuna shi ba babba…
Read More
Bincike: Majalisa ta zargi Malami da yi mata katsalandan

Bincike: Majalisa ta zargi Malami da yi mata katsalandan

Daga BASHIR ISAH Kwamitin Majalisar Wakilai ya zargi Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami da jami'an hukumar Interpol kan yi masa katsalandan a binciken da yake gudanarwa. Kwamitin mai bincike kan badaƙalar satar ɗanyen mai tun daga 2014 zuwa yau, ya ce bai ga dalilin da zai sa jami'an Interpol a bisa buƙatar Ma'aikatar Shari'a suka yi wa wanda ya yi fallasa tambayoyi bayan da Majalisar ta fara gudanar da bincikenta ba. Kwamitin na bincike a kan zargin da aka kwarmata na sayar wa Chana ɗanyen mai ganga miliyan 48 mallakar Najeriya ta haramtacciyar hanya a 2015 wanda kuɗin ya…
Read More
Akwai ’yan adawar Tinubu a fadar shugaban ƙasa, inji El-Rufa’i

Akwai ’yan adawar Tinubu a fadar shugaban ƙasa, inji El-Rufa’i

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zargin cewa akwai masu ƙin ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu a Fadar Aso Rock da su ke ƙoƙarin ganin sun kai shi ƙasa a zaɓe. Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, a cikin shirinsu na Sunrise Daily da safiyar Laraba. El-Rufa’i ya ce, mutanen, waɗanda bai bayyana sunansu ba, sun fusata ne tun lokacin da aka kayar da ɗan takararsu a zaɓen fidda-gwani na APC. Ya kuma ce mutanen na fakewa da buƙatar ganin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi…
Read More
An damƙe matasan da suka yi garkuwa da yara a Kano

An damƙe matasan da suka yi garkuwa da yara a Kano

Daga RABIU SANUSI, Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta yi nasarar damƙe Nura Auwal da abokinsa Abubakar Lawal bisa zargin garkuwa da wasu yara ƙanana. Sanarwar da Rundunar ta fitar ta bakin mai magana da yawunta, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ta ce iyayen yaran da ke zaune a Unguwar Bachirawa cikin Ƙaramar Hukumar Ungoggo a jihar, sun kai rahoton ɓacewar 'ya'yan nasu ofishin 'yan sanda na yankin. Ta ce masu garkuwar sun tura wa da iyayen rubutacciyar takarda ɗauke da lambar sunan asusun banki da lambar waya don tattauna kuɗin fansa Naira miliyan biyu da suka nema kan kowane…
Read More
Allah Ya yi wa Farfesa Ibrahim Umar rasuwa

Allah Ya yi wa Farfesa Ibrahim Umar rasuwa

Daga WAKILINMU Allah ya yi wa tosohon mataimakin shugaban Jami'ar Bayero da ke Kano, Farfesa Ibrahim Umar rasuwa. Majiya daga ahalin marigayin ce ta tabbatar da rasuwar ga jaridar Daily Nigeria, inda ta ce ya rasu ne ranar Litinin a Kano. Marigayin wanda shi ne malami na farko da ya fara koyar da darasin 'Physics' a BUK a shekarar 1976, ya zama mataimakin shugaban jami'ar ne daga 1979 zuwa 1986. Kazalika, ya riƙe Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, babban birnin Jihar Neja. A zamaninsa an samu cigaba mai ma'ana wajen yi wa BUK gine-gine da dama. Da shi…
Read More