Labarai

Tinubu ya naɗa Kansila Muslihu Yusuf na Kano a kwamitin yaƙin neman zaɓensa

Tinubu ya naɗa Kansila Muslihu Yusuf na Kano a kwamitin yaƙin neman zaɓensa

Daga WAKILINMU A karon farko, Jam'iyyar APC ta naɗa kansiloli a cikin Babban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa don zaɓen 2023. A makon da ya gabata ne Daraktan Ofishi na musamman mai kula da ƙananan hukumomi na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa wa Sanata Bola Tinubu, wato Hon. Kolade Alabi David, ya naɗa Kansilan mazaɓar Gurungawa na Ƙaramar Hukumar Kumbotso da ke Jihar Kano kuma jagoran kansilolin APC na ƙasa, Hon. Muslihu Yusuf Ali, a matsayin Mataimakin Kodineta na Ƙasa (na shiyyar Arewa) don tabbatar da nasarar APC a mazaɓu da rumfunan zaɓe. Waɗanda aka naɗa…
Read More
Zaɓen 2023: Zulum ya bai wa makarantu Borno hutun kwana 8

Zaɓen 2023: Zulum ya bai wa makarantu Borno hutun kwana 8

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Borno ta ba da sanarwar bai wa makarantun jihar hutun kwana takwas albarkacin zaɓe mai zuwa. Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin haka ne domin bai wa ɗalibai damar sauke nauyin da ya rataya a kansu lokacin zaɓe. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Ma'aikatar Ilimi ta fitar ta hannun Daraktan hukumar kula da makarantun jihar, Mustapha Bukar Umara, a madadin Kwamishin Ilimi na jihar. Sanarwar ta nuna hutun zai kankama ne daga ranar Alhamis, 23 ga Fabrairu zuwa Laraba, 1 Maris, 2023, don zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan Majalisar Tarayya. Sai…
Read More
Tinubu ya yi ta’aziyyar kisan ‘yan Tijjaniyya a Burkina Faso

Tinubu ya yi ta’aziyyar kisan ‘yan Tijjaniyya a Burkina Faso

Daga WAKILINMU Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC, Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyya ga shugannin ɗarikar Tijjaniyya da kuma iyalan mabiya ɗariƙar su 19 da aka kashe a ƙasar Burkina Faso. Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutanen ne 'yan Nijeriya a ranar Laraba a kan hanyar su ta zuwa ƙasar Senegal domin ziyara. A wata sanarwa da mai taimakawa Asiwaju Tinubu a kan yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya sanyawa hannu, ɗan takarar shugaban ƙasar ya nuna baƙin cikin sa kan abinda ya faru. "Wannan abin baƙin ciki ne a ce mutane basu ji ba…
Read More
Ba ka da ɗa’a : Bafarawa ya mai da martani ga El-Rufa’i kan maganar dattawan Arewa

Ba ka da ɗa’a : Bafarawa ya mai da martani ga El-Rufa’i kan maganar dattawan Arewa

Daga AMINA YUSUF ALI Ɗaya daga cikin Dattawan Arewa, kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto a jam'iyyar PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana cewa, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i sam ba shi da ɗa'a ko sanin ya kamata. A cewar Bafarawa, a yayin da yake mayar da martani ga wata tattaunawa da El-Rufa’i ya yi da sashen Hausa na kafar yaɗa labarai ta BBC, inda shi El-Rufa'in ya bayyana dattaijan Arewa a matsayin akwai-ya-babu wato huhulahu waɗanda ba za su iya tabuka komai a zaɓe ba. A cewar sa, El-Rufa'i ƙaramin alhaki ne mai tunani irin na son zuciya. A…
Read More
Buhari da Emefiele na kan gaba a maƙiyan takarar Tinubu, inji Jaafar Jaafar

Buhari da Emefiele na kan gaba a maƙiyan takarar Tinubu, inji Jaafar Jaafar

Daga BASHIR ISAH Ɗan jarida, Jaafar Jaafar, mawallafin jaridar Daily Nigerian ta intanet, ya ce akwai haɗin baki game da matakin sauya fasalin wasu takardun Naira da Babban Bankin Nijeriya ya ɗauka. Ya ce an ɗauki matakin ne don hana ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar (APC), Bola Ahmed Tinubu, cika burinsa. Idan za a iya tunawa, kwanan nan aka jiyo Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya faɗa a hirar da tashar Channels TV ta yi da shi cewa, akwai wasu maƙiya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke ƙoƙarin ganin sun kai Tinubu ƙasa game da zaɓen 2023. A martanin da…
Read More
Rushewar gini: Minista ya sa a kamo masu ruwa da tsaki

