Labarai

Muna ɗaukar mata aiki amma sai wacce ta dace – Kwamandan vijilante na Kano

Muna ɗaukar mata aiki amma sai wacce ta dace – Kwamandan vijilante na Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kwamandan ƙungiyar tsaro ta vijilante a Jihar Kano, Shehu Rabi’u ya ce suna ɗaukar mata aiki, domin akwai rawar da suke takawa a wajen tsaron jihar. Da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa a Kano ranar Talata, Rabi'u ya ce ba ko wacce irin mace su ke ɗauka aikin tsaro ba, sai wacce ta dace. Ya ce suna ɗaukar ma’aikata aiki waɗanda shekarunsu suka fara daga 18 zuwa 40, inda ya qara da cewa su na yin duba na tsanaki kafin ɗaukar ma’aikata domin guje wa ɗaukar bara-gurbi cikin al’umma. “Mukan ɗauki mata…
Read More
‘Yan fashi sun fasa bankuna da dama a Jihar Kogi

‘Yan fashi sun fasa bankuna da dama a Jihar Kogi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni daga Jihar Kogi na cewa 'yan fashi da makamai sun far wa rassan bankunan Zenith, da UBA da First Bank da ke ƙaramar hukumar Ankpa. BBC ta rawaito cewa lamarin ya faru da tsakar rana, inda ɓarayin suka yi awon-gaba da maƙudan kuɗaɗen da ba a san adadinsu ba. Ganau sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa, 'yan fashin sun zo bankunan cikin ƙananan motoci da babura da bas-bas, inda suka wawushe kuɗin da ke bankunan da wurin hada-hadar kasuwancin kuɗi na POS da ke kusa da bankunan. 'Yan bindigan sun yi ta…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin harajin kiran waya – Pantami

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin harajin kiran waya – Pantami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙarin harajin kiran wayar sadarwa da ofishin kasafin kuɗi na Nijeriya ke ƙoƙarin yi. Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fasahar Zamani, Isa Ali Pantami ne ya sanar da dakatarwar a ranar Litinin yayin taron ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa na haraji kan hanyoyin sadarwa don bunƙasa ɓangaren tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani a Abuja. Ministan ya ce tun tuni fannin sadarwa ya cika da harajai da yawa. Gwamnatin Tarayya ta hannun ofishin kasafin kuɗi na tarayya a baya ta bayyana cewa za ta fara aiwatar da…
Read More
Nijeriya za ta zama babbar mai kai wa Turai iskar gas — Minista

Nijeriya za ta zama babbar mai kai wa Turai iskar gas — Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙaramin Ministan Albarkatun Man fetur, Timipre Sylva, ya ce Nijeriya na shirin zama babbar mai safarar iskar gas ga Nahiyar Turai, sakamakon matsalar makamashin da ake fama da ita a duniya, wanda yaƙin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine ya haifar. Sylva ya shaida hakan ne a ranar Talata yayin wani zagayen tattauna wa a yayin babban taron Gastech karo na 50 da ke gudana a birnin Milan, Italiya. Ministan ya ci gaba da cewa, a halin yanzu, tallafin da ake samu na bunƙasa iskar gas ya kasance nasara ga Turai da Afirka.…
Read More
Sarkin Hausawan Pantami ya zama Jakadan Zaman Lafiya

Sarkin Hausawan Pantami ya zama Jakadan Zaman Lafiya

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Wasu ƙungiyoyin al'umma uku a Gombe sun karrama Malam Abdussalam Muhammad Sarkin Hausawan Pantami da lambar yabo ta Jakadan Zaman Lafiya wato 'Peace Ambassador' a turance. Ƙungiyoyin su ne Arewarmu Duniyarmu da Arewa Youth and Women for Change da kuma Hausa Fulani Youth and Development Orientation Forum Association of Nigeria (HAFYDOF). Sun karramma Sarkin Hausawan ne a matsayinsa na dattijo mai kishin al'ummarsa da kuma taimaka wa matasa. Da yake jawabi a wajen bikin da suka shirya a Gombe, Shugaban Ƙungiyar Zauren Hausawa ta duniya, Ambasada Muhammad Kabiru Kuri, ya ce sun karrama sarkin…
Read More
‘Yan sanda sun ceto ɗan takarar majalisar dokoki daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