Rushewar gini: Minista ya sa a kamo masu ruwa da tsaki

Daga BASHIR ISAH Ministan Birnin Tarayya, Malam Muhammad Bello, ya bai wa hukumomin tsaro umarni a kan su tsare jami'an Hukumar Gidaje ta Tarayya da injiniyan da ginin benen Abuja da ya rushe yake hannunsa. Kodinetan Hukumar Buƙansa Abuja, Umar Shuaibu, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Asabar. Ministan ya sa a tsare jami'an da ke da ruwa da tsaki wajen ba da izinin gina ginin da ya rushe da kuma injiniyan da ke aikin. Shuaibu ya ce ginin wanda ya rushe a yankin Gwarinpa kwana biyu da suka wauce, mutum 24 suka maƙale yayin da uku…
Read More
Ƙarancin sabbin kuɗi: Zulum ya yi barazanar ƙwace takardar mallakar bankuna a Borno

Ƙarancin sabbin kuɗi: Zulum ya yi barazanar ƙwace takardar mallakar bankuna a Borno

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Maiduguri Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya gargaɗi bankuna a jihar kan su bayar da sabbin kuɗaɗe a na'urorin cire kuɗi na ATM don rage ƙarancin kuɗaɗen ga jama'a, ya ce idan ba haka ba gwamnatin jihar za ta ƙwace takardun mallakar filayen bankunan; face sai idan bincike ya tabbatar cewa matsalar daga bankin CBN ce. Zulum ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Juma’a a Maiduguri lokacin da yake rangadin rassan bankunan domin gane wa idonsa yadda ƙarancin takardun sabbin kuɗin ya jefa jama'a cikin mawuyacin hali a jihar. “Duk wani banki a Jihar…
Read More
EFCC ta cika hannu da ‘yar Nollywood kan wulaƙanta sabbin takardun Naira

EFCC ta cika hannu da ‘yar Nollywood kan wulaƙanta sabbin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH Jami’an Hukumar Yaƙi da Rashawa (EFCC) na shiyyar Legas sun fara binciken Oluwadarasimi Omoseyin wadda ‘yar fim ce a masana’antar Nollywood bisa zargin yin facaka da wulaƙanta sabbin takardun Naira. EFCC ta ce abin da wadda ake zargin ta aikata ya saɓa wa Sashe na 21 (5) Dokar Babban Bankin Nijeriya (CBN) na 2007. Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce an tsare Omoseyin ne a ranar Laraba a yankin Ikoyi, Jihar Legas. Kamen nata ya biyo bayan bidiyon da aka yaɗa mai ɗauke da yadda take facaka da sabbin takardun Naira da tattaka su…
Read More
Ba don faranta wa Transparency International muke yaƙar cin hanci da rashawa ba, inji Gwamnatin Tarayya

Ba don faranta wa Transparency International muke yaƙar cin hanci da rashawa ba, inji Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani kan hasashen cin hanci da rashawa na Ƙungiyar Transparency International (TI), wanda ya nuna cewa, Nijeriya ta samu koma-baya a yaƙi da cin hanci da rashawa. Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu na Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya na mayar da martani ne a kan kare gwamnatin Jam’iyyar All Progressives Congress a ranar Laraba, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja. A cewar Lai Mohammed, yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya…
Read More
‘Ku ba ni kwana 7 zan magance ƙarancin kuɗi’ – Buhari

‘Ku ba ni kwana 7 zan magance ƙarancin kuɗi’ – Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su ba shi kwana bakwai domin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin kuɗin da ake fuskanta a ƙasa sakamakon canjin kuɗin da CBN ya yi. A wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Femi Adesina, ya ce Buhari ya bayyana haka ne yayin ganawarsu da ƙungiyar gwamnoni ta Progressive Governors Forum ranar Juma'a a Fadar Shugaban Ƙasa. Gwamnonin sun ziyarci Buharin ne domin tattauna mafita dangane da ƙarancin kuɗin da ake fama da shi a ƙasa baki ɗaya wanda a cewarsu lamarin na barazana…
Read More