‘Yan sanda sun ceto ɗan takarar majalisar dokoki daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'yan sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar kuɓutar da ɗan takarar majalisar dokoki ta jihar Katsina a ƙarƙashin Jam'iyyar PDP a zaɓe mai zuwa na shekara ta 2023. 'Yan bindigar dai sun yi garkuwa da Hon. Ibrahim Tafashiya wanda ke neman zama ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Kankiya a zaɓe mai zuwa. Kakakin rundunar SP Gambo Isa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar. “Gaskiya ne tawagarmu ta kuɓutar da Tafashiya daga hannun ‘yan ta’adda kuma an sake haɗa shi da iyalansa,” inji shi. Kakakin rundunar ya ci…
Read More
Matsin rayuwa ya tilasta min sakin matata, inji wani magidanci a Katsina

Matsin rayuwa ya tilasta min sakin matata, inji wani magidanci a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wani magidanci Amiru Sani mai kimanin shekara 27 a duniya ya bayyana wa manema labarai a Katsina cewar ya saki uwargidansa saboda yanayin matsin rayuwa da ya shiga. Magidancin mai mata biyu ya bayyana cewar yana matuƙar son matar tasa amma saboda matsin tattalin arziki da ya shiga ba zai iya cigaba da ɗaukar nauyinta ba. "Ba don ba na sonta ba, ba don na gaji da zama da ita ba, na saketa ne kawai don samar wa kaina sauƙi daga halin tsadar rayuwar nan da muka samu kanmu a ciki," inji shi. Amiru Sani…
Read More
Koyar da ɗalibai da harshen Hausa zai magance matsalar ilimi a Kano – Munzali Jibril

Koyar da ɗalibai da harshen Hausa zai magance matsalar ilimi a Kano – Munzali Jibril

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Fitaccen masani kuma malamin harshen Turanci Farfesa Munzali Jibril ya ce koyar da ɗalibai da harshen Hausa shi ne kaɗai mafita ga matsalar ilimi a Arewacin ƙasar nan. Munzali Jibril ya bayyana hakan ne yayin taron wuni ɗaya da ilahirin ‘yan takarar gwamna a mabanbantan jam’iyyu domin gabatar musu da manufofin da za su ciyar da Kano da Jigawa gaba. Taron wanda Zauren Ƙwararru na Kano da Jigawa wato (Kano Jigawa Professional Forum) ya shirya da manufar kawo gyara kan yadda ake tafiyar da al’amura a jihohin biyu. Farfesa Munzali ya ce ɗalibai da dama…
Read More
Babu barazanar tsaro ga zaɓen 2023 — Sufeto-Janar

Babu barazanar tsaro ga zaɓen 2023 — Sufeto-Janar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sufeto-Janar na 'yan sandan Nijeriya, Usman Alkali Baba, ya tabbatar da cewa babu wata barazana ga gudanar da zaɓen 2023. Sufeto-Janar ya bayar da wannan tabbaci ne a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja. A cewar Baba, wannan tabbacin ya biyo bayan nazarin barazanar tsaro da 'yan sanda su ka yi, ta yin amfani da mafi kyawun tsari a duniya don tabbatar da yanayin da ake sa ran za a gudanar da zaɓen. Baba ya yi magana ne a wata ganawa…
Read More
DSS ta kama Tukur Mamu a filin jirgin saman Kano

DSS ta kama Tukur Mamu a filin jirgin saman Kano

Daga BASHIR ISAH Jami'an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama Malam Tukur Mamu a Bababban Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Jihar Kano. Tun farko Mnahaja ta rawaito yadda jami'an tsaro suka tsare Mamu a birnin Alƙahira, babban birnin ƙasar Masar, inda daga nan aka dawo da shi Nijeriya. Mamu ya ce shi da iyalansa suna kan hanyarsu ta zuwa Ƙasar Saudiyya ne inda aka tsare su na tsawon awa 24 a Alƙahira. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, jirgin da ya dawo da su Tukur Mamu ya sauka filin jirgin saman Kano ne da misalin ƙarfe…
Read